← Book details Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 66

Sashe 26

Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Gaskiya Malam. Ban tabbatar da haka halayen ka suke ba sai tunkarowar wannan magana ta siddiqa. To inaso ka bude kunnuwan ka kaji. Uba a sunan yanka kake awajen siddiqa. Yan uwan ka ma iyayen ta ne. Haka na bangare na ma iyayen ta ne. Don haka ba sai da kai ba. Za'ai komai a gama. Ala barshi idan daurin auren ya gabato a sanar da kai." Ta karasa zancen hadi da buga tsakiyar zaninta ta saki katon tsaki ta wurga masa harara ta koma cikin daki.

Tana shiga daki ta cigaba da mita. Siddiqa da ke zaune tana nunke zannuwanta ta daga idanu ta dube ta.

"Menene ya faru?"

"Bakya jiyo kururuwar baban ku ne? "

"Da ke mp3 dina a kunne ta ke."

"Hmm. " Safiya tayi kwafa. Ta nemi gefen katifa ta zauna .

"Ai ingaya miki baban ku ni na kasa ganewa kamar mai bakin ciki da hassada. Kememe yaki har ya na cewa idan Allah yayi ba zaki aure shi ba dukkanin abubuwan da za'ayi ba zaki aure shi ba "

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun..."

"Hmm! Ke dai bari kawai. Ai sai dai yaji ranar bikin kawai kamar tashin bomb."

"Gaskiya baba bai kyauta mun ba."

"Bar dan abu takazar ubancan." Safiya ta bata amsa. Batare da ta kwabi yarinyar akan aibata mahaifin nata data yi ba. Itama ta kunduma zagi ta hadashi akan sunan mijin nata.

××RAFIN KANYA××

Bayan sun kammala jarabawar kare karatu ta sakandire sunyi jarabawar jamb da post utme. Su ummy suka hada kayan su zuwa kauye..

Kutsawa suke yi suna ta tafiya da kafafun su. Tun bayan da motar da suka hau ta sauke su a titi.

Sanye Fareeha da Madeeha suke cikin wasu dogayen riguna bakake da Hibba ta kawo musu tsaraba lokacin data je hutu Dubai.

Ya yinda ummy ma ke sanye cikin atamfar da mahaifiyar hibban ta bata a sallar baya.

Junaid na bayan su rike da ledoji dauke da kaya aciki

"Kai na gaji da turmutsun kasar nan wallahi. Sai wani shigewa take cikin takalma." Fareeha ta fada tana mai zare takalmin ta covered shoe da kasa ta shiga ciki ta karkade.

"Ke ki dago kafa" Madeeha ta dubi Fareeha. Fuskar ta dauke da murmushi.

"Ke sai wani dadi kike ji... Mun zo kauye."

Madeeha abunda Fareeha ta fada ya bata dariya. Tayi murmushi kawai tana wasa da damun geron da ke gefen ta.

"Tabbas dadi nake ji. Kinga tumun nan gasashi nake so nayi na ci da mun karasa."

Takaicin maganar Madeeha yasa Fareeha ta tabe baki hadi da yamutsa fuska.

"Meye abun so a wani tumun gero oho."

"Hmm Fareeha kenan. Tawa rabin rai. Ke fa na lura idan kina ciwon mara kinfi kowa mita."

Sukayi murmushi baki daya. Kafin ummy ta dan daga murya. Da ke tuni ita da Junaid sun kere su Fareehan.

"Ba zaku dago kafa ba?"

"Gamu nan ummy." Madeeha ta fada tana jan hannun Fareeha.

"Na tsani kauyen nan wallahi."

'lafiyar ki kuwa yau Fareeha? Kauyen na ku kika tsana? Lalle wannan ciwon marar na wannan karon ya zo miki da zafi. Chab."

Bata sake cewa komai ba tayi gaba abun ta. Fareeha ta bi bayan ta tana kananun mita.

Sunyi tafiya mai dan tsawo kafin su fara shiga cikin kauyen. Masu mashin na daga gefen bakin kasuwa suna jiran masu hawa.

Suna ganin su ummy suka tashi mashinan. Su ummy suka hahhau kan acaban. Aka kai su inda zasu sauka.

Gidah ne madedeci na masu karamin karfi da wadatar zuciya da ke kauyen na rafin kanya.

"Ah'ah'ah Innarajo ga su Mardeeya."

"Kai Gwaggo sunana Madeeha fa ba Mardeeya ba. "

"Ke ni bazan iya ba. Mardeeyan dai zan ce. Da waseelah"

"Yasin sunana Fareeha ba waseelah ba."

Suka tuntsire da dariya baki daya. Kafin su karasa wajen kakar ta su Innarajo. Ta tsufa sosai..An kwantar da ita akan wata yaloluwar katifa. Idanunta a rufe ta makance bata gani.

"Innarajo ga su junaidu yan birni." Gwaggo ta fada da karfi a dede kofar kunnenta

"Ah.. suna ina? Lale marhaban."

"Ga mu nan kakus..."

"Innarajon mu .."

"Inna tah..." ummy ta fada. Hadi da matsawa kusa da innarajon ta saka hannuwan ta akan kafafun innarajon tana matsa mata su.

"Hadiza ce.?"

"Eh ni ce inna.."

"Kinje makarantar? An baki kudin makarantar?" Innarajon ta shiga surutai irin na tsufan nan.

Ta basu tausayi dukkanin su. Ummy ta rungume ta tsam ajikin ta tana hawayen itama.

Aka dai yi yan koke koken qarin tsufan innarajon kafin daga bisani su shiga hirar yaushe gamo da su gwaggo da Bappah Borkindo.

Kwanakin su goma sha hudu a kauyen na rafin kanya. Tukun sannan suka dauki hanyar dawowa zuwa cikin kano gidah.

Da sati uku ma sukayi niyyar yi. Sai Yazed ya kira waya kan jarabawar su Madeeha ta futo. Labari ne mai dadi da babbar samun cigaba ga rayuwar karatun su Madeeha.

Madeeha ta samu gurbin karatu na scholarship a makarantar gaba da sakandire. Kuma babbar makarantar da ake ji da ita a kàsa baki daya.

Makaranta ce ta reshen kasar ingila. Wanda ko a masu kudin ma sai wanda ake damawa da su ne kan samu gurbin karatun acikin ta.

Birmingham University Nigeria (university in kano) Jami'ace da ke garin Kano . Itace makarantar gaba da sakandire da Madeeha ta samu gurbin karatun kyauta tun daga aji na daya zuwa na karshe .

Wani farin ciki na biyu ha'ila yau mahaifi ga Yazed ya biyawa Fareeha kudin makarantar itama ita da yar cikun sa Hibba. Da wasu yara su goma a karkashin campaign din kujerar takarar sa ta siyasa.

Ranar don dadi hawaye suka din gayi sosai. Aka rasa me hana wani yi acikin su.

Suka shigo garin Kano da tarin kayan kauye. Ummy ta shiga tayiwa iyayen Yazed godia bisaga abubuwan arzukan da suke musu a rayuwa. Bayan matsugunin da suka basu na kwana da daukar duk wani wahalar su na ci da tufatarwa.

Komai da komai na yan makaranta sai da Alhaji Abdulrashid ya sayawa su Fareeha... Lamarin sai godiya ga Allah mubuwayi gagara misali...wai su Fareeha da Madeeha ne zasu yi jami'a. Jami'ar ma ta kudi ta 'ya'yan manyan masu kudi na kasa baki daya. ... Birmingham University Nigeria (University in kano)

.
_INA JAMA'AR TA MU? KU MARMATSO KUSA . GA TAGOMASHIN ARZIKI. SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI. MUN GWADA DOLE MU BADA SHEDA_

_INA AMARE, UWAYEN GIDA, YAMMATA? IYAYE MAZA DA KE SON FARANTA RAYUKAN MATAN SU DA YAYAN SU DA MA KANNEN SU?_

_ALBISHIRIN KU. GA GORO. DOMIN WANNAN DADDADAN LABARI DOLE MU BAKU ALBISHIR DA ALHERIN GORO. GORON MA FARI KAL KAL_

_WAI AKACE KAMSHI RAHAMA NE... KAMSHIN MA MUSANMAN ME SANYAYA ZUCIYA DA RATSA MAGUDANAR JINI DA TSOKA._

_INA MASU NEMAN KAMSHIN TURAREN SAUDI ARABIA? T'CHAD DA MAIDUGURI? IRE IREN KAMSHIN DA BAYA BIN ISKA YANA KAMA WAJE YA RIKE GIDAH..._

_KAMSHIN TURAREN KAYA, TURAREN GIDA, TURAREN JIKI, TURRARN GASHI, TURAREN TSUGUNNO, TURAREN WANKA, TURAREN WANKI, TURAREN MOPPING, TURAREN BANDAKI, TURAREN LABULAYE DA ZANNUWAN GADO, AIR FRESHENER DA TURAREN AKWATUNA DA DRAWER DA MOTA... KAI HAR MA DA TURAREN DA KE CIRE BACIN RAI YA MUSANYA DA FARIN CIKI SABODA TSANANIN SANYAYAWAR SA DA YAYE DUHU DA DAMUWA_

_BA ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNADA NAU'IKAN TURARUKA NA KHUMRAH KALA KALA. SUNADA TURAREN RUWA NA FESAWA DANA MAIKO. SUNADA KAYAN GYARAN JIKI.._

_SUNADA KULACCA DA SAURAN BODY BUTTERS MASU YAYE WARI KODA KUWA AN YI KWANAKI BA WANKA BARE WANKI._

_SUNADA KABBASA TA TURARA KAYA DA KASAKEN TURARUKAN WUTA NA KARFE DANA KASA DAMA NA ZAMANI YAN WAJE._

*_YERWA INCENSE AND MORE_*

_YERWA INCENSE AND MORE_

_YERWA INCENSE AND MORE_

_MASARAUTAR KAMSHI KENAN. KAYAN SU NA AKAN FARASHIN SARI DA SAYA DAYA DAYA.. SUNA YIWA AMARE HADI DA UWAYEN GIDAH DAMA YAMMATA. SUNAYIN NA TARON SHAGULGULAN BIKI DUK AKAN FARASHI MAI RAHUSA_

_BA'ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNA DA TARIN KAYAYYAKI MASU KYAU DA RAHUSA HADI DA INGANCIN DA ALKALUMA SUNYI KADAN WAJEN BAYYANA MUKU._

_SUNA TURA KAYAYYAKIN SU FADIN NAJERIYA DA KETARE BAKI DAYA._

_ADIRESHIN SU. SUNA GARIN KANO DAURA DA TITIN DA ZAI SADAKA DA GARIN MAIDUGURI_

_SUNA KAN MANHAJOJIN SU DAKE KAFAFE DA DAMA KAMAR:_

_INSTAGRAM: @yerwaincense_and_more_

_FACEBOOK:yerwacollection_

_WHATSAPP: 08095215215/09044191709_

_A YANZU HAKA KAMFANIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE SUNA SALES DIN KAYAN SU NA 250ML NA TURAREN WUTA DA KUMA 240 DA 190ML NA KHUMRAHS_

_IDAN ANJE ACE DAGA ZAFAFA NE AKWAI RAGIN KUDI DA HADI NA MUSANMAN DA ZAA YIWA DUKKANIN KAYAN DA KUKA SAYA._

_KYAU!! INGANCI! RAHUSA!! KAMA JIKI DA GIDAH!! AIKI!! ADADE ANA MOREWA SAI KAYAYYAKIN TURARUKAN KAMFANIN:*YERWA INCENSE AND MORE*_

_____
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥

0022419171
Maryam sani
Access bank

*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

_𝕂𝕀 𝕂𝕌𝕃𝔸 ℕ𝕀!!_
_(𝕄𝔸𝕃𝕃𝔸𝕂𝕀ℕ ℤ𝕌ℂ𝕀𝕐𝔸)💕_

_ℕ𝔸ℕ𝔸 ℍ𝔸𝔽𝕊𝔸𝕋_
_𝕄𝕀𝕊𝕊 𝕏𝕆𝕏𝕆_

_ℙ𝔸𝕀𝔻 ℙ𝔸𝔾𝔼:23_

_ZAFAFA BIYAR 2023_

_

    *Da* wurwuri Madeeha ta tashi bayan tayi sallar asubahi bata koma ba. Aikin da yake a matsayin nata da ummy ta raba musu kullum su ta fara yi.

Ta wanke dukkanin bandakunan nan ga ruwa nan a famfon da ke ciki. Ta share parlor hadi da goge shi da mopper.

Ta kusa karasa aiyukan ta ne Fareeha ta tashi bakin ta dauke da addua.

"wai har kin kusa gama aikin ki?"

"Eh mana... Na ma gama nan kadai nake jira ki tashi na tattare."

"Chab.. Kai na gaji wallahi da wadannan ayyukan Madeeha. Yanzu mu da masu kudi ne da muna daga kwance ma'aikata zasu mana komai. Sai dai suce Hajia ko aunty dan 'daga kafarki zan tattare nan."

Madeeha ta juya kalli Fareeha tana mai mamakin kalaman ta. Cikin mamaki ta sake daga kai ta dube ta.

"Wai rabin rai meye ne kike ta kallo na?"
Chapter 26 · 0% Book details