← Book details Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 66

Sashe 23

Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya nufi wajen drawer ya zaro wani dan karamin akwati baki. Takardu ne aciki da wasu tsofaffin hotuna.

Hotunan ya zaro guda uku. Dik sun ja kura. Ya yago tissue ya goge hotunan. Kyakkyawar fuskar ta ta bayyana.

Hakoran ta a jere farare tas. Karamin ciki da hakorin makka guda daya. Ta sha daurin ture kaga tsiya. Gefe da gefen kumatun ta sun lotsa (dimples).

Hannun sa ya sa ya shafa fuskar . Ji yake tamkar itace agaban sa. Ya furzar da iska daga bakin sa mai dumi.

Hannu ya saka ya kekketa hotunan. Ficewa yayi zuwa kitchen Mami ce tsaye agaban gas cooker.

"Kai kuma yaushe ka dawo?"

"Ban dade da dawowa ba Mami "

"A kawo abinci ko? "

"A koshe nake wallahi. "

"Harda wallewa? Haba Rayyan. Kai shikenan haka zaka zauna ba cin abinci kamar ba namiji ba?"

Sosa keyar sa kawai yayi. Ya dauki ashana zai fice daga kitchen din ta kira sunan sa,

"Rayyan."

"Naam..."

"Me zakai da ashana?"

"Zan kona abune."

"Toh idan ka gama sai ka a jiye a saman cabinet su Lulu yanzu zasu iso kar su dauka."

"Tohm Mami."

Fucewa yayi daga kitchen din ya shige dakin sa. Ya tattaro hotunan daya yayyaga ya shige da su cikin bandaki cikin sink ya zuba su dake ba ruwa ya bushe. Ya saka ashana ya kyasta musu nan da nan suka hau konewa.

Suna gama konewa ya yayyafa wa tokar ruwa ya zuba ashara. Ya koma ya kai ashanar kitchen.

"Allah ya jikan ki...Nanatah" hawayen da yake kokarin makalewa ne suka shiga kwarara daga idanun sa. Ya lumshe idanun sa. Ya na mai tariyo rayuwar su ta baya shi da ita alokacin da tana raye.

×××
×××
×××

*Ta kasance* jumu'ah ranar da take kebantacciya ta motsa jiki wato physical exercise a makarantar ta su ta : Eloquent international school.

Daga ajin su suka fito. Dukkanin su a aji daya suke. Amman kowanne da bangaren da yake .

Dukkanin su kowanne yanada kwakwalwa. Malamai da yawa na yabawa a bisa kaifin basirar su. Musanman yan biyu Fareeha da Madeeha.

Fita yayi zuwa harabar wajen gidan. Wanda ke a matsayin ma'adanar motocin gidan.

Kamilu driver ne a tsaye yana goge motar da ake dakko yan makaranta. Da yin cefane.

"Ranka ya dade barka da rana."

"Barkan mu dai kamilu. Ya aiki?"

"Alhamdulillahi ranka ya dade.*

"Ma shaa Allahu! Allah ya temaka."

"Amin amin ranka ya dade. Ai na wanke maka motar ta ka."

"Gatacan kam tana sheki lalle ta wanku. Godiya na ke kamilu. Fita zakayi ne?"

"Zan dakko su Hibba ne daga makarantar"

Agogon da ke wutsiyar hannun sa ya kalla . Da sauri yayi hanyar motar sa yana cewa da kamilu,

"Bari na dakko su... "

"Ah ranka ya dade da ka barshi."

"Ai ni nayi niyyah kamilu. Ba komai ka karasa aikin ka. Bara na dakko su."

"Tohm godiya na ke ranka ya dade Allah ya kara wadatar arziki. Amin"

"Amin Yaa Rabbi kamilu."

Daman yana ta son ganin fuskar mutuniyar ta sa. Don haka ya tashi motar da sauri ya fice daga gidan. Kai tsaye ya wuce makarantar ta su.

Yayi parking a harbar wajen da aka tanadar na parking motocin iyayen dalibai ko wakilan su.

Bayan ya faka motar. Ya janyo wayar sa ya shiga mayar da amsar chats din da yake ta WhatsApp.

Tamkar ance ya daga kai. Yana dagawa ya sauke idanun sa akan su su uku.

Ya janye da sauri ya mayar kan su su hiyu. So yake gano hakikanin gaskiya wacece Fareeha wacece madeeha idan ka tsame tawadar Allahn gefen wuyan Madeeha. Itama sai dai idan ba hijabi ta saka ba shine kake ganewa.

Amman muddin tana sawa shikenan ba za'a taba gano wacece ba. Hibba ta bude baki ganin Yayan na ta.

"Yaya oyoyo..."

Ta bide gaban motar ta shige. Ya yinda su biyu suka bude gidan baya zauna..

Ya juyar da kansa bayan ya musu wani kallo mai wuyar fassarawa. Dukkanin su suka gayshe shi ya amsa yana sakin tattausan murmushi....

Haka ya tashi motar yana ta kallon su ta mirror. Musanman Fareeha da ke ta tsakiya. Saitin mirror din.

Garin kallon su saura kadan yayi awun gaba da wani matashi dake tallan agwaluma..

_INA JAMA'AR TA MU? KU MARMATSO KUSA . GA TAGOMASHIN ARZIKI. SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI. MUN GWADA DOLE MU BADA SHEDA_

_INA AMARE, UWAYEN GIDA, YAMMATA? IYAYE MAZA DA KE SON FARANTA RAYUKAN MATAN SU DA YAYAN SU DA MA KANNEN SU?_

_ALBISHIRIN KU. GA GORO. DOMIN WANNAN DADDADAN LABARI DOLE MU BAKU ALBISHIR DA ALHERIN GORO. GORON MA FARI KAL KAL_

_WAI AKACE KAMSHI RAHAMA NE... KAMSHIN MA MUSANMAN ME SANYAYA ZUCIYA DA RATSA MAGUDANAR JINI DA TSOKA._

_INA MASU NEMAN KAMSHIN TURAREN SAUDI ARABIA? T'CHAD DA MAIDUGURI? IRE IREN KAMSHIN DA BAYA BIN ISKA YANA KAMA WAJE YA RIKE GIDAH..._

_KAMSHIN TURAREN KAYA, TURAREN GIDA, TURAREN JIKI, TURRARN GASHI, TURAREN TSUGUNNO, TURAREN WANKA, TURAREN WANKI, TURAREN MOPPING, TURAREN BANDAKI, TURAREN LABULAYE DA ZANNUWAN GADO, AIR FRESHENER DA TURAREN AKWATUNA DA DRAWER DA MOTA... KAI HAR MA DA TURAREN DA KE CIRE BACIN RAI YA MUSANYA DA FARIN CIKI SABODA TSANANIN SANYAYAWAR SA DA YAYE DUHU DA DAMUWA_

_BA ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNADA NAU'IKAN TURARUKA NA KHUMRAH KALA KALA. SUNADA TURAREN RUWA NA FESAWA DANA MAIKO. SUNADA KAYAN GYARAN JIKI.._

_SUNADA KULACCA DA SAURAN BODY BUTTERS MASU YAYE WARI KODA KUWA AN YI KWANAKI BA WANKA BARE WANKI._

_SUNADA KABBASA TA TURARA KAYA DA KASAKEN TURARUKAN WUTA NA KARFE DANA KASA DAMA NA ZAMANI YAN WAJE._

*_YERWA INCENSE AND MORE_*

_YERWA INCENSE AND MORE_

_YERWA INCENSE AND MORE_

_MASARAUTAR KAMSHI KENAN. KAYAN SU NA AKAN FARASHIN SARI DA SAYA DAYA DAYA.. SUNA YIWA AMARE HADI DA UWAYEN GIDAH DAMA YAMMATA. SUNAYIN NA TARON SHAGULGULAN BIKI DUK AKAN FARASHI MAI RAHUSA_

_BA'ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNA DA TARIN KAYAYYAKI MASU KYAU DA RAHUSA HADI DA INGANCIN DA ALKALUMA SUNYI KADAN WAJEN BAYYANA MUKU._

_SUNA TURA KAYAYYAKIN SU FADIN NAJERIYA DA KETARE BAKI DAYA._

_ADIRESHIN SU. SUNA GARIN KANO DAURA DA TITIN DA ZAI SADAKA DA GARIN MAIDUGURI_

_SUNA KAN MANHAJOJIN SU DAKE KAFAFE DA DAMA KAMAR:_

_INSTAGRAM: @yerwaincense_and_more_

_FACEBOOK:yerwacollection_

_WHATSAPP: 08095215215/09044191709_

_A YANZU HAKA KAMFANIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE SUNA SALES DIN KAYAN SU NA 250ML NA TURAREN WUTA DA KUMA 240 DA 190ML NA KHUMRAHS_

_IDAN ANJE ACE DAGA ZAFAFA NE AKWAI RAGIN KUDI DA HADI NA MUSANMAN DA ZAA YIWA DUKKANIN KAYAN DA KUKA SAYA._

_KYAU!! INGANCI! RAHUSA!! KAMA JIKI DA GIDAH!! AIKI!! ADADE ANA MOREWA SAI KAYAYYAKIN TURARUKAN KAMFANIN:*YERWA INCENSE AND MORE*_

_____
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥

0022419171
Maryam sani
Access bank

*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

*Thanks for choosing us*🔥

_𝕂𝕀 𝕂𝕌𝕃𝔸 ℕ𝕀!!_
_(𝕄𝔸𝕃𝕃𝔸𝕂𝕀ℕ ℤ𝕌ℂ𝕀𝕐𝔸)💕_

_ℕ𝔸ℕ𝔸 ℍ𝔸𝔽𝕊𝔸𝕋_
_𝕄𝕀𝕊𝕊 𝕏𝕆𝕏𝕆_

_ℙ𝔸𝕀𝔻 ℙ𝔸𝔾𝔼:20_

-----

  Haka suka karasa gidah da karfin addu'a. Don da gasken gaske Yazed ya fada kogin kaunar daya daga cikin su. Ko Fareeha ko Madeeha . Gashi har yau ya kasa tsayawa ya tabbatar wacce daga cikin su ce ta zamar masa MALLAKIN ZUCIYAH. ? Ba kadan ba zuciyar sa ta kamu da kaunar dayan su. Kaunar ma mai wuyar fassarawa.

"Godiya dubu Yaya Yazed...." Madeeha ta yaba masa da godiya abisa dauko su da yayi daga makaranta..

"Thank you Yaya .." Hibba ma ta masa godiya.

Ya yinda Fareeha tayi murmushi kawatacce .

"Sannu da kokari..."

"Yauwa kanne na...."

Suka jera su uku. Kusan kansu daya. Sun fi Hibba tsawo da kadan. Don su din dogaye ne . Ko a shekarun su a tsawon su sai an duba.

Har kofar da zata shiga sashen su suka mata rakiya. Kafin su ma su wuce boys squatter din da yake a matsayin na su.

Yazed ya dade jingine da jikin mota ta baya. Ya nata saqawa da warewa akan kaunar da ke addabar zuciyar sa da gangar jikin sa baki daya.

Bude mota ya sakeyi ya shige kai tsaye ya fuce daga cikin gidan .

✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓

Tun da ya kwana da ciwon kan daya kwanta da shi. Bai sake shi ba sai gab da sallar asubahi ya farka

Gani yayi har lokacin sallar dare da yake yi ta shude yau ya makara.

Don haka ya mike da sauri bakinsa dauke da addu'a ya shige cikin bandaki. Alwala ya dauro ya shimfida sallaya ya tada sallah da niyyah.

Bayan ya idar ya daga hannu yanata kwarara addu'oi. Yana cikin lazimi ne akayi kiran sallah.

Ya dauki wayar sa ya fice zuwa masallaci. A kofar fita wajen gidah yaci karo da bappan su.

"Bappah.."

"Na'am danyaye.."

Murmushi Rayyan yayi. Jin yadda bappan na su ya kira shi .

"Muje ko ...? Kar mu makara."

"Bappah barka da asubah."

"Barkan mu dai Rayyanu ."

Fita sukayi. Bappan na rike da hannun na Rayyan. Ya rike sa gam tamkar irin karamin yaron nan da ke tafe ana kula da shi.

"Shi ya sa ko laifi ka mun zaka ga wani lokacin bana bi takan lefin. Kasan me yasa?"

"A'ah Bappah..."

"Saboda u're very religious ... Kana riko da addini sosai. Sallah bata wuce ka musanman ta asubah. Kowacce sallah kullum kana jam'i acikin masallaci. Ga yawan azumi.."

Rayyan yayi murmushi kawai yana sauraron Bappan na su. Alhaji Harith ya yi murmushin shima. Kafin ya cigaba da cewa,

"Keep it up ... Ubangiji Allah yasa ka dore har karshen rayuwar ka."

"Aamin Bappah Amin."

Karasawa sukayi cikin masallacin. Ba dadewa kuwa aka kira assalatu. Sai da aka idar da sallah. Suka karasa yan addu'oin su tukun sannan suka koma cikin gidah. Sai ga Raees yana tafe yana hade hanya. Yanata goge idanun sa da alama baccin bai sake shi ba. Ya yin da Yaseer ke biye da su a baya.

"Kai kuzo nan..."
Chapter 23 · 0% Book details