← Book details Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 66

Sashe 3

Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta dan jima tana musu fiffita. Dai dai lokacin da aka fara kiraye kirayen sallar azahar.

Wata yar roba dauke da ruwa ta janyo ta tsiyaya a yar karamar butar ta. Kafin ta bude kofar dakin ahankali ta fice zuwa wajen tsakar gidah

Bandaki ta shige da sauri ta rage cikin ta. Sannan ta fito waje ta fara alwala. Tana yi tana kakkauda kai gefe da gefe saboda gudun fitina.

"Kai Kai Kai... A'ina kika samu ruwa? Cabdijan Malam fito nan." Ladiyo da ke tsaye kerere akan Fadila ta yage baki tana mai sake kiran,

"Malam wai kana ina ne?"

Fito da kansa yayi ta kofar dakin sa yana yamutsa fuska .

"Menene wai? Iyye?"

"Ruwa naga Fadila na amfani da shi. Kuma dai banga ta saya ba."

"Ke ... Wane dan jakar uban ne ya baki ruwa?"

Fadila ta kasa cewa komai. Ruwa ma batada ikon mallaka batare da an nemi ba'asin a'ina ta same shi ba.. Ruwan ma sai dai ta cire kudi ta saya guga daya nera ashirin a rijiyar gidan da Ladiyo tasaka a ka haka kafe ta tsare wai ta zama mallakinta.

"Kaga tayi shiru ko? ... Ai na gayan ka sata tayi. To wabillahi.."

"Wallahi ban diba miki ruwa ba. Anas daya shigo gidan nan jiya shi ne ya ebo mun a waje bokiti uku."

"Yana ina dan bankadaddiya? Wannan yaro wannan yaro ba dan ni na haife shi ba Allah ca zan ba jini na ba ne. Dan kan uba." Ta karasa fada hade da dankarawa Fadila harara.

"Allah ya baki hakuri."

"Da hakuri yayi gabas. Yamma nayi matsiyaciya. " Ta buga tsaki ta shige daki.

Malam Haladu ya yamutsa fuskar sa yana tabe baki.

"Me zakiyi yanzu?"

"Sallah zan ."

"To idan kin sallame ki zo yanzu."

"Toh Malam."

Kanta a kàsa ta koma daki. Ta zura hijabin ta ta tada sallah. Ta dade a sujjada tana addu'oin ta. Hawaye na tsiyaya daga idanun ta.

Hakika rayuwar ta data yaranta na cikin halin bakar kaddara da rashin samu. Rayuwa ce abar tausayi ga kokawa.

Ita din mata ce ta aure ga Malam Haladu. Amman tamkar wacce tazo haya haka aka dauke ta agidan nan.

Kyara, Tsangwama da mugunta kullum cikin shan su suke ita da yaran nata.

Gashi Allah ya azurta ta da samun albarkacin yara har uku. Hammadu da Haidar da Hadiyyah.

Ko da ta shafa addu'oin da tayi bayan ta idar. Hawaye ne ke kwarara daga idanunta kawai.

Ta rasa wacce irin rayuwar aure take agidan.. Gashi babu wanda zata tunkara da damuwar da ke dankare a cikin kirjin ta.

Kasancewar ita din irin tsatson fulanin tashi dinnan ce. Ita da iyayen ta sunyi tashi daga rugar su zuwa garin na kano acan baya bayan gari.

Wataran mahaifin ta ya fita kora shanun sa. Ya jima bai dawo ba. Har ya wuce lokacin dawowar tasa. Hakan yasa mahaifiyar ta ta shirya tabi bayan sa. Don nemo shi jin ko lafiya?

Ashe fitar karshe sukayi. Shanuwar sa daya ce ta kasa acikin jejin bayan unguwar.

Ya baro ta dan dawowa cikin unguwa ya samu wuka ya yanka kar ta mace ta zama mushe. Ashe ajali ne ki kiran sa. Tsallakawar da zeyi wata mota ta taho da sauri gingimari ce. Alokacin kuma mahaifiyar Fadila ta hango shi. Ta kira sunan sa da karfi ganin ga mota nan zata risko shi Bai jiyo ba. Ta tsallaka kenan. Shi kuma ya hangota yana kokarin dakatar da ita. Kawai motar tabi takan su ta nuke su. Nan take basu shura ba rai yayi halin sa.

Sai ya zamto Fadila bata da kowa. Ba wasu suaran dangi . Ita kadai iyayen ta suka haifa. Kuma baa san usulin su ba.

Bayan an share makoki. Sai rikon ta ya koma hannun gidan mai unguwa. Har ta fara tasawa. Aka danka mata shanun ta da iyayenta suka bari. Wannan dukiya data samu ta shiga zukatan Maza da dama. Akaita turereniyar neman auren ta.

Saboda tana da kyawu sosai ga kuma tulin dukiya ta shanu da iyayen ta suka bari. Har ya zamto sun tumbatsa har garke biyu

Malam Haladu ya kasance acikin maneman na Fadila. Duk inda ta saka kafa yana biye da ita yana gaya mata sakon zuciyar sa. Irin kaunar da yake mata da son kasancewa da ita a matsayin matar sa.

Ya hure mata kunne dai. Har dai ta amince da soyayyar sa. Aka daura musu aure. Ya lalube shanunta baki daya ya sayar da zummar wai zai saya mata gidajen haya ya kuma kai ta umara.

Nan kuwa harkar gaban sa yayi da kudin ta. Ya rika kashewa yan mata yana saye da sayarwa. Ya sayi wani gidah awata unguwar suka koma can. Anan ya auro Ladiyo ma.

Ya saka su agida daya da Fadila. Ya dinga cin kudaden nan tas har ya karar da komai. Fadila ba dangin iya bare na baba. Gashi sun koma wata unguwa ta daban da batasan kowa ba balle takai kukanta wajen mai unguwa.

Haka ta hakura da cin kashin da Haladu da Ladiyo suke akan ta. Ba ruwa agidan. Ladiyo tasaka aka haka mata rijiya. Makota ma suna zuwa su eba. Amman Fadila bata isa ta debi ruwan nan ba sai dai ta saya. Duk guga daya nera ashirin...

Haladu ba ruwan sa da ita. Daman auren dukiyar ta yayi da kuma na kauda sha'awa. Don haka sam bata gaban sa. Wataran idan abun na kansa. Haka zai nemata ko tanaso ko bataso ya raya sunnah ta karfi da yaji cikin mugun ta da kiyayya.

Duk ta rame ta jeme. Abinci sai dai na sadaqa da makota ke bata saboda tausayin da take basu. Ga yara har uku kyawawa amman yunwa duk ta jeme su.

Haka kawai take rayuwa sakaka sam ba dadi.. Kullum cikin kai kukanta take ga Allah madaukaki da ya yaye mata wannan kangin rayuwa.

....Ta runtse idanu ta bude hawaye na dada kwaranya daga idanun nata..

"Ke Fadila... Fadila."
Ta jiyo muryar Haladu na da da dukan kunnenta

"Ga ni nan.. Malam."
Ta fada tana mai gyara kwanciyar yaran ta fice da sauri zuwa dakin sa.

Ya dankara mata harara ya rufe kofar bayan ta shiga dakin na sa. Ladiyo ta tabe baki tana hararar kofar dakin da kallo ..

Ta jima aciki kafin ta fito daga dakin tana goge hawaye. Ragowar ruwan ta ta dauka ta shige bandaki tayi wankan tsarki. Ta koma daki ta cigaba da kaude kaude..

Tana cikin tattare kofar dakin ta. Sai ga shigar kanwar Haladu gidan. Da suke kira da Fatsuma wadda ke aure a yobe...

"Salamu alaikum.... Na ce Allah ya kawo mu. Kuma yad-da muka dama haka za'a sha...

"wa'alaykm salam..." Fadila ta amsa hadi da cigaba da tattare yar kasar dake zubowa ta saman dakalin dakin bakin kofar.

Dakin ya lume ciki. Yayinda tudun kyauren ke wajen gini..idan ana ruwa sosai ruwan ke musu gyara yana shiga ciki.

Wani lokacin a tsaye take har ruwan ya dauke. Idan dakin ya cika cikin dare. Sai ta goya 'da daya a baya. Daya ta dora shi akan wuyan ta. Yayinda daya ta rike a hannunta.

"Wai ko bakwa jine? Ni fa wulakanci ne banaso... Yanzun sai na yage zani mu daku da mace"

"Ah lale.marhaban... Fatsuma sannu da zuwa." Ladiyo ta fada. Hadi da tafa hannuwa tana dashare hakora.

Fadila gabanta ya yanke ya fadi.. Domin a duk sanda Fatsuma zata zo. Sai ta baqanta mata rai sunyi rigima. Gabanta na duka haka ta yi ta maza ta gyara zaman dankwalin kanta ta fita tsakar gidan fuskar ta dauke da fara'a

"Sannu da zuwa Fatsuma.. Anzo kalau?"

"Hmm ashe kina jina kikayi kunnen uwar shegu ki kai gum da bakin ki. "

"Kai Fatsuma kiyi hakuri. Ban waye ki ba. Sai da Ladiyo ta kamo suna."

Fatsuma ta yatsina fuska hadi da juyar da kai gefe ta kaikace kai..

"Ina Haladun?"

"Yana dakin sa"

"Haladu. Haladu.. Haladuwalle dan uwa rabin jiki."

Haladu ya bude kyauren dakin sa ya zura kansa waje.

"Menene?"

"Kai Haladu ... Ba sannu da zuwa sai ya tambayar menene? Daman zuwa nayi akan alkawarin da kayiimun."

Ya yamutsa fuska .

"Ki dauki duk wanda yayi miki arai,. "

"Godia na ke Haladu .. Ga daquwa tsaraba"

Ta mike ta kai masa. Ya karba ya koma dakin sa ya rufe.

"Muje daki akawo miki abinci."

"To Ladiyo."

Fadila tayi murmushin yake. Ladiyo da Fatsuma suka shige dakin na Ladiyo.

Ita kuma Fadila ta koma cikin dakin ta. Tana shiga ta rarumo yaran nata ta rungume su. A dukkanin halin data samu kanta na matsatsi da uqubar rayuwa data roki Allah kofofin rahamar sa da saukin rayuwa. Zata rungume yaran nata. Kallon su kadai na rage mata damuwa. Haka zalika idan ta rungume su takan samu kanta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.

Bayan wayewar gari... Fatsuma ta shiga dakin Haladu sukayi maganganun da zasuyi.

Ta yiwa Ladiyo sallama ta shiga dakin fadila. Suka gaysa. Ta mike tana duban yaran na fadila. Kafin ta saka hannu ta sunkuce Hadiyyah.

Wani karamin hoto dake jikin kusa na yaran su uku Fatsuma ta dauka ta zura a jakar ta.

"Toh da alheri. Duk sanda muka shigo kano zan kawo Hadiyyah ta gaysa da yan uwan ta."

Ta saka kai ta fice. Fadila ta bi bayanta jikin ta na rawa . Yayinda idanuwan ta suka fara zubar da ambaliyar hawaye.

"Bangane ba Fatsuma.."

"Toh uban yaran shi ya bani damar na dau dik wanda nake so ya bani rai da mutuwa. Alkawari ne ya yi mun tun tuni. Ladiyo yaranta manya ne kuma ba yaran Haladu bane tunda ubansu daban. A bazawara ya aure ta.. wadanda suke gabanta yanzu kuma basu mun ba. Ba zan dauka ba. Yanzu dan na dauki daya daga cikin uku da Allah ya baki shine kike kuka? Kashe ta nace zanyi? Karki manta bantaba haihuwa ba. Ai ko kara kyamun. Amman baki cancanci ma na dinga bata lokaci na ba ina miki bayani tamkar wata ishasshiya. Sai watarana ." Tana karasa fada ta fuce daga gidan da sauri.

Mota hayis dake jiranta da yan bikin da suka zo tare ta shige suka tafi. Fadila ta koma kuryar dakinta tana zubar da hawaye.
Chapter 3 · 0% Book details