Sashe 52
Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Sai da safe .. " ta fada tana kyakkyabe fuska.
Hakan ya bashi dariya. Yayi murmushi kawai kafin yace da ita,
"Sai da safe my cutie pie...I love you soo much."
Juyawa tayi da sauri tabar wajen. Murmushi yayi kawai yabi bayanta da kallo yana girgiza kai
Ji yake tamkar an yaye masa dukkanin wata damuwar sa. Ranar ya kasance cikin farin ciki marar misaltuwa.
Ko dah Madeeha ta koma sashen su. Ta bawa ummy sakon yazed . Ummy ta saka Madeeha ta raba musu. suna ci suna hira.
Sai bayan sunje kwanciyar bacci Fareeha ta sanar da Madeeha dukkanin abubuwan da yazed ya fada mata.
Madeeha tayi farin ciki ba kadan ba ta kuma sake babbawa Fareeha shawarwari masu kyau . Ta kuma aminta da Fareeha ta bawa Yazed dama su fara soyayya. Don bashi da wani makusa ko wasu halaye na 'ki.
Haka suka raba dare suna hira. Kafin daga bisani suyi sallar nafila su ka kwanta bacci.
Madeeha ta riga Fareeha yin bacci. Don Fareeha ta jima tana mamakin Yazed da kalaman sa. Dakyar bacci barawo ya saceta...
XOXO WRITES✓
_𝕂𝕀 𝕂𝕌𝕃𝔸 ℕ𝕀!!_
_(𝕄𝔸𝕃𝕃𝔸𝕂𝕀ℕ ℤ𝕌ℂ𝕀𝕐𝔸)💕_
_ℕ𝔸ℕ𝔸 ℍ𝔸𝔽𝕊𝔸𝕋_
_𝕄𝕀𝕊𝕊 𝕏𝕆𝕏𝕆_
_ℙ𝔸𝕀𝔻 ℙ𝔸𝔾𝔼: 44_
_ZAFAFA BIYAR 2023_
___
Exams suka fara ranga ranga...Kowanne dalibi na makarantar Birmingham ya shiga taitayin sa bisaga jarabawar da suka fara wadda itace zasu kare karshen ajin zuwa shiga na gaban sa. Wato next level..
Dukkanin kwanakin da akayi ana karatun ya zuwa farun jarabawar su da karewar su. Madeeha bata taba bari dede da minti daya ta tsaya da Rayyan ba.
Duk hanyar da tasan zata hadu da shi sai ta dena bin ta. Duk layikan waya da yake siya yana kiran ta da tura mata sakwanni tuni ta tottoshe su ta goge.
Gashi ta kulle duk wata kofa da tasan Rayyan din zai bi ya hadu da ita. Hakika ba karamin azabtar da zuciyar Rayyan din take ba.
Tamkar wanda ya tashi daga ciwo haka yake rayuwa. Duk ya bi ya kare a tsaye. Fuskar sa tayi fayau. Idanuwan sa sun furfuto tubarkAllah.
Data zana jarabawar ta zata bar cikin makarantar ta koma gidah. Rayyan yabu har ta kan Fareeha don son ganin Madeeha. Nan ma bai samu dama ba. Fareehan tace a'ah.
Gefe daya itama Fareehan Yazed nata bibiyar ta data karbi soyayyar shi. Ta samu ummy da zancen. Ummy tayi shiru kawai can kuma ta bi su da cewar su mayar da hankulan su akan karatu... Su kuma cigaba da addua itama zata taya su da ita. Allah ya musu zabi na gari acikin dukkanin lamuran su. Musanman a bangaren mazaje na kwarai..
Haka dai kwanaki suka yi ta shudewa. Har Allah ya sa su Madeeha suka kammala jarabawar da suke yi. Akayi musu hutu na dogon zango. ...
Rayyan ya kasa hakuri. Sukunin sa ya kai maqura. Ya kasa jure rashin ta a tattare da shi. Komai ya hadu yayi masa zafi.
Ranar data kasance itace wadda dukkanin dalibai zasu kammala jarabawar su ta karshen zangon karatun ajujuwan da suke ciki.,
Rayyan da wurwuri ya kare rubuta jarabawar sa ya fita daga cikin dakin jarabawar ya zuwa kofar dakin da su Madeeha ke zana jarabawar ta su.
Kanta a kàsa takardar jarabawar da ta ke rubutawa ya hango ta zaune cikin jallabiya baka. Ta yane kanta da mayafin jallabiyar. Ba kadan ba ta masa kyau. Tamkar ya shige ciki ya nufi inda take...
Ya kasa hakuri. Ya nemi wajen wasu kujeru acan gefe daga bayan kofar dakin jarabawar ya zauna..
Shiru shiru yana dai ta jiran fitowar sa sai gata ta fito tana nannade takardar tambayar jarabawar / question paper .. Ta zura acikin jakarta tare da biron da ke hannun ta.
Ya na hangota sai ga shi ya mike ya nufi inda take. Alokacin har ta fita daga harabar wajen dakin jarabawar zuwa farfajiyar faculty din na su
Ya nufeta da sauri har yana tuntube. Sanye yake cikin manyan kaya farare tas da su. Samfarin riga da wando dinkin Bauchi. Bai saka hula akan sa ba. Kanannadadden kwantaccen gashin kansa na fulanin usul ya kwanta luf.
"Madeeha..... "Ya kira sunanta hadi da sassarfa ya cimmata.
Kin kula shi tayi. Ta sake yin sauri ta shiga tafiya. Bai fasa bin ta ba yana kiran sunan ta.
"Madeeha ."
"Dan Allah... Dan Allah! Ka kyale ni."
"Madeeha please .."
Katse shi tayi da sauri tana,
"Please... Dan Allah ka kyale ni...."
"Madeeha ba zan iya dena KULA ki ba wallahi... Kin MALLAKe duk wasu kafafe da ke cikin ZUCIYA ta... Madeeha dan Allah ki dena azabtar da ni akan laifin da ban aikata miki ba Madeeha... "
Yamutsa fuska tayi. Tayi gaba da sauri . Ya cigaba da bin ta yana magana bai fasa ba...
"Ke kadai ce nake gani kullum a cikin baccina, ke ce abar begena kuma ke ce wadda nake so, domin a gurin ki nake tsammanin samun farin cikin da nake fata. Ina son ki Madeeha. Ina kuma kaunar ki sosai ..Nesantar ki babban aiki ne da yake jigata zuciya ta, dama ace kin san halin matsi da takura da nake shiga da kuma shaukin son kasancewa a tare da ke da nake ji cikin zuciya ta a dukkan lokacin da na nesanta da ke da kin tausaya mun Madeeha..."
Bata ce masa uffan ba... Tana dai ta tafiya yana bin ta yana magana shi kadai kamar sabon tabi.
"Madeeha...I fell in love when our eyes first locked and still fall deeper every day...You carry my heart and my soul. There is nowhere else I'd rather
be than be with you always and forever, no one else I would rather spend time with. I miss you when we are apart. You are my world and everything in it..."
Tayi hanzarin saka hannu ta tsayar da white bus da ke tunkaro su. Kwandastar motar ya daga hannu yana,
"Wajen mutum daya ne..."
"Eh ni daya ce.."
Suna bude motar tayi zuruf ta shige ciki. Komawa yayi da sauri inda ya ajiye motar zai shiga ciki sai ga zuwan su T-Boy,
"Maza ina zuwa?"
"Zamuyi magana anjima in shaa Allah..." Ya basu amsa da haka ya shige cikin motar tasa da sauri ya tashe ta.
Dafifin dogon traffic jam yaci karo da shi tun daga wajen faculty din su madeehan zuwa gate din waje.
Ba wata hanya da mutane zasu wuce inde ba masu tafiya a kafa ba. Wata motar ruwa ce da ke bawa dukkanin shuke shuken makarantar ruwa ta jirkice ta fadi awajen gate. Don haka ba masaka tsinke ta masu shiga da futa daga cikin makarantar..
Inda Allah ya temaka motar su Madeeha na shigewa tsautayin ya gitta motar ta fadi. Lekawa Rayyan yayi ya hango dafifin mutane da motoci fal.
Ya koma ya zauna hannun sa daya akan sitiyari dayan kuma ya juyar dashi ta baya. Ransa duk a jagule ba bu dadi
Wasa wasa sai da ya bata wajen mintina talatin duk da haka motar baa samu nasarar dauke ta ba. Takaici yasa ya juya baya ya hango wata yar hanya ya ja motar tasa baya ya faka ta awajen ya fita daga cikin motar.
Kai tsaye ya futa daga cikin makarantar zuwa titi. Ya samu wani dan adaidaita sahu daya aje wata mata ya shiga ciki da sauri.
"Yallabai Ina kayi?" Dan adaidaita sahun ya tambaye shi.
"Sultan road..."
"Tahh.. Dari biyar saboda kaga kai kadai ne."
"To ba damuwa.*
Nan da nan me adaidaitan ya tashi adaidaita sahun na sa ya ja su suka hau titi. Rayyan ji yake tamkar yayi fuffuke ya tashi ya ganshi agaban madeeha
Ya riga ya yanke da zuciyar sa sai dai ko me zai faru ya faru..Dole ne yaje gidan su Madeeha. Inda taki amincewa da ganin sa to lalle zai nemi manyanta suyi magana..
"Aboki na ga rake.."Dan adaidaitan ya daga ledar raken da yake gaftara ya mikawa Rayyan
"Godia na ke. A koshe na ke wallahi."
"Kabar dadi.. Wato nake gaya maka rake duniya ne mutumi na.."
"Allah sarki..."
"Wallahi .. Allah ya zuba albarka a arake. Wallahi idan ka gutsuri rake... kai lamarin ba magana kawai. Fafet nake gaya maka.. Fafet (perfect).."
Rayyan ahun ya bashi dariya. Ya murmusa sosai. Dan adaidaita na tafiya yana gaftarar rake ya cigaba da cewa,
"Siyasar najeriya jagwal ce mutumi na.."
"Allah aboki na?"
"Yasin.. Yan kutukumar... Ni da zaa sayar da najeriya a rabawa kowa kudin sa ya kama gaban sa wallahi. "
Rayyan ya kasa rike dariyar sa. Ya dara sosai yana girgiza kai. Dan adaidaitan ya daga hannun sa daya sama yana kwarara bayani.
"Allah... Ko a bawa shugaban koriya ta arewa ya mulke mu ya koya mana hankali. Ko sojoji su karbi mulki. Allah wallahi."
"Gaskiya kam" Rayyan ya fada yana jin kansa kamar ya futa daga ciki. Ganin sai wani tafiya dan sahun yake ahankali...
"Talakawan najeriya bamuda hankali..akan ashana fa da burodi sai kaga mun sake zaben wadanda suka gasa mana aya a baki...."
"Hakane kam..."
"Ai shiyasa kawai sai addua da fatan Allah yazaba mana shuwagabanni na gari. Wadannan duk sun tsufa Dan balai ba zasu ba matasa ba. Kalli dai gwamnan mu Na'ilele Zanzabawa.. mutumin nan kudi kawai yake ciki."
"Ai kwua... Dan Allah ko zaka dan kara gudu aboki na."
"Yadda kace haka za'ai aboki na... " Dan adaidaita sahun ya fada. Hadi da kara gudun adaidaita sahun
Rayyan sai kallon agogon sa dake daure a wutsiyar hannun sa yake. Ga surutan me napep da yaki rufe bakin sa. Me napep din ya sake dakko wata hirar yana mai nunawa Rayyan wani gidah a bakin titi.
"Kai kudi suna inda suke mutumi na.me gidan nan daya rasu gidajen sa ashirin da uku a ikoyi da ke Lagos. Da k.....
Rayyan bai karasa ji ba ya saka hannu ya danno earpiece din da ke kunnen sa. Ya juyar da kansa kawai...
Ko da Madeeha ta koma gidah. Daman ita kadai su ummy ke jira sun gama shiryawa da kayan su dauke a akwati na har biyu.
Tuni daman Fareeha ta karkare tata jarabawar tun da sassafe.
"Dan Allah kuyi sauri... Kuje ku fara gano kawun na ku. Kafin sannan Hajiya ta dawo sai muyi mata sallama daga nan sai mu wuce tasha.
"Tohm ummy insha Allah.."