← Book details Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 66

Sashe 39

Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

_KAMSHIN TURAREN KAYA, TURAREN GIDA, TURAREN JIKI, TURRARN GASHI, TURAREN TSUGUNNO, TURAREN WANKA, TURAREN WANKI, TURAREN MOPPING, TURAREN BANDAKI, TURAREN LABULAYE DA ZANNUWAN GADO, AIR FRESHENER DA TURAREN AKWATUNA DA DRAWER DA MOTA... KAI HAR MA DA TURAREN DA KE CIRE BACIN RAI YA MUSANYA DA FARIN CIKI SABODA TSANANIN SANYAYAWAR SA DA YAYE DUHU DA DAMUWA_

_BA ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNADA NAU'IKAN TURARUKA NA KHUMRAH KALA KALA. SUNADA TURAREN RUWA NA FESAWA DANA MAIKO. SUNADA KAYAN GYARAN JIKI.._

_SUNADA KULACCA DA SAURAN BODY BUTTERS MASU YAYE WARI KODA KUWA AN YI KWANAKI BA WANKA BARE WANKI._

_SUNADA KABBASA TA TURARA KAYA DA KASAKEN TURARUKAN WUTA NA KARFE DANA KASA DAMA NA ZAMANI YAN WAJE._

*_YERWA INCENSE AND MORE_*

_YERWA INCENSE AND MORE_

_YERWA INCENSE AND MORE_

_MASARAUTAR KAMSHI KENAN. KAYAN SU NA AKAN FARASHIN SARI DA SAYA DAYA DAYA.. SUNA YIWA AMARE HADI DA UWAYEN GIDAH DAMA YAMMATA. SUNAYIN NA TARON SHAGULGULAN BIKI DUK AKAN FARASHI MAI RAHUSA_

_BA'ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNA DA TARIN KAYAYYAKI MASU KYAU DA RAHUSA HADI DA INGANCIN DA ALKALUMA SUNYI KADAN WAJEN BAYYANA MUKU._

_SUNA TURA KAYAYYAKIN SU FADIN NAJERIYA DA KETARE BAKI DAYA._

_ADIRESHIN SU. SUNA GARIN KANO DAURA DA TITIN DA ZAI SADAKA DA GARIN MAIDUGURI_

_SUNA KAN MANHAJOJIN SU DAKE KAFAFE DA DAMA KAMAR:_

_INSTAGRAM: @yerwaincense_and_more_

_FACEBOOK:yerwacollection_

_WHATSAPP: 08095215215/09044191709_

_A YANZU HAKA KAMFANIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE SUNA SALES DIN KAYAN SU NA 250ML NA TURAREN WUTA DA KUMA 240 DA 190ML NA KHUMRAHS_

_IDAN ANJE ACE DAGA ZAFAFA NE AKWAI RAGIN KUDI DA HADI NA MUSANMAN DA ZAA YIWA DUKKANIN KAYAN DA KUKA SAYA._

_KYAU!! INGANCI! RAHUSA!! KAMA JIKI DA GIDAH!! AIKI!! ADADE ANA MOREWA SAI KAYAYYAKIN TURARUKAN KAMFANIN:*YERWA INCENSE AND MORE*_

_____
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥

0022419171
Maryam sani
Access bank

*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

*Thanks for choosing us*🔥
_𝕂𝕀 𝕂𝕌𝕃𝔸 ℕ𝕀!!_
_(𝕄𝔸𝕃𝕃𝔸𝕂𝕀ℕ ℤ𝕌ℂ𝕀𝕐𝔸)💕_

_ℕ𝔸ℕ𝔸 ℍ𝔸𝔽𝕊𝔸𝕋_
_𝕄𝕀𝕊𝕊 𝕏𝕆𝕏𝕆_

_ℙ𝔸𝕀𝔻 ℙ𝔸𝔾𝔼: 33_

_ZAFAFA BIYAR 2023_

____
Rungume hotan tayi tsam a jikin tah... Ya yin da hawaye daya na bin daya suka shiga reto a kyakkyawar fuskar ta. Duk kuwa da ta manyan ta. Usulin kyawun ta yana nan..

Ta sa ka hannun ta daya ta shafe hawayen da ke yar tsere a fuskar ta. Ta saka hannu ta daga hotan tana kare musu kallo. Su su uku a jere acikin hotan.

Itace a tsakiyar su. Ya yin da Hammad ke gefen ta . Gefen hagun ta kuma Hydar ne. Sai ita Hadiyyan a tsakiyar su.

Ta saka yatsan ta daya tana shafa Hadiyyan. Ta runtse idanun ta gam tana sauke ajiyar zuciya. Cikin rawar murya tamkar tana magana da wani ta shiga cewa,

"Hadiyyah na kasa amincewa da bakya tare da mu. Zuciya ta tana ingiza gangar jiki na da kina raye Hadiyyah tamkar yadda Asabe suka ce kina rayen. Idanuwa na na mun gizo da faifon fuskar ki Hadiyyah....Allah ya bayyana mana ke idan har kina raye. Idan bakya raye Allah ya jikan ki da rahama."

Sai kuma tayi shiru, Ta saka hannu ta janyo yar wayarta karama. Ta lalubo number dan na ta na fari Alhaji Hammadu. Duk kuwa da ta manyan ta . Allah ya azurta tah da gani sosai. Kunnenta ne dai guda daya ya tabu sai da temakon hearing device ..

Kara wayar tayi a kunnenta bayan ta kira shi.

Hajia Fadila: " Salamu alaikum. "

Alhaji Hammadu: "Wa'alaykumus salamu Hajjajun mu. Barka da safiya! Ya jiki jikin na ki? Allah yakara miki lafiya da nisan kwana mai amfani Hajjajun mu."

Hajiya Fadila: " Da imanin Allah... "

Alhaji Hammadu: "Da imanin Allah... Hajjaju. Hajiya kin tashi?"

Haj. Fadila: "Na tashi Hammadu. An kwan kalau?"

Alh. Hammadu :" Alhamdulillah Hajjaju. Bari na shigo dama nayo ta bangaren ku. Yanzu haka ina cikin mota "

Haj. Fadila: "Toh Allah ya kawo ka lafiya "

Sallama sukayi . Ta katse kiran. Hadi da mikewa tsaye tare da dogara yar sandar ta dake kusa da ita.

Ta shiga bandaki bakinta dauke da addua. Dukkanin abunda take bukata akwai a bandakin. Ta yi wanka hadi da dauro alwala....

Ta sauya kayanta. Wanda ta cire kuma ta saka shi a kwandon kayan wankin ta.

Tana zaune a bakin gadon ta ta jiyo kwankwasa kofa hadi da sallama. Ta dan daga murya yadda za'a iya jiyo ta,

"Wa'alaykm salam.. Shigo."

Ma'aikata ne suka shiga su biyu. Ya yinda Hajia Hindu ke biye da su abaya. Hannun ta dauke da tissue da abun sakace hakora.

Yan aikin suka gaishe ta bayan sun a'ajiye kuloli da abun zuba abincin agaban ta. Hadi da wani babban tray dake dauke da tea flask da cokula.

"Hajia barka da safiya."

"Barkan mu dai.."

"Kin tashi kalau? Ya jiki jikin na ki? Allah ya kara miki lafiya."

"Aamin Aamin .. Tare da ku baki daya."

Hajia Hindu na zaune suna gaysawa sai ga shigar alhaji Harith. Lokacin Hajian na tambayar Hajia Hindu,

"Ya kwanan yaran gaba daya?"

"Duk suna nan kalau Hajiya. Zasu zo su gayshe ki. "

Alhaji Harith na shiga Hajia Fadilan ta fara murmushin ganin dan autan na ta.

Shima yayi murmushin ya karasa kusa da ita ya zauna tamkar zai koma cikin tah.

"Hajiya ta..."

"Na'am Harith."

"Hajia ina kwana? Ya jikin na ki? Fatan kin tashi lafiya. Ya akaji damu Hajiya? Allah ya kara miki lafiya da nisan kwana mai amfani."

"Amin Amin Harith . Da imanin Allah. Tare da ku baki daya."

"Allahumma Amin Hajian mu "

Suna gaysawar ne sai ga wata daga cikin ma'aikata gidan tayi sallama aka bata izini ta shiga.

Ta tsugunna har kasa cikin ladabi da biyayya tace,

"Bappah ne yazo yace a masa iso."

"Wai su Yaya musanman Yaya Hammadu ba zai iya shigowa kai tsaya cikin gidan nan ba sai an masa iso ko yaushe."

"Ai Hakan yanada kyau kuma. Aqida ce me kyau musanman a musulunci." Cewar Hajiya Fadila ta bawa dan nata alhaji Harith amsa.

Alhaji Harith ya mike da sauri ya fice daga cikin dakin yana cewa,

"Bari naje na masa iso to .. Yaya kenan."

Ba jimawa sai ga su sun shiga cikin dakin bakin su dauke da sallama.

Yana shiga cikin dakin. Alhaji Hammadu ya cire hular sa. Ya matsa daf da mahaifiyar ta sa kamar ko da yaushe yana cewa,

"Hajia a saka mana albarka."

Tayi murmushi kafin ta saka hannunta akan sa tana cewa,

"Allah yayi muku albarka. Allah ya cigaba da dafa mu ku a dukkanin lamuran ku. Sharrin mutum dana aljan. Sharrin karfe . Tsautsayi da asara Allah ya kare ku Amin."

"Aamin Hajiya.."

Alhaji Harith ma ya matsa ya zare hular sa matar sa sai dariya take itada Hajiya .

"Nima ashafamun tubarrakin. Auta shalele."

Suka saka dariya baki daya. Hajiyan ta saka hannunta akan sa ta shafa tana masa addua shima kamar yadda tayi musu jam'i da tana shafa kan alhaji Hammad Yayan sa.

"Yayana barka da safiya? Ya wajen su Yaya Bintu da yarana baki daya.?" Hajiya Hindu ta gayshe da Alhaji Hammadu tana mai kokarin mikewa ta basu waje.

"Suna nan kalau Alhamdulillahi. Allah ya saka da alkhairi. "

"Aamin Aamin. Ga plates man Yaya ku ci abinci. Ka saka mana albatka."

"Ah ai dole na zuba naci. Nagode kwarai. " Cewar alhaji Hammad hadi da daukar cup yana zuba kunun shinkafa

Sukayi dariya baki dayan su. Ta mike ta basu waje ta fita zuwa parlorn ta na sama.

Alhaji Hammadu ya sake yiwa Hajiya sabuwar gaisuwa bayan wadda sukayi ta waya. Alhaji Harith ma ya gayshe da Yayan na sa.

"Dan birni kira Aliko hydara. Nambar tasa ce ne idan na kira sa sai naji muryar aliyu dan gidan Asabe. "

"Allah sraki. To Hajiya yanzu kuwa."

Lambar Alhaji Hydar kanin sa ya kira Kuma Yaya ga Alhaji Harith.

Bayan sun gaysa da juna.. Nan yake sanar masa kan yazo gidan kanin su alhaji Harith. Hajiyan su tana neman sa.

Ba'a dau wani dogon lokaci ba kuwa alhaji Hydar ya shiga gidan. Hajia Hindu ta sakko daga sama suka gaysa. Kafin daga bisani alhaji Harith ya fita ya shiga da shi zuwa dakin Hajiya.

Gaishe gaishe suka fara yi a tsakanin su. Kafin daga bisani su shiga cin abincin karin kumallon Tare da mahaifiyar ta su Hajiya Fadila. Gwanin ban sha'awa.

Bayan sun kammala cin abincin sun nutsu sun shiga hira kamar ko da yaushe idan sun hadu. Hajiya Fadila nata binsu da kallo. Yaran nata suna da hadin kai da kaunar junan su.

Tunowa tayi da Hadiyyah na tare da su da tuni kilan tana tsakiyar su suna hira.

"Hajiya menene?"

"Hajia akwai abun da yake damun ki ne?"

"Hajiyan mu ko wani abun kikeso yanzu ayo miki ?"

Shiga tambayar ta sukayi. Kowane cikin su fuskar sa dauke da damuwar ganin hajiyan da ta sauya lokaci daya

Girgiza kai tayi. Ta kakaro murmushi. Dan sauran hawayen data makale ya shiga zurara a fuskar ta

Cikin rawar baki da jiki ta janyo hotan dazu tana mika musu. Yayinda hawaye suka shiga kwaranya a kyakkyawar fuskar ta,

"Hadiyyah... Wai shin ina Hadiyyah ta ke? Har yanzu babu wani labari ? "

Suka yi shiru kowane yana jinjina maganar tata . Da yadda tambayar tazo musu a bazata.

Alhaji Hammadu ya sauke gauruwar ajiyar zuciya kafin cikin kasa da kai yace,
Chapter 39 · 0% Book details