← Book details Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 66

Sashe 38

Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

_SUNA TURA KAYAYYAKIN SU FADIN NAJERIYA DA KETARE BAKI DAYA._

_ADIRESHIN SU. SUNA GARIN KANO DAURA DA TITIN DA ZAI SADAKA DA GARIN MAIDUGURI_

_SUNA KAN MANHAJOJIN SU DAKE KAFAFE DA DAMA KAMAR:_

_INSTAGRAM: @yerwaincense_and_more_

_FACEBOOK:yerwacollection_

_WHATSAPP: 08095215215/09044191709_

_A YANZU HAKA KAMFANIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE SUNA SALES DIN KAYAN SU NA 250ML NA TURAREN WUTA DA KUMA 240 DA 190ML NA KHUMRAHS_

_IDAN ANJE ACE DAGA ZAFAFA NE AKWAI RAGIN KUDI DA HADI NA MUSANMAN DA ZAA YIWA DUKKANIN KAYAN DA KUKA SAYA._

_KYAU!! INGANCI! RAHUSA!! KAMA JIKI DA GIDAH!! AIKI!! ADADE ANA MOREWA SAI KAYAYYAKIN TURARUKAN KAMFANIN:*YERWA INCENSE AND MORE*_

_____
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥

0022419171
Maryam sani
Access bank

*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

*Thanks for choosing us*🔥

_𝕂𝕀 𝕂𝕌𝕃𝔸 ℕ𝕀!!_
_(𝕄𝔸𝕃𝕃𝔸𝕂𝕀ℕ ℤ𝕌ℂ𝕀𝕐𝔸)💕_

_ℕ𝔸ℕ𝔸 ℍ𝔸𝔽𝕊𝔸𝕋_
_𝕄𝕀𝕊𝕊 𝕏𝕆𝕏𝕆_

_ℙ𝔸𝕀𝔻 ℙ𝔸𝔾𝔼: 32_

_ZAFAFA BIYAR 2023_

_*BIRMINGHAM UNIVERSITY NIGERIA_*
_(UNIVERSITY IN KANO)_

*YANA* tafe a mota hannun sa daya akan sitiyari. Ya yinda dayan rike yake da wayar sa yana karanta labarai da shafin BBC suka saka wanda ke kan manhajar Facebook.

Sannu a hankali ya karasa makarantar. Tun daga main gate kake iya jiyo sautin da ke nuni da cewa ana wata hidima a cikin makarantar.

Karasawa yayi wajen taron. A nata hada hada. Wasu na shiga wasu na fita. Kowanne yaci ado cikin shiga ta alfarma mai kyawu da tsada.

Tsayawa yayi yana bin su da kallo. So yake idanuwan sa su dora ganin su akan MALLAKIN ZUCIYAr sa.

Ya dan yi kamar mintina goma zuwa sha biyar a zaune cikin motar kafin ya fita daga ciki . Wayar sa a hannun sa yana duba call logs dinsa.

Lalubo number T-Boy yayi ya kira shi.

"Maza kuna ina? Alright! Gani nan."

Yana katse kiran ya mayar da wayar sa cikin aljihun gaban rigar sa.

Kai tsaye ya shige cikin wajen taron bayan ya nuna gate pass.

Wurin ya kaawatu da kwalliya gwanin ban sha'awa. Komai baki da fari. Harda kujerun zama da teburan su. Wato dai black and white semester party.

Wurin da aka rubuta vvip table ya nufa. T-Boy ne zaune da B-junior da Na'eem.

Sashen maza daban, Haka ma sashen mata daban yake. Kowane bangare ne tebura ne kashi kashi. Da suka kunshi fannin vip, vvip da ma regular table.

Bayan haka akwai malamai na kowanne bangare na makarantar. Akwai sauran staffs da ke aiki a makarantar.

Ciki harda vice chancellor da sauran masu manyan mukamai. Bayan an hallara aka sake yin addu'oi na musulunci. Saboda manyan bakin da suka sake zuwa, Sannan kiristoci ma suka wassafa bangaren su.

Daga nan kuma aka fara gudanar da dukkanin jadawalin maqasudin taron daya hada su.

Rayyan ya nufi wajen su T-Boy ya zauna bayan ya basu hannu sun gaggaysa.

T-Boy: "Maza an iso kenan...?."

Rayyan: "Na iso T-Boy..."

B-junior: " Maza..."

Rayyan: " sup bruh!"

Na'eem: "Cousin"

Rayyan :"Couz"

Bayan sun gaggaysa ne... Dukkanin su suna zaune akan teburi na alfarma na vvip. An cika su da ruwa da lemo da su cake da sauran desserts.

Masu kula da masaukin daliban nata hada hadar kakkawo wa kowane tebur abinci da abun sha da sauran kayan kwalam da makulashe.

Bangaren matan na kallon na mazan. A teburin farko baby saj-jeedah ta ke. Da Na'eemah kanwar Na'eem.. Da wata Fatima.

Teburi na biyu da ke kallon na su su Fareeha ne da Madeeha da Hibba da su Nawal da Nour.

Cikin ikon Allah Rayyan ya daga kansa daga screen din wayar sa dake hannun sa yana dannawa.

Yana juyawa hadi da ajiye idanuwan sa. Basu fada ba kan kowa ba sai Madeeha da ke murmushi tana kallon wayar hannun Hibba.

Wani bakon yanayi ne ya riske shi. Ya kasa janye idanun sa daga kanta. Sosai ya tsayar da hankalin sa da nutsuwar sa akan ta.

Bata sanma yanayi ba. Domin baki daya hankalin ta na kan wayar Hibba suna karanta wani labari da aka turo a blog.

Saj-jeedah na daga kai ta hango shi ya zubawa wani waje ido. Bin idanuwan sa tayi da inda ya tsayar da kallon na sa. Tana juyawa ta hangi Madeeha. Wani abu ya taso ya tokare mata a makoshin ta. Ji take tamkar ta tashi ta bubbuge madeehan.

"Mr Ray..." Saj-jeedah ta dan daga murya tana kiran sa.

Sam bai ji me take fada ba, Ya shagala da kallon Madeeha. Wannan abu da yayi ba kadan ba ya sanya wutar kiyayyar Madeeha ta kara ruruwa a zuciyar saj-jeedah.

Gashi ba dama ta tashi ta koma inda yake. An saka wani dogon karfe an raba tsakanin wajen zaman mata dana zama.

Rayyan ya dade yana kallon Madeeha. Bai janye idanun sa ba har sai da ita madeehan ta juya baya suna magana da wata course mate din ta.

Haka dai aka cigaba da gudanar da liyafar taron. Rayyan dai yaji dadin zuwa taron. Saboda idanun sa sun dau hotan fuskar Madeeha. Ya yin da zuciyar sa tayi gamo da abunda ta ke bege. Tabbas ranar ta kasance masa wadda ba zai taba manta ta ba.

Acikin abubuwan da za'a gudanar a taron akwai bada awards da za'ayi ga wasu malaman na cikin makarantar. Saboda kwazon su. Da kuma babbar gudunmuwa da sike bayarwa ga karatun da daliban da ke cikin makarantar baki daya.

Yazed na daya daga cikin malaman da za'a bawa kyaututtukan. Alokacin da za'a bashi ya nufi teburin su Madeeha ya bata wayar sa. Kan ta dauke shi a hoto a sanda aka mika masa award din

Hakan kuwa akayi. Ta fita zuwa wajen bashi award din. Sanye cikin kayanta da suka yo mata matukar kyau tamkar a sace ta a gudu. Saboda madaukakin kyawun da tayi. Abunda ya sake kara mata kyau ma shine jan jambakin da data saka a dan karamin labban ta.

Rayyan ji yake ina ma yaje ya hanata. Gashi mazan wajen duk sun zuba mata idanu. Hakan ya sosa masa rai saboda yana da tsananin kishi akan abunda yake so.

Ya tsiri mikewa tsaye don mazan bayan sa su dena kallon Madeeha ya kare saitin ta ya tsaya . Mutane nata ce masa,

"Dan matsa bama gani. Kaga dan matsa. Ha'a aboki na dan matsa bama gani....please check out... U're blocking our view ... Mr. Man please have a sit. "

Wadannan sune kadan daga cikin maganganun da mazan da ya kare musu ke ta fada.

Bai samu nutsuwar zuciya ba har sai da ta koma wajen zamanta ta zauna. Ya samu kansa da sauke nannauyar ajiyar zuciya. Har sai da su T-Boy suka juya suna tsokanar sa.

Na'eem ya danyi murmushi yana kallon Rayyan kafin yace da shi,

"Ka gaya mata u're into her?"

"Bangane ba."

"Ina nufin ka sanar mata sakon da ke cikin zuciyar ka?"

"Tukun na dai... Amman na fara nuna mata wasu abubuwan da kalamai."

"Gwara dai kayi gaggawar sanar mata. Kafin wani ko wasu suyi maka shigar sauri. "

Rayyan ya juya ya dankara masa harara. Hadi da sake gyara zaman sa yana bin Madeeha da waji kallo. Irin kalon nan mai sanar da sakon zuciya amma ta cikin idanu.

Na'eem ya sake kallon Madeeha sai kuma ya kalli Rayyan kafin ya sake cewa,

"Ina ganin ta a area dinmu. Yan biyu ne ma ko?"

"Eh Yan biyu... Jikin gidan ku suke ai."

"Oh really.? Kasan fa wannan malamin na mu agidan yake ai."

"Yazed yake ko Khaled dinnan ko?"

"Eh.. Yazed din. Gidan su daya kenan?"

"Maybe. Amma basa kama at all."

"Yeah ba sa kama. Ai da ba agidan suke ba. Cuz da ba kowa agidan ma sai wasu ina tunanin masu jiran gidan ne. To daga baya yam gidan suka dawo daga kasar waje. "

"Oh okay.."

"Yeah... Kasan wani abun mamaki?"

"Na me fa?"

"Suna mun yanayi da su Hajia fa a fuzge. Ina nufin su Madeeha din da wata ."

"Oh please..."

"No dagaske na ke... Sai dai ance kowa yana da me kama da shi Allah akwai wata yar babba haka ba wani can ba. Tana yanayi da su Bappah"

Takaicin kalaman sa ya sa Rayyan ya juya ya masa wani kallo kafin ya tabe baki hadi da yamutsa fuska kawai.

Na'eem ya kyalkyale da dariya kawai shima. Kafin yace,

"Wata rana zaka gani.."

Ya juya suka cigaba da hirar su da su T-Boy.

An ci an sha an gyatse. Kafin ashiga fun activities. Su Madeeha suka tashi suka tafi bayan Yazed ya ce su futo su tafi.

Alokacin Rayyan an kira shi a waya ya tashi ya fita. Ko da ya dawo bai samu haduwa da su Madeeha ba. Yaci je lebe ransa duk ya jagule.

Suma basu wani dade ba yayi musu sallama ya tafi gidah. Yaso ya sake ganin Madeeha kafin su tafi.

Yana driving yana hasaso dazu da yake kallon ta. Tana magana tana kallon wayar dake hannun wadda suke tare

Kyawun ta. Dan karamin bakin ta, kyakkyawar surar ta dama lafazin muryar ta, Jan ajinta, mutuncin ta, basirar ta, Kai . Komai nata ya na burgeshi sosai.

*NEW NASSARAWA GRA*

Hannunta yana rawa ta janyo tsohon da ke ma'adanar data ajiye shi. Da sauri gaban ta ya shiga bugawa alokacin da ta.....

_
_INA JAMA'AR TA MU? KU MARMATSO KUSA . GA TAGOMASHIN ARZIKI. SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI. MUN GWADA DOLE MU BADA SHEDA_

_INA AMARE, UWAYEN GIDA, YAMMATA? IYAYE MAZA DA KE SON FARANTA RAYUKAN MATAN SU DA YAYAN SU DA MA KANNEN SU?_

_ALBISHIRIN KU. GA GORO. DOMIN WANNAN DADDADAN LABARI DOLE MU BAKU ALBISHIR DA ALHERIN GORO. GORON MA FARI KAL KAL_

_WAI AKACE KAMSHI RAHAMA NE... KAMSHIN MA MUSANMAN ME SANYAYA ZUCIYA DA RATSA MAGUDANAR JINI DA TSOKA._

_INA MASU NEMAN KAMSHIN TURAREN SAUDI ARABIA? T'CHAD DA MAIDUGURI? IRE IREN KAMSHIN DA BAYA BIN ISKA YANA KAMA WAJE YA RIKE GIDAH..._
Chapter 38 · 0% Book details