← Book details Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 66

Sashe 57

Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sukayi dariya sosai., Hajiya Fadila ta amince da zaman ummyn tare da ita agidan Alhaji Harith dan autan ta..

Alhaji Harith ya saka aka tashi gyaren eani babban sashe dake cikin gidan sa. Sama da kàsa ne.. Tuni aka fara saka masa kayan gidah masu kawatuwa na kamfanin Maab luxury home......

°°°°°°°°°

Ranar......

NANA HAFSATOU✓
_𝕂𝕀 𝕂𝕌𝕃𝔸 ℕ𝕀!!_
_(𝕄𝔸𝕃𝕃𝔸𝕂𝕀ℕ ℤ𝕌ℂ𝕀𝕐𝔸)💕_

_ℕ𝔸ℕ𝔸 ℍ𝔸𝔽𝕊𝔸𝕋_
_𝕄𝕀𝕊𝕊 𝕏𝕆𝕏𝕆_

_ℙ𝔸𝕀𝔻 ℙ𝔸𝔾𝔼: 48_

_ZAFAFA BIYAR 2023_

_______
Ranar laraba, itace ranar da Alhaji Harith da kansa ya shiga zungureriyar motar sa ya nufi kauyen rafin kanya daga cikin garin na kano..don dakko mahaifiyar sa Hajiya Fadila, da yayar sa Hadiyyah (ummy) da su Madeeha...

Ko da ya karasa .... A kofar wani gidah mai dakali ya faka motar. Ya sanya wasu yara suka dinga daukar kayan abinci daga booth dinsa zuwa cikin gidan su Innarajo .

Har sun kammala shiryawa suna daga zaune akan tabarma. Ummy na matsa kafafun mahaifiyar ta Hajiya Fadila.

Alhaji Harith ya saka akai masa iso cikin gidan kafin daga bisani yayi sallama ya shiga ..

Su ka hau yi masa sannu da zuwa mai tattare da sakin fuskar lale maraba..

Guri ya nema ya zauna a kusa da mahaifiyar ta su Hajiya Fadila. Ya gayshe ta cikin girmamawa ta amsa a sake. Ya juya ya gayshe da Hadiyyah ummy itama ta amsa fuskar ta kunshe da farin ciki.

Su Madeeha suka hau gaishe da shi cike da girmamawa ya amsa yana mai kiran sunayen su.

Innarajo tana bacci. su borkindo kuma suna bakin kasuwa. Gwaggo kuma tana bandaki.

Bayan ta fito ta tsaya suka gaysa da Alhaji Harith... Ta nufi wajen Innarajo tana dan bubbuga hannunta kadan,

"Ba sai kin tashe ta ba.." cewar Alhaji Harith.

"A'ah ai dama zan tashe ta ta sha magani... Ga kuma yamma ta gabato."

"Allah sarki .. "

Innarajon ta farka tana salati. Gwaggo da ummy suka mikar da ita daga kwancen da take suka jingina ta abango.

Alhaji Harith ya matsa kusa da su yana gayshe da innarajon. Ta amsa shi tana murmushi.

Sun dan jima ana yar hira jefi jefi. Kafin daga bisani ya mike yace yana jiran su a waje. Ya zaro kudi masu dan yawa ya ajiye a gefen Innarajo..

"Gashi kyaci goro..."

Ya sake debo wasu da basu kai na innarajon ba ya ajiye a gefen Gwaggo,

"Gashi ba yawa."

Suka shiga yi masa godia.

"Kai harda wahala haka? Ga kayan abinci fal Innarajo ya kawo mana.. Mungode Allah ya saka da alkhairi." Gwaggo ta fada tana mai yiwa Innarajo nuni da kayan abincin da Alhaji Harith ya sa yara suka shiga da shi..

"Sannu da kokari dan nan Allah yayi muku albarka..Allah ya saka da alkhairin sa ya jikan mahaifa.."

"Aamin..."

Ya fice da sauri yana mai godiya da adduoin da suke ta yi.

Fareeha da Madeeha suka dauki kayayyakin na su suka saka a motar alhaji Harith... Kayan kauye fal Innarajo ta basu wai sukai wa yan uwa da ke cikin birni.

Sannan suka koma sukayi wa su gwaggon sallama. Junaid da ummy suka riko Hajiya Fadila suka saka ta acikin mota.

Sannan suka koma sukayi sallama da Innarajo. Gwaggo bata bar daga musu hannu ba har sai da motar su tabar wajen..

Bakin kasuwa suka nufa inda su Borkindo su ke. Ummy tayi musu sallama. Alhaji Harith ya zaro kudi ya basu sukayi ta godiya . Junajd ne a gaba. Kujerun tsakiya ummy da Hajiya Fadila. Kujerun karshe kuma Fareeha ne da Madeeha..

✓✓✓✓

Sannu ahankali suka karasa cikin kwaryar birnin kano....Alhaji Harith ya dan daga murya yana cewa,

"Yaya Hadiyyah gidah zamu wuce ko.?"

Ummy dake daga baya tayi murmushi kafin tace,

"A'ah gidan su Yazed din zamu je... Sai mun sanar musu zamu tashin ai... Ko da nan da zuwa wani satin ne"

Alhaji Hydar ya girgiza kansa tamkar karamin yaro yace,

"Haba Yaya... Shikenan sai mu kyale ku ku cigaba da kwana a boys squatter din wasu? Kuna da gata kuma..."

Ummy tayi murmushin da gefen kumatun ta suka lotsa kafin tace,

"A daiyi hakuri Bappan su... In shaa Allah da mun karasa dan abubuwan da zamuyi sai mu kira waya. Ko Umma?"

Hajiya Fadila tayi murmushi kafin tace,

"Nima na dauka wucewa can gidan auta zamuyi...Sai da kikayi bayani naga dacewar gaya musu din... Zuciya mai halacci bata mance alkhairi komai girman sharri.."

"Yauwa.... Allah ya bamu sa'a..."

"Aamin...." Suka hada baki wajen amsa ummy.

Su dai su Madeeha ba sa cewa komai suna dai kase da kunnuwan su suna sauraron komai.

A haka alhaji Harith ya karasa unguwar sultan road. Ya saka yatsa yayi nuni da gidan Bappah Hydar,

"Ga dai gidan Yaya Hydar... Ina ne inda kuke din wannan ko na gaba?"

"Wannan ne..." Cewar Junaid..

Har kofar gidan Alhaji Harith yayi parking da motar sa.

"Mun zo ."

"Toh mungode Allah ya saka da alkhairi."

"Dan Allah Yaya ki dena godiyar nan haka .. Idan bamu muku ba a duniya wa zamuyi wa?... Muje ko Hajiya?"

Hajiya Fadila ta daga kai .. Ummy ta temaka mata ta sauka daga kan kujerar motar. Ahankali tana dogara yar sandar ta suka karasa shiga cikin gidan..

"Bari na tsaya anan ko? Idan an mun iso sai na shigo ciki " Alhaji Hydar ya fada yana dogara jikin sa da bangon gidan

Shiga ciki su Hajiya Fadila suka yi. Kan su tsaye suka shige sashen su Yazed din bayan sunyi sallama...

Safiya sai leke take yi tana zunde... Hadi da saka yatsa tayi nuni da su.

"Uwar yan sa'ido.." Madeeha ta fada tana yatsina fuska.

"Lamba daya ma kuwa... shegiyar mun kusa bar mata gidan sai ta jika ta shanye.."

Suka tuntsire da dariya suna tafawa. Suka karasa shiga sashen su hibban. Anci saa ma kuwa mahaifin su hibban na nan. Ummy ta gayshe su da su Madeeha. Yayinda su ma su alhaji àbdulrashed din suka hau gayshe da Hajiya Fadila..Yazed ma da ke gefe duk suka gaysa..

"Tare muke da kani na ...Yace idan ba damuwa ayi masa iso ya shigo.."

"Haba ba damuwa... Uhm yauwa Junaid please ka rako shi ya sbigo."

"Tohm."

Flta Junaid din yayi da sauri ya kira Alhaji Harith,

"Bappah sun ce ka shigo."

"Okay Junaid..."

Junajd din na gaba alhaji Harith na bin bayan sa suka karasa shiga cikin gidan...

Bakin sa dauke da sallama. Suka amsa masa baki dayan su. Alhaji Abdulrashid ya nuna masa waje ya zauna..

"Ah ah... Alhaji Harith oil?Da man talaka na ganin ku?" Cewar Alhaji Abdulrashid..

"Na'am ranka ya dade Ina gaisuwa.."

"Haba wane mutum .. mune da gaysuwa.."

Hannu ya bashi suka gaysa suna murmushi. Kafin daga bisani suka gaggaysa da sauran yan parlorn baki daya ..

Alhaji Harith yace,

"Ai da wucewa ma zamuyi .. Sai ita Yaya Hadiyyah din ke cewa a gaskiya sai tazo ta muku bayani. She's my elder sister ai.."

"Kasan Allah sai yanzu na ga kamar ku... Allah da iko ya ke... Ya wajen su Alhaji Hammad ? Shi Alhaji Haydar muna gaisawa da shi muna unguwa daya."

"Wallahi Alhamdulillah... Zabe ya karato. Muna fatan Allah ya baku nasara Amin."

"Allahumma Aamin.."

Alhaji Harith ya danyi gyaran murya kafin dai ya fada musu komai a dunkule a kuma takaice..

Dan tausayi Haj Ruwaida har hawaye ta zubar... Sosai labarin ya girgiza su. Kuma kwarai matuka sun yi farin ciki ga ummy da iyalan ta da suka hade da dangin su bayan shekaru .. Gefe daya kuma basu ji dadi da zasuyi nesa da su ba. Saboda sabon da sukayi da juna.. Ga kuma qima da darajar su ummyn ta sake dagawa awajen su .. Dubada ganin dangin da suka fito na manyan masu kudi da ake damawa dasu a kasar baki daya

Dakyar Alhaji Harith ya amince su ummy su karasa sauran kwanakin su su dawo gidan su da yayi musu wanda ke a cikin gidan sa ..

Har mota su ummyn suka yiwa su Hajiya Fadila rakiya... Alhaji Harith na ta jaddada wa ummy dan Allah kar su kara kwanaki nan da zuwa ranar zai aiko mota ta kwashe su da yaran baki daya .

Ummy tayi murmushi kawai tana kada masa kai... Ya zaro kudi da yawa ya mikawa Junaid yace ya bawa ummyn ya zaro wasu kuma yace na sa da su Madeeha ne..

Basubar wajen ba har sai da motar su Alhaji Hydar din ta ja tatafi.. Sannan suka shige gidah.ummy na gaba su kuma suna daga baya...

"Wai Yaya da wa naji kana waya ne dazu...?" Cewar Fareeha..

Kafin junaid ya amsa Madeeha tayi karaf din cewa,

"Wai dazu... Kullum zaki ce .. Haka zakigan shi yanata murmushi yana amsa wayar "

Rankwashin su yayi a tsakiyar kai. Suka saki dariya baki daya. Junaid yayi murmushi kafin yace ,

"Qibdiyya ce...."

Suka hada ido suka tuntsire da dariya.

"Wacece kuma qibdiyya...?"

"Mariyatul qibdu... Qibdiyya"

"Chab aina take ko yar nan unguwar ce?"

"Kun fa santa..."

Sukayi shiru suna tunani ..Fareeha ta girgiza kai. Madeeha ta daga idanu da sauri tana rufe baki,

"Mari me awara...?"

Junaid ya dage girar sa daya yana murmushi

"Ita dai... Ta fara karatu ma ai a school of hygiene.."

"Marin?"

"Banason wulakanci meye kuma mari? Mariya ko ki ce qibdiyya.."

"Wai dan Allah dagaske ko da wasa?"

"Kai yaran nan bakuda kai ma ga gaskiya ga rantsuwa? Na taba kamanceceniya da irin wannan zancen?"

Suka girgiza kai. Ya dage kafada,

"Toh... Ni na fita cafe zan curo assignment. Ungo ku raba ku ajiye mun nawa." Ya mikawa Fareeha kudin ya fita da sauri.

Sandarewa sukayi suna mamakin wai Yayan su mari yake so. Waya ga abu kamar wasa karamar magana ta zama babba ..

Suka tsaya suna tuno baya suna ta dariya. Kafin daga bisani su shige boys squatter inda suke..

Ransu fes. Zuciyar su tayi kal kal... Sun samu sauyin kaddara... Sun tashi daga duhu zuwa haske... Daga rashi zuwa samu... Alhamdulillah!! Dukkan yabo ya tabbata ga Allah mai kowa da komai...

×××

Da sauri take tafiya hannunta rike da bakar leda da ke dauke da ....

WATTPAD: MISSXOXO00
AREWABOOKS: MSSXOXO

_𝕂𝕀 𝕂𝕌𝕃𝔸 ℕ𝕀!!_
_(𝕄𝔸𝕃𝕃𝔸𝕂𝕀ℕ ℤ𝕌ℂ𝕀𝕐𝔸)💕_

_ℕ𝔸ℕ𝔸 ℍ𝔸𝔽𝕊𝔸𝕋_
_𝕄𝕀𝕊𝕊 𝕏𝕆𝕏𝕆_

_ℙ𝔸𝕀𝔻 ℙ𝔸𝔾𝔼: 49_

 _ZAFAFA BIYAR 2023_
Chapter 57 · 0% Book details