← Book details Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 66

Sashe 10

Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ka dafa ki manta akan ki da yara na ciyo bashikan. Ankon abasiyyan hashire kince mala yadi ce ke ba zaki dinka ba sai les. Mukaje kasuwa na saya miki dandatsetse da yari (dan kunne) Sa'ilin nan yaron nan aqeelu shima ya jajibo fada ya ciyo kudin mutane nan ma kika tàsani agaba na ciyo bashikan na biya masa. Yarinyar nan hafsatu zasuyi maulidi kika sakani agaba sai da na ci bashi na saya mata dakwalen kaji har biyu na bikin maulidi da shadda yar wambai da farin hijabi. San....

"Sannan me? Dakata me gidah ni banason sharri. Banda boye boye. Borin kunya yasa kazo kana lissafin abubuwan da kayi mana. Bayan manyan kudaden da ya saka ake neman ka waya saka ka ciyo su idan ba kankin kanka ba? Ra'ayin ka ne bakai shawara ba wai kai zaka sayo mota ka dinga hayar gari gari ka ciyo bashi ka sai mota. Yan fashi da suka fika so suka garkaneka suka kwace mota. Banda sharholiyar da kuke kai da su badamasi a yar kasuwa. Ummimi gidan sallau me ido daya ance har abada kuna tare . Su kuke kashewa kudi. Lemon kwalba da kajin rudiyye anc...

Bata karasa ba auwali ya zundumawa kawu Ashiru kira. Da sauri jikin sa na bari ya fito daga dakin.

Auwali yayi kansa . Kawu Ashiru ya goce da sauri yana daga hannuwa alamun roko.

Hakan yasa ummy dake daki ta fita da sauri jin karar magiyar kawu Ashirun tayi yawa ba zata iya shiru ba. Duk kuwa da tayi shiru ne da fari don gudun maganar su .

"Bawan Allah kayi masa hakuri dan Allah. "

"Baiwar Allah babu ruwan ki ... Kinji ko?" Cewar auwali. Yana mai daga mata hannu alamar ta dakata.

"Tsaya tsaya zan baka ashirin din. Naji naji zan baka " kawu Ashirun ya fada yana sauke numfashi.

Kai tsaye yayi inda katuwar akuyar Ummy take a daure. Ta kusa haihuwa ma. A kwance take. Ba imani haka kawu Ashirun ya sunce ta ya riko kafarta daya yana janta

Su Fareeha suka fito daga dakin da sauri . Ummy ta saka musu hannu da su dakata. Fareeha ta fashe da kuka. Domin akuyar ita kadai ce kadarar su. Ummy taketa kiwon ta. Tace idan ta haife yaran ta shayar da su sai a sayar ta. Zata biyawa Junaid kudin makaranta da yakeyi ta gaba da sakandire. School of science and technology.

Amman saboda tsabar rashin Imani. Kawu ashiru yayi gaba da akuyar. Yayinda auwali ya biye masa a baya.

"Amma ummy d..."

"Ya isa hakanan..." Ta dakatar da su.

"Ungo ku rike kudin tara. Ku wuce ku tafi . Allah yabada sa'ar karatu." Tana mika musu kudin ta koma daki

Su kuma suka fice zuwa makaranta . Rayukan su duk ba dadi akan fin karfin da ake nuna musu akan su da ma dukiyar su da suka mallaka.

Ta taga ta leka taga sun fice. Hawayen da take ta ajiyar sa ne. Suka shiga silalowa daga idanun ta. Masu dumi da alhini. Sosai take kukan ahankali. Zuciyar ta na zafi. Ta matse idanun nata. Hawayen nata suka shiga reto a kyakkyawar fuskar ta.

"Yaa Allah... Ka na ga ni.. Allah ka bi mana hakkin mu " Ta fada ahankali tana jujjiya kai cikin karshen damuwa da tsantsar firgici...

"Yaa Allah kana gani.... Allah kai mana sakayya..." Ta sake fada tana zubar da hawaye sosai......

MSS XOXO WRITES✓✓✓

_𝕂𝕀 𝕂𝕌𝕃𝔸 ℕ𝕀!!_
_(𝕄𝔸𝕃𝕃𝔸𝕂𝕀ℕ ℤ𝕌ℂ𝕀𝕐𝔸)💕_

_ℕ𝔸ℕ𝔸 ℍ𝔸𝔽𝕊𝔸𝕋_
_𝕄𝕀𝕊𝕊 𝕏𝕆𝕏𝕆_

_ℙ𝔸𝕀𝔻 ℙ𝔸𝔾𝔼:09_

___
**GOVERNMENT GIRLS JUNIOR/SENIOR SCHOOL**

Tun kafin su karasa harabar cikin makarantar suka hango cincirundon taron yan latti.

Gaban Fareeha ya yanke ya fadi. Ta dubi Madeeha da sauri cikin muryar tsoro mai tattare da fargaba tace,

"Shikenan mun makara Madeeha.. Zo mu koma gidah kawai."

Madeeha ta dubeta ta tabe baki hadi da kamo hannun Fareeha taja suka tunkari gate din makarantar da sauri.

Fareeha nata kiciniyar kwacewa. Idanuwan ta sun kawo ruwa sosai saboda tsabagen tsoron dukan latti da ta ke.

"Wai kin manta yau zamuyi test din malam Ali? Zaki ce mu koma gidah mu fadi test din kenan. Duk lefin kawu Ashiru ne. Allah yai mana sakayyah. Yadda ya kwace akuyar Ummy da mugunta kamar tasa. Insha Allahu ya dinga ganin ibtila'i kenan a rayuwa ..."

"A .m..in" Fareeha ta amsa muryarta na kakkarwa. Alokacin data hango malam me dukan latti.

Ya daga dorinar sa me baki uku. Yanata wullata yana cabewa. Ta bayan wasu dalibai Madeeha ta shigar da su. Fareeha sai nokewa ta ke.

Da karfi cikin cikar kuzari madeeha ta tura Fareeha ta cikin gate din lokacin da baba me gadi ya bude .

"Kai kai ku zo nan dan uban ku. Makararru."

Madeeha ta karasa da sauri tana turo baki.

"Malam ni ba yanzu na zo ba. "

"Karya kike yi."

"Haba Malam... Kasan dai kullum tare muke da kanwata kuma tana ciki...."

"To meya fito da ke.? Iyye"

"Biro na na wullar.... Shine na fito dubawa "

"Yanzu yana ina?"

"Bangan shi ba."

Malam ya daga kai ya dubeta .. Ya juya ya dubi cikin harabar makarantar ya hango Fareeha.

Dan tabe baki yayi. Ya ce da ita

"Je ki .. ki ka sake irin wannan hukuncin na fitowa ana tsaran latti wallahi sai na zane ki "

Ta daga kai kawai tana lankwasa yatsunta

"Wuce ki shige."

Da sauri ta shige cikin makarantar hadi da sauke nannauyar ajiyar zuciya. ...

Fareeha ta rungumeta ajikinta. Itama tana sauke zuciya.

"Kar ki sake irin haka Madeeha... Kinji ko?"

Dan murmushi madeeha tayi .

"Ai shiya sa nace ki cire tsoro a ranki. Allah yaga zuciyar mu. Da daura niyyar da mukayi saboda tun asubah ba mu koma ba. Kawu Ashiru ne ya janyo lattin nan."

"Naji na ji... Ni dai ki dai na cire ni a komai kina dorawa kan ki lefi. Ba na so .. ki dai na kinji?"

"Na ji rabin rai...."

Dariya suka tuntsire da ita. Kafin daga bisani su shige ajikin su. Da sauri suka samu wajen su suka zauna. Malamin har ya rubuta tambayar test din da zasu yi. Paper suka yayyago suka rubuta sunayen su. Suka rubuta tambayar tukun sannan suka fara rubuta amsoshin su .

Suna da kaifin basira... Nan da nan suke rike karatu na kowanne sashe na daga arabi da boko.

Gaba daya daliban sun kai tsawon awa daya da rabi suna amsa tambayoyin kafin lokaci ya cika. Malamin da kansa ya zazzagaya wajen teburin da daliban suke a zazzaune ya karbi takardun na su.

Sannu a hankali haka suka karashe dukkanin sauran darussan su na ranar.

Lokacin tara ana kada kararrawa suka nufi wajen iya me awara. Daman kamar ko yaushe idan da kudi a hannun ummy tana basu nera hamsin su biyun. A tare suke ciyayya. Su sayi awarar ashirin. Wainar fulawa ta ashirin sai Kuma su sayo ruwan sha goma na leda pure water.

Sam ba subi ta kan su khairiyyah da batoul yaran kawu Ashiru. Da sukan musu magana. Kafin su amsa su sai sun mula sun ga dama tukun suke kulasu. Suna gefen me dankalin hausa suna ci suna korawa da fan ice .

Hakan ya sa Madeeha ta dire rantsuwa kan lalle ta dena musu magana. Tunda ko a gidah basa musu magana. Tunda dai suna musu basa kula su koda sun musu. Wannan ne ya sake tunzura madeeha . Ta kafa takunkumin suma wallahi sun dena kula su.

Daman ko a gidah ma iyayen su su kawu Ashiru da Rahila basa bari suyi musu magana. Ko aamsa suka basu ranar sai sun sha bugun mahaifin su Ashiru kuwa.

Wannan ne yasa zuciyar madeeha ta kekyashe. Inde ba dole akayi mata ba kan ta zumunci da su ..

Awa daya na cika aka kada kararrawar komawa aji.. Wani malamin da ke musu social science ne ya shiga.

Madeeha da Fareeha suka mayar da hankulan su sosai wajen daukar darasin malamin. Ya iya koyar wa yana musu darasin cikin kulawa da yadda zasu gane dalla dalla.

×YAN TUMAKI×

     Turken Malam Falalu suka je me sayar da tumaki. Kawu Ashiru ya ja akuya ya kaita har gaban Falalu yana sauke numfashi.

Domin akuyar na dauke da ciki tayi nauyi sosai. Dakyar ya ja ta ya kai ta turken Falalu.

Auwali na daga gefen sa ya murtuke fuska. Falalun ya dube su ya sauke idanun sa akan akuyar.

"Kalau?" Ya tambaya yana kallon kawu Ashiru da alamun tambaya.

"Eh akuya zan sayar "

"Toh...." Falalu ya fada. Hadi da dora hannun sa akan akuyar

"Kudi hannu kake so?"

"Eh.." Kawu Ashiru ya amsa shi yana raba idanuwa.

"Ai ni Ashiru tsoron shiga lamarin ka na ke. Musanman dukkanin abun da ya shafi harkar kudi. Sam ba kada yaddaa akai. "

Kawu Ashiru ya matsa wajen Falalu sosai tamkar zai koma cikin sa.

"Kudi hannu na ke so Falalu .. a matse na ke da girman Allah kaga wannan mutumin shi zan yiwa biyan bashi. Sauran kudin ma basu hadu ba. Ka temaka mun Falalu."

Falalun ya daga kai ya sauke akan auwali da ke cika yana batsewa,

"Kai Ashiru kayi sauri.... "

"Yanzu kuwa... Kaji ko Falalu? Dan Allah ka temaka ka saya. "

"Ni yanzu ba kudi a hannu na. Zaka tatikemun aljihu wallahi."

"Ka temaka Falalu."

"Shikenan ba damuwa. Rike.. ungo ga su." Ya zaro kudade ya mikawa Ashiru.

"Yauwa Falalu godiya na ke. "

Matsawa yayi ya koma wajen auwali ya mika masa kudin. Ya karba ya zura a aljihun gaban rigar sa.

Sannan ya daga kai ya sauke akan Ashiru kafin yace da shi,

"Na baka kwana ki uku. Ka gaggau ta cikato sauran kudaden nan namu. Idan ba haka ba. To ka kuka da kan ka. "

"Godiya na ke maigida na. Allah ya sakaa maka da alkhairi."

Hannu kawai ya iya daga masa ya fice daga yar kasuwar sayarda tumaki.

Kawu Ashiru ya jima a tsaye yana sakewa da warewa kafin daga bisani ya dauki haramar komawa gidah.

\\\\\\\\\\\\\\\\\\/////////////////////

A matukar gajiye ya dawo gidan. Tsit gidan babu hayaniya. Hakan ya tabbatar masa da yaran na makaranta basu dawo ba.

Dakin sa ya wuce yana tafe yana jera atishawa. Yabude dakin sa zai shiga kenan ya hango mahaifiyar ta su a zaune ta kofar dakin ta.
Chapter 10 · 0% Book details