← Book details Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 66

Sashe 1

Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

_ZAFAFA BIYAR 2023_

_SABUWAR SHEKARA, SABUWAR TAFIYA, SABON SALO, SABABBIN NISHADI MASU DAUKE DA DIMBIN DARUSSA DA YALWAR KAUNA MARAR GAURAYE_

_KU KASANCE TARE DA ALKALUMAN ZAFAFA BIYAR DON WANNAN TAFIYAR TAFU KOWACCE..💕_

_DANDANO DAGA LITTAFIN:_

_*KI KULA NI (MALLAKIN ZUCIYAH)*💕_

_DAGA ALKALAMIN:_

_NANA HAFSATU (MSS XOXO)_

×××××××××××
*_BIRMINGHAM UNIVERSITY NIGERIA_*
_(UNIVERSITY IN KANO)_

×××. °°°. ×××. °°°.

*Cikin* takun sa na kasaita mai tattare da zatin haiba da madaukakin kwarjini ya fara hawa mattakalar benen da zai sadaka ga dinning hall/cafeteria din makarantar.

Daga can karshen kuryar hall din ya hango abokan na sa su biyu. Kamar ko da yaushe babu dalibai awajen sosai. Sai wanda suka isa suke kuma gadara da kudin iyayen su.

Duk inda ya gifta sai dalibai yan uwan sa sun juya sun sake duban sa sosai. Saboda tsananin kyawun sa, Kasaitar sa da kuma gayun sa.

Sanye yake cikin kananun kaya. Samfurin riga Burberry da wando Dkny. Agogon sa kalar rigar jikin sa na Rolex, Sai azurfa a yatsan sa daya.

Ya karasa wajen abokan nasa ya zauna yana cije lebe.

"Geee..." Cewar dayan abokin nasa.

"Guy...Sup?"

Abokan nasa su biyu suka mimmika masa hannu hadi da kiran sa da Gee da kuma Guy.

Agogon hannun sa ya kalla. Sai kuma ya daga kai ya leka yar karamarr transparent barandar da ke kusa da table dinsu. Wacce idan ka leka ka na hango farfajiyar makarantar .

Sosai ya shiga baza idanuwa amma sam bai hango ta ba.

"Wai Ray me kake dubawa ne?"

"Mystery gurl din sa mana .."

Bai basu amsa ba. Ya dai jiyo T-Boy na ba wa B-junior amsa.

"Ko bata da lafiya ne? Ko wani abun na daban ya sameta?"

"Wai Ray da wa kake ne? "Cewar B-junior.

"Jokes aside... Tasan yanayin da kake ciki kuwa?" T-Boy ya fada yana bin Ray din da kallo.

Rayyan ya kamo kasan leben sa ya ja. Ya ki ce musu komai. Da sauri kome ya tuna oho. Sai ya janyo wayar sa da ke cikin aljihun gaban rigar sa.

Gallery ya shiga. Nan da nan ya dakko hotan time table dinsu ya shiga dubawa. Suna da lectures a lokacin. Kuma idan har bata je ba ba zata samu daily attendance din da lecturer din ke yi ba. Kullum da safe yake karba kuma individually .

"Ray... "

"Gee... Guy... Snap out of it." T-Boy ya fada hadi da murza yatsun sa a daidai saitin fuskar Ray. Ganin tamkar baya duniyar su ya lula tunani.

Mikewa yayi bai ce musu komai ba. Suma suka tashi suka bi bayan sa. Da sauri hadi da gudu gudu ya karasa Elizabeth Arden twin theatre din da anan suke lectures.

Da sauri ya shiga ajin hade da gyara zaman face mask din daya sakala. Yana shiga ya zaro paper ya rubuta registration number din ta da sunan ta da sunan course din.

Ana fara mikawa row by row shima ya mikawa malamun ya fice da sauri

"Guy... Wannan ai sayar da rai ne. Zaka je ka wani yi mata attendance. Yarinyar da bata ta ta ka. Bata kula ka. Ka zama lunatic wallahi. "

Bai bi ta kan T-Boy ba. Sai ma murmushi da yayi masa na gefen bakin nan irin ba ta kai na ke ba.

Yana juyar da kansa ya sauke idanun sa akan ta. Tana tafe sanye cikin dogon hijabi har kasa. Maroon color. Farcenta sun sha maroon lalle tayi bala'in kyau.

Ta sakala jaka mai dauke da littafai. Dayan hannun nata kuma water bottle ce shudiya.

Kasa jurewa yayi. Ji yake tamkar an tsunduma shi cikin farin ciki marar misaltuwa da bai taba shiga ba.

Sauran dalibai aka tsaya ana kallon su. Daman theatre din lectures din tamkar mudubi take ana hango komai na ciki.

Dan haka idanuwan ta suka cicciko zatayi kuka. Ganin malamin har ya shiga kuma tasan ya karbi attendance bugu da kari baya bari ashiga idan ya shiga.

Rayyan ya tunkareta gaban sa na faduwa. Ko sau daya bata taba bashi damar magana da ita ba. Harara ce kullum take aika masa. Da mummunan kallo. Wanda duk duniya ita kadai ke yi masa hakan. Amman ya rasa meyasa ta zamar masa MALLAKIN ZUCIYAH...

Bakinsa na rawa. Yayin da idanuwan sa ke narkewa da kaunar da yake mata wadda ke ninkuwa a duk lokacin da ya dora idanuwan sa akanta. Ko da kuwa sunan ta aka kira.

"KI KULA NI........."Ya fada cikin muryar sa mai dadin sauraro. Gashi yayi lafazin ne cikin sigar zallar kauna ga abunda ake nunawa kaunar.

Ga takaicin lecturer ya shiga ba zaa shiga ba. Na biyu rashin attendance da bata samu ba. Na uku takurar sa daya isheta.

Cikin kufulewa da kololuwar karshen takaici ta dube shi a yatsine tace,

"In kula ka... Akan wane dalilin?"

"KI KULA NI.... saboda kin zamar mun MALLAKIN ZUCIYAH..💕"

Gaba tayi saboda tsananin yadda ranta ke tafarfasa da bacin ran sa.

Jakarta ya riko. Hadi da sake zube mata manyan idanun sa akanta yana binta da wani kallo mai tura sako..

"Cika mun jaka Malam.."

Tana kokarin janye jakarta hannun sa ya gogi nata. Cikin gigicewa ta daga hannu ta tsinka masa mari .

Baki daya daliban wajen kowa ya bude idanuwa da bakuna.

T-Boy zai bugeta. B-junior ya hana ta hanyar riko hannun sa.

=====

*KING CHARLES TEA ROOM*

"What the fuck.... Gee me yaran nan ke takama da shi ne? Mulki ko sarauta? Tukunna ma wacece acikin yan biyun? identical twins ne ance."

"Eh naji Fatee kasan... Faculty dinsu daya...Tace sunan su Fareeha da Madeeha.

"Ray kai wa kake so ... Fareeha din ce ko Madeeha?"

===============

"Allah Suwaiba... Na tsani Hajiyan nan.. Na ki jinin yadda alhaji ke rawar jiki akanta."

"Mahaifiyar sa ce kawata."

"Duk da haka bana kaunar hakan...Kaunar da yake mata tayi yawa. Sai fa abunda tace yake yi. Gaskiya banaso. Ko kayan gidah zai canza sai ya hada da nata ya canza. Komai yace Hajiya. Komai komai..."

====

"Haba Malam.. gaskiya ba zata sabuba. To har sai an jira sun turo? Ke siddiqa ki ce masa mu zamu turo manya suyi tambaya."

"Yanzu banda tambadewa irin ta ki safiya kintaba ganin gidan mata sun tura maganar aure gidan su manemin ta saurayi ? Gidan budurwa su aika tambaya? Wanne irin sauri kikeyi haka? Aina aka taba haka?"

"Ahayye ragadada... Yanzu sai mu zauna mu zuba musu na mujiya.? Aa wallahi kaji rantsuwar gaskiya.m"

"Haka kikace? To wallahi sai dai ke ki nemi mutanen da zaki tura ba hannu na aciki...."

=====

Hannunta yana rawa ta janyo tsohon hotan dake ma'adanar data ajiye. Da sauri gabanta ya shiga bugawa alokacin da ta.......

===

Dukkanin KOWA da KOMAI RUBUTACCE NE DAGA ALKALAMIN QUDRA.. DON HAKA TUN RAN GINI TUN RAN ZANE.. DAN ADAM BAYA TABA TSALLAKE KADDARAR SA..

Littafi ne da yazo da wani salo mai tattare da dimbin darussan rayuwa. Hadi da nishadi kana da zazzafar kauna marar gauraye..💕

**Dandano kenan daga tsakuran wasu rassa na cikin littafin KI KULA NI (MALLAKIN ZUCIYAH)💕

wanda ni nana hafsatu zan kawo muku shi daga cikin jerin LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR 2023

______________________
*RUMBUN K'AYA*🔥

*DAUDAR GORA*🔥

*IDON NERA*🔥

*A RUBUCE TAKE*🔥

*KI KULANI*🔥

*_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊

*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*

*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*

*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️

*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*

*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*

*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*

Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥

0022419171
Maryam sani
Access bank

*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

*Thanks for choosing us*🔥

*_K I K U L A N I_*
_(MALLAKIN ZUCIYA)💕_

_N A N A H A F S A T_
_MSS XOXO_

_F R E E - P A G E :002_

_ASSALAMU ALAIKUM JAMA’AR KWARAI.. JAMA’AR AMANA… JAMA’AR ZAFAFA… MASOYA KUMA MABIYA MASU ALHERIN SAYAN ZAFAFA A KODA YAUSHE BA GAJIYAWA…GODIA MAI TARIN DIMBIN ALBARKA DA FATAN ALKHAIRI AGARE KU.._

_KUNSAN DUK INDA ABUBUWAN ARZUKA SUKE MUNA SHIGA MU KURDA MU NEMO MUKU SU DOMIN JIN DADIN KU..🥰💕SABODA KU DIN NA GABAN GOSHINAN MU NE._

_TAMKAR KO DA YAUSHE.. YAU MA MUNZO MUKU DA WATA TSARABAR.. TSARABAR DUNIYAR KAYAN KITCHEN, DECORATIONS DA SAURAN SU… KU MARMATSO KU JI…_

*_MAAB LUXURY HOME_*
*_MAAB LUXURY HOME_*
*_MAAB LUXURY HOME_*

_KUN GANI KO? TO INA AMAREN? INA UWAYEN GIDAH INA YAMMATAN DA KE SHIRYE SHIRYEN SHIGA DAGA CIKI? INDA ZAKU JE KU KANKARO MUTUNCI KU DANDALO ARZIKI NA KECE RAINI.. INDA ZAKU WUCE RENI DA GANIN KASKANCI..INA MAZAN DA KE BURIN FARANTAWA MATAN SU DA ‘YAYAN SU DA KANNEN SU? _

_MAAB LUXURY HOME: RIGIJI GABJIN KENAN! WOHOHO WANI KAYA SAI AMALE KAN DAUKA.. MAAB LUXURY HOME : ALJANNAR KAYAN KITCHEN KENAN, INDE AKACE KAT TOH KARSHEN MAGANA TA KARE KENAN.. MAAB LUXURY HOME ; A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY KITCHEN UTENSILS, HOME DECORATIONS AND MUCH MORE_

_ADIRESHIN MU: MUNA KAN TITIN AHMADU BELLO WAY, KANO STATE. ZAKUGA TAMBARIN DA MAAB LUXURY HOME.._

_DAN SAUKAKA MAKU FITA ZUWA SHAGON MU. ZAKU IYA ORDER AKAWO MUKU DUKKANIN INDA KUKE A FADIN NIJERIYA DA KETARE. _

_INSTAGRAM: @maabluxuryhome._

_FACEBOOK: @maabluxuryhome._

_KO KU NEME MU TA LAMBAR TARHON MU: 08034631010_

_KYAU! INGANCI! RAHUSA! ADADE ANA AMFANI DA SHI SAI KAYAN: MAAB LUXURY HOME_

_100% TESTED AND TRUSTED😍☑️_
______

*A* darare ta kashe dan kyandirin da ke ci ahankali ya kusa cinyewa. Ta dubi yaran nata su biyu maza. Sun zuba mata idanu.

Ta yafito daya da hannu yana matsowa kusa da ita ta goye shi a baya. Ya yinda ta dauki dayan a hannu.

"Kuyi shiru. Kar wanda yayi magana.. "

Sikif ta fice daga cikin dakin zuwa bandaki bayan tayi adduar shiga. Dan ruwan da ke cikin bokitin da ta sakaye shi a bakin kyauren ta dakko. Ta saka hannun ta aciki da dan dumi kadan.
Chapter 1 · 0% Book details