Sashe 53
Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Yauwa Allah yayi muku albarka...."
"Aamin Aamin ummy."
"Aamin Ummyn mu "
Shiryawa suka karasa yi. Suka fita daga cikin gidan su uku.. Su biyu suna tafe a gaba. Sai Yayan su Junaid daga bayan su.
Yazed ya sha kwanar gidan kenan ya hango su tsaye a titi suna jiran mota. Gangarawa yayi da motar sa wajen su. Idanun sa na tsayar da kallon su akan Fareeha da ke ta buya abayan Madeeha.
Gayshe shi sukayi. Ya amsa yana mai sake tattare duban sa gaba daya ya mayar kan Fareeha.
"Ina zaku je ne? Ba dai tafiyar tazo ba?"
"Itace.... Amma yanzu zamu biya gidan kawun mu kawu Ashiru ne mu gayshe su sai mu dawo mu wuce can din."
"Allah sarki. Allah ya bada ladan zumunci ku shigo na kai ku dan Allah." Ya karasa fada yana kannewa Fareeha ido guda daya.
Duk suka shige cikin motar. Junaid agaba. Su kuma suna baya...
Suna ta yar hirarrakin su a haka har suka karasa unguwar su ta da. Wato gyada road.
An samu sabon gina gine na gidaje da shaguna na kasuwanci. Sosai cigaba ya wanzu ba lefi a unguwar ta gyada road.
Har kofar gidan Yazed ya kai su sannan ya ce
"Ina jiran ku idan kun gama.."
"Ah ba zaai haka ba... Kar mu bata maka lokaci." Junaid ya fada masa yana murmushi.
"Ba damuwa Allah... Zan jira."
"Tohm shikenan mungode."
Shigewa sukayi cikin gidan . Tun daga bakin kofa suke sallama..Gidan ya sake zama dan karami. Sashen da daa yake a matsayin na su Madeeha yanzun babu shi. Mutumin daya sai wajen ya gine shi ta can baya. Sam ba zaa ce dama ginin aciki yake ba.
Daga soro kake jiyo kururwar kawu Ashiru yana bambamin masifa. Shi da matar sa Rahila ne suka cacar baki.
"Sittin ta ubangiji kai ka dauka. Nera dari biyu da hamsin ana nan wajen kafin rufe budewar ido da rufewar sa sai naga wayam babu ka yashe? Kudin da sai da na kitse kai sama da uku kafin na hadasu..wallahi sai ka biyani." Ta karasa fada hadi da rarumo kwalar rigar sa ta rike.
"Kinci haka kaza ta uban ki Rahila. Na tattaro na kwashe miki albarka . Ni zaki duba kice na dauka miki kudi?"
"A hayye... Sandamu.... Yo ai ba yau farau ba. Rannan ma kai ka dauka mun nera dari kaketa jera rantsuwar aqeelu ne."
Kici kici suka hau kokawa. Rahila ta daga shi ta nana da kàsa. Da ke karfin ba daya bane. Ta hau ruwan cikin sa tana bugu kenan su Fareeha suka shiga suna cigaba da sallama. Sam su kawu Ashirun basu ji ba sunata hayagaga.
Tana zaune a ruwan cikin sa suka shiga. Badan ta sansu tun suna jarirai ba yau da tabbas ta karyata ganin ta da cewar ba su din bane ba.
Saboda tsananin mamakin data shjga sunata gayshe ta ta kasa amsawa. Tana mai bin tun daga kan yan yatsunsu na kafafun su da kallo.da ke sanye cikin takalmi covered da ya shiga da kayan da ke jikin su.
Tamkar larabawa haka take kallon su. Yau da ace akwai inji dake canza mutane to da ta tabbatarwa kanta kai su akai aka canzo su.
"Ina wuni ...?"
"Kawu..Ina wuni?"
Suka shiga gayshe da su.. Rahila sai ta zama tamkar sokuwa ta kasa cewa komai. Kawu Ashiru ya jirketa dakyar yana mayar da numfarfashi.
"Shegiya katuwa. Kin zaune ni da wannan malamalan cinyoyin na ki. Ina magana kinyi shiru...Me kike kallo ne haka?" Ya karasa fada yana sakin siririn tsaki .
Yana daga idanuwan sa ya sauke akan fuskokin su. Madeeha, Fareeha da kuma Junaid.
Da sauri ya mike yana gyara zaman rigar sa da matar sa Rahila ta hautsina ta ta chukurkuda...
Ya buda katon bakin sa. Ya kurma wani uban ihu me hade da tsawa.
"Uban me ya kawo ku gidah na??????
MX WRITES✓✓
_𝕂𝕀 𝕂𝕌𝕃𝔸 ℕ𝕀!!_
_(𝕄𝔸𝕃𝕃𝔸𝕂𝕀ℕ ℤ𝕌ℂ𝕀𝕐𝔸)💕_
_ℕ𝔸ℕ𝔸 ℍ𝔸𝔽𝕊𝔸𝕋_
_𝕄𝕀𝕊𝕊 𝕏𝕆𝕏𝕆_
_ℙ𝔸𝕀𝔻 ℙ𝔸𝔾𝔼: 45_
_ZAFAFA BIYAR 2023_
××Jikin su sai yayi sanyi sosai . Ganin duk wannan tsawon lokacin da suka dauka tare har yanzu kawun na su baya kaunar su sam.
"Nace me ya kawo ku gidana iyye? Yan gaba da iska.."
Fareeha da Madeeha suka hada idanu. Fuskokin su dauke da rashin jin dadin abunda kawun na su ya musu ..
Junaid ya dan matsa daga inda yake zuwa kusa da kawun na su. Kawu Ashiru ya saka hannu ya tunkuda shi can gefe yana mai jifan sa da harara...
"Kawu kayi hakuri......Zuwa muka yi mu gayshe da ku." Junaid ya fada yana mulmula kasan gwiwar hannun sa daya dauje da bangon da kawu Ashiru ya nana shi da shi....
"Na hada ka da hakurin na kwarfe dan abu ta kazar uban ka."
Madeeha ta dan juya kafa zata tafi Fareeha ta riko hannun ta ... Ta hanata tafiya.
Junaid ya musu alamar da su tsugunna.
"Ina kwana?" Suka hada baki wajen sake gayshe da Rahila matar kawu Ashiru.
Ta yamutsa fuska tana tabe bakin ta.. Ta daga yatsa daya tana mai dora shi akan su Fareeha.
"Kwailin kuke... Allah ya shirya. Dubi yadda kuka kod'e kuka 'dashe... Allah ya kyauta. " Ta karasa fada hadi da mikewa tsaye ta shige cikin dakin ta.
"Ba zaku tashi ku fita ba...?" Ya rarumo takalmi kafa daya ya nufe su da shi zai doka musu.
Suka tsaya basu tafin ba. Ai kuwa ya fara rafka musu ta ko'ina..Junaid ya rike takalmin yana rokan kawun na su,
"Dan Allah kayi hakuri... Kaji kawu?"
"Laaa.. Rahila kina ji? Rama dukan da na musu zeyi. Ya rike takalmin. Shikenan shaudamun. Nace rafkamun...."
"Ni na isa na dake ka kawu? Na isa na rama dukan da kake mana? Hakuri nake ba ka. Ka kyale mu dan Allah mu zauna mu gaysa kawu. Gayshe ku muka zo yi."
"Idan ka sake maganar gayshe mu kuka zo yi da girman Allah sai na raba hannuwan ka da jikin ka. Kaga dan iskan ya...
Bai karasa fada ba aqeel 'dansa ya shigo gidan da sauri yana dariya.
"Ah Fareeha.. Madeeha... Junaid. Wallahi ku ne. Yara ke cewa kunzo nace bari na zo na gani ko dagaske suke. .."
"Mune Yaya aqeel.."
"Mune Yaya "
Suka shiga amsa shi. Yanata farin cikin ganin su. Ya yinda kawu Ashiru ke dankara masa harara.
"Ban dari biyu dan kani na." Aqeel ya dubi Junaid ya fada yana mai sosa keyar sa.
Junaid ya danyi murmushi ya zaro gudar dari biyar daga cikin dan kudin da yake samu a kasuwar sabon gari shagon abokin sa da ke siyar da shaddodi da atamfofi da kayan yara..Junaid din ne ke jiran shagon na sa duk ranar da ya tashi daga makaranta.
Aqeel ya saka hannu biyu ya karba yana shararawa Junaid godiya.
"Ba zan taba mantawa da kai ba a rayuwata Junaid. Pi network na fashewa da girman Allah zan saya maka jirgi da gidah a kasar turkiya, Ina nan ina mining ... Kaji ko?
Junaid yayi murmushi kawai. Har yanzu yayan na su bai dai na maganar pi network ba ...
Yar ledar da ummy ta cika ta musu ita da omo a babbar leda da sabulan wanka dana wanki tace su bawa kawun na su. Ita Fareeha ta mikawa aqeel don tasan kawu Ashirun ba karba zeyi ba..
"Me muka samu? Laa Umma kunga abun arziki"
Kawu Ashiru ya saka hannu ya buge ledar hannun aqeel a kàsa. Ya kwasa yayi kan su Fareeha suka fita da gudu. Banda Junaid da ke tsaye kawu Ashiru nata rafka masa takalmi a hannu.
Sai daya ga dukan yaki ci yaki karewa ne yasa ya fuce wajen shima da sauri ya yinda kawu Ashiru ya bi bayan su yana saukar musu da rundunar ashariya. Aqeel nata bashi hakuri..
"Yan haka kaza ta uba.. Idan na sake ganin kafar dayan ku anan da girman Allah sai na datse ta. .." Fada yake sosai idanuwan sa a rufe ko ganin Yazed beyi ba.
Yazed ya girgiza kai kawai. Ya karasa wajen kawu Ashirun yana gayshe da shi. Sai a sannan kawu Ashirun ya daga kai ya sauke akan Yazed din. Ya shiga kakaro murmushi yana cewa,
"Lafiya kalau yaron kirki.... Ya mutanen gidan?"
"Sunan kalau Alhamdulillahi... "
Kawu Ashiru ya sake daga yatsa yana nuna su da su.
"Kuje can gayyar tsiya... Wanda baa san usulin mahaifiyar ku ba... Na datse zumuncin da ke tsakanin mu da ku. Kar shege da shegiyar da suka sake dakko kafafun su suka zo gidana.. Kai kuma yaron kirki kuyi ahankali domin tsintacciyar mage bata mage." Ya juya ya fadawa Yazed kafin ya shige cikin gida yana jera tsaki wani bayan wani..
Jikin su dik a sanyaye.... Gefe daya kunya duk ta lullube su..Musanman Fareeha da soyayya ta shiga tsakanin su da yazed din..
Haka dai suka shiga mota... Duk a takure. Yazed din ya tashi motar suka dauki hanyar komawa gidah..
============
Sannu ahankali haka dan adaidaita sahun ya kai shi har kofar gidan su Madeeha.. Ya zaro kudin sa ya mika masa.
Tsayawa yayi yana bin layin da kallo kafin ya sauke kallon sa akan gidan da su Madeeha ke cikin sa.
Masu gadi ya gani a kofar gidan su biyu. Ya karasa kusa da su ya mika musu hannu suka gaysa.
"Dan Allah tambaya na ke...."
"Toh Allah yasa mun sani.."
"Madeeha na ke nema ko tana ciki?"
Daya mai gadin ya daga kai kafin yace,
"Sun fita ba dadewa can..."
"Fareeha fa?"
"Tare suke da Yayan su ma... Da oga Yazed."
Rayyan ya daga kai... Ya janyo kásan leben sa ya taune yana mai furzar da iska daga bakin sa. Kafin ya sauke idanun sa akan agogon da ke daure a hannun sa.
Komawa yayi dan gefe ya zauna hadi da zaro wayar sa ya shiga dubawa.. Ba dadewa can tamkar ance ya daga kai... Yana daga idanun sa ya sauke akan matar data futo daga cikin gidan . Hannun ta rike da yar jakarta ta hannu. Gefen ta kuma akwatuna ne...
Wata mota ta tsaya agaban ta... Ta bude gidan gaba ta shiga.. Bayan masu gadin sun temaka mata da zura akwatunan a bayan motar..