Sashe 55
Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bappanin sa ne su uku sai Hajiya Fadila kakar su da kuma Anty Kulu matar Bappah Haydar kuma mahaifiya ga su rayhan da Na'eem.
Gayshe su yayi dukan su yana bin motar da kallo. Hajiya fadika tace da shi,
"Dan yaye kauye zamuje.. ka dawo adaidai dama yanzun na ke son cewa a kiramun kai nace maka zamuyi tafiya. Yi maza ka shiga ciki kaci abinci kaji? Mu ma ba dadewa zamuyi ba da yardar Allah.." Tace da Rayyan fuskar ta qumshe da farin ciki.
"Tohm Hajiya... Allah ya kai ku lafiya ya dawo da ku lafiya."
"Aamin Yaa Rabbi..."
Ya dan saka hannu ya sosa keyar sa yana kallon Hajiyan.
"Wani abun kake so ne dan yaye?"
Rayyan ya girgiza mata kai yana dan girgiza takalmin kafar sa daya..
"Ka tabbata?" Ta sake tambayar sa. Domin ta gano akwai abunda yake son cewa,
Jan kasan leben sa yayi ya ciza kafin yace,
"Hajiya.... Wata nagani wallahi kamar su daya da su Bappah."
Gaban Hajiya Fadila ya yanke ya fadi. Ta dube shi cikin rawar jiki da baki.. Yayin da su bappan ma sukayi kansa suna jiran karin bayani.
"A Ina ne Rayyanu?" Hajiya Fadila ta tambaye shi cikin kidimewa..
"A kusa da gidan Bappah Hydar."
Alhaji Hydar yayi murmushi . Duk suka juya suna duban sa yace
"Hajiya dama na gaya muku ai .. Inde ba gizo take mana ba Allah hadiyya ce."
Hajiya Fadila ta sauke nannauyar ajiyar zuciya kafin tace,
"To ai ita wannan kace daka bincika sunan ta hadiza aka ce maka ko?"
"Kwarai haka zancen yake Hajiya."
Hajiya Fadila ta sake sauke gwauron numfashi kafin tace,
"Muje dai kauyen da aka fadadin.. Allah kuma ya amince mana Amin."
"Aamin..." Suka hada baki wajen amsa adduar ta.
Motar suka shisshiga. Bappah Harith ne me tukawa da Hajia Hindu a gefen sa. Su kuma su Hajiya suka shiga baya yayinda kujerar tsakiya Bappah Hydar ne da anty Kulu. Sai kuma kujerun karshe bappa Hammad ne da Hajia Fadila.
Rayyan bai dena kallon su ba har suka fice daga gidan sannan ya saka kai ya shiga ciki bakinsa dauke da adduar fatar samun nasara...
××RAFIN KANYA××
Basu wani dau tsawon lokaci ba suka karasa kauyen na rafin kanya.. Hajiya Fadila da ke can baya ta dan daga murya kafin tace,
"Kun ce su Asabe da dan ta Yusha'u tuni sun karasa kauyen ko?"
"Eh Hajiya.... Yusha'un ma yace zasu zauna a sakateriyar kauyen kafin mu karasa."
"To Alhamdulillah.."
Suka karasa wajen sakateriyar kauyen..Suka dauke su . Asabe ta shige wajen Hajian itada Anty Kulu. Yusha'u kuma suka zauna shi da Bappah Hammad .. A haka suka karasa har kofar gidan bisaga kwatance...
Wani yaro suka tura ciki kan ya yi musu iso kafin su shiga.. A lokacin kuma Innarajo ce taketa surutai tana mai nanata,
"Allah ya bayyana miki iyayen ki... Allah yasa karshen wahalar kenan... Zo ki karbi kudin makarantar ki tafi."
Ummy ma gafenta tana zubar da hawaye.. Dan hotan su da ke yar jakarta ta zaro tana kallon su su uku. Ta saka hannu tana shafa fuskokin su. Ya yinda hawaye daya na bin daya suka shiga reto a kyakkyawar fuskar ta.
Su Madeeha ma hawayen suka shiga zubarwa... Bakunan su dauke da adduar samun farin ciki ga mahaifiyar ta su ummy.
Yaron ne ya shiga yayi sallama. Hadi da cewar wasu mutane da suka zo daga birni cikin wata zungureriyar mota suna neman a musu iso su shigo ciki.
Borkindo ya mike da yar rediyon sa a hannu ya fita. Ya dan jima kafin ya shigo da sauri yana hamdala.
A jere suka shiga cikin gidan. Lokacin su ummy na kallon borkindo da son sanin karin bayanin game da farin cikin da yake yana hamdala.
Hajiya Fadila ce agaba. Tana dogara yar sandarta tayi sallama ta shiga cikin gidan. Idanun ta suka sauka akan ummy da ke yiwa Innarajo firfita.
Take jikin ta ya hau rawa. Labbanta sukayi mata nauyi. Idanun ta suka shiga haska mata fuskokin ta tun tana kankanuwar ta. Cikin rawar baki da jiki tace,
"H a d i y y a h........."
Ummy ta daga kai da sauri ta sauke akan Hajiya Fadila. Rabon da a kiira ta da sunan tun tana kankanuwar ta ba zata taba mantawa ba. Domin tuni lokacin da rikon ta ya koma hannun su Innarajo yan kauyen basu iya fadar sunan ba sike kiranta da hadiza, shikenan sunan ya bita. Har girman ta ana kiran ta da Malama hadiza ...
MX WRITES✓
_𝕂𝕀 𝕂𝕌𝕃𝔸 ℕ𝕀!!_
_(𝕄𝔸𝕃𝕃𝔸𝕂𝕀ℕ ℤ𝕌ℂ𝕀𝕐𝔸)💕_
_ℕ𝔸ℕ𝔸 ℍ𝔸𝔽𝕊𝔸𝕋_
_𝕄𝕀𝕊𝕊 𝕏𝕆𝕏𝕆_
_ℙ𝔸𝕀𝔻 ℙ𝔸𝔾𝔼: 47_
_ZAFAFA BIYAR 2023__
_____
"Hadiyyah...!!!" Alhaji Hammadu da Alhaji Haydar suka fada a tare..
Ummy ta mike da sauri ..muhucin hannun ta ya fadi a kàsa .. Jikin ta ya dau rawa da bakin ta.
"Ya Haydar... Ya Hammadu?" Ta fada sunayen su ...
Hajiya Fadila ta fashe da kukan farin ciki.... Hawaye suka shiga kwarara a idanuwan tah..
Dogarawa take ahankali har ta karasa wajen ummy data sandare a tsaye. Gaba daya gani ta ke mafarki ki take.
Kana kallon ta kasan jinin su daya da ummyn da kuma Alhaji Hammadu da Alhaji Hydar da Alhaji Harith shima ya dakko kyawun su.
Hajiya Fadila ta saka hannun ta ta riko na ummy tana duban tah sosai. Har ta yar tawadar da ke gefen hancin ta tun tana kankanuwar ta tana nan bata fita ba..
"Hadiyya..."
"Na'am.." ummy ta fada hade da fashewa da kuka...
Gaba dayan su mamaki ne ya rufe su. Su Madeeha da su gwaggo kuma farin ciki suke akan burin ummy ya cika. Ta hadu da jinin ta.
Ko sau daya da bakin ta bata taba gaya musu batada dangantaka da su Innarajo ba. Gwaggo ce ta zaunar da su ta gaya musu komai. Da suka fadawa ummy game da abunda gwaggon ta gaya musu. Murmushi kawai tayi tace eh... Amma dai batada wanda suka zarta su innarajon a yanzu...
Kana kallon su kasan yan uwan juna ne kuma na jini. Saboda madaukakiyar kamar da suke da ita...
Alhaji Hammadu hannun sa na rawa yayi nuni da ummy yana kallon su Harith.
"Itace yar uwar mu wato kanwar mu da muke uwa daya uba daya kamar yadda Hajiya ta gaya mu ku. Yan uku ne mu Hajiya ta haife mu. Ni Hammadu , Hydar da ita Hadiyyah... Allhamdulillahi Yaa Allah!!" Yana karasa fada ya dubi gabas yayi sujjada yana mai sake yin hamdala ga Allah buwayi gagara misali da ya hadasu da tagwan haihuwar su bayan shudewar shekaru masu tarin yawa....
Ummy ta rungume Hajiya Fadila tsam a jikinta. Dukkanin baki dayan su kuka suke yi. Ciki harda Alhaji Harith. Don ba ranar da zatazo ta wuce ba ayi zancen Hadiyyah (Ummy)ba..
"Ashe rai kanga rai Umma Tah.? Ashe idanuwana zasu sake ganin ki Umma Tah... Nayi kewar ki da yan uwana Umma Tah. "
"Mu ma haka Hadiyyah... Mu ma haka.." Hajiya Fadila ta amsata tana sake rungume ta tsam a jikin ta.
Baki daya sauran yan uwan tausayin su ya sake shigar su ..Haka kawai a raba 'ya da uwar ta..
Bayan sun kammala koke koken su... Sabuwar hira ce ta shigo ta yaushe gamo? Sunata tuno baya... Ummy ta juyar da hannu ta na kiran su Madeeha da suka shige daki.
Fitowa sukayi Fareeha agaba, Madeeha na biye da ita a baya da Junaid. Suka tsugunna har kasa suka gayshe da su cikin girmamawa,
Ummy tayi murmushi tana mai nuni da yatsa ga su Fareeha,
"Ummah ta... Wannan shine Yayan su na faari.."
"Ma shaa Allah..."
"Haba? ma shaa Allah..."
"Ma shaa Allah..."
"Ya sunan su...?"
Suka shiga tambaya suna bin su da kallo cike da kauna,
"Sunana Junaid.."
"Ma shaa Allah..."
"Wadannan kuma yan biyu ne .. Fareeha ce wannan ga kuma Madeeha.."
"Ah ma shaa Allah... Alhamdulillahi.. Kai tubarkAllah... Ma shaa Allah... Sun debo kyawun ki ... Ma shaa Allah Hadiyyah ke ma ashe kinada yan biyu..?"
Haka dai kowanne ya shiga tofa albarkacin bakin sa akan yan biyun da kuma Junaid gwanin ban sha'awa.
Ummy ta sake nuni da Innarajo da ke kwance akan katifa tace,
"Wannan itace Innarajo... Wadda ta zamemun mahaifiya tun da karancin shekaruna ya zuwa aurena.... Wannan kuma sunan ta Gwaggo... Kanwa ce ga Innarajo .. Ga borkindo Yaya ne agare ni shi din 'dan Innarajo ne tare muka tashi.. wannan gambo ne da ne ga gwaggo... Wanda shima tun yana karami yake agurin Innarajo."
"Ma shaa Allahu... "
"Allah ya saka muku da alkhairi da rikon Hadiyyah da kuka yi.."
"Jazakum Allah bil jannah..."
"Allah sarki... Hadiyyah. Mai gidan na ki anan garin yake ?"
Ummy ta girgiza kai kafin tace,
"Acikin garin kano yake ..Marigayi sheikh sufyan zubair da ke gyada road. Allah ya masa rasuwa.. Gidah daya muke da kanin sa Ashiru .. Kafin rayuwa ta juya mana... Wasu mutane masu dattako suka bamu matsugunin zama agidan su da ke unguwar.... Ah.. unguwar..."
"Sultan road..." Madeeha ta karasa mata..
"Yauwa sultan road.. cin mu da shan mu da tufatarwa da makarantun yara.. Kai komai dai sun dauke mana .Dan siyasa ne ma na majalisar jaha ta mazabar gyada road..."
"Okay ko Alhaji Abdulrashid?"
"Shi..."
"Allah ya saka musu da alheri suma... Allah ya biya su "
"Aamin" suka amsa baki daya..
Asabe da ke gefe ta dubi Hadiyyah tace da ita,
"Hadiyyah kin gane ni?"
Ummy ta dan kalleta na yan wasu mintoci kafin tace,
"Asabe...?"
Asabe tayi murmushi tana duban Hajiya Fadila,
"Hadiyyah ta gane ni..."
"Ai dama tun suna kankana kin manta tana maqale mkli?"
"Tabbas anyi haka.. Kingsne wannan?" Ta nuna mata Yusha'u
Hadiyyah (ummy) ta girgiza kai tana murmushi,
"Bangane shi ba gaskiya."
"Ai dama ba lalle ki gane shi ba gaskia tunda ko a shekarun baya ya 'daraku sosai.."
Borkindo ne ya dawo daga bakin kasuwa daya tafi bayan shigar su Hajiya fadila. Hannun sa dauke da katuwar kwarya cike da fura da nono a dame harda kankara kananu aciki da kwakwa. A gaban su ya ajiye ta ya dakko kofunan su silver na baki ya sake ajiyewa a gefen furar yana fadin,
"Bismillan ku yan uwa ."