Sashe 47
Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Naam" ta amsa ummyn gaban ta na faduwa.
"Yauwa yaronnan wai da kuke gaysawa a makaranta. Ki fita harkar sa kinji ko? "
"Toh ummy "
"Yauwa kuci gaba da tsare mutuncin kan ku. Kada kuma ku dauki kanku wasu daban. Allah ne me azurta wa ya kuma talautaa. Kullum dai adduar itace mu kasance cikin masu wadatar zuciya. Ku kalli na kasan kasa da ku sai ku godewa Allah. Ahar kullum idan dan Adam na kallon na sama da shi to fa yayi sallama da farin cikin zuciya kenan. "
"In shaa Allah. Ummy."
"Yauwa. Mahaifiyar sa tazo nan dazu bata wani jima da tafiya ba. Tanata burga akan kudi tana fadan bakaken maganganu. Tace kema ta same ki a makarantar ko?"
"Eh ta same ni ummy."
"Yauwa to ki fita a harkar yaron da ma dukkanin abubuwan da suka dangance shi. "
"In shaa Allah ummy "
"Allah zai baku mazajen kwarai. Inda zakuje ku huta wani na kuma ya huta. "
"Aamin Ummy."
"Yauwa a yanzu dai sai ku mayar da hankulan ku kan karatu. Allah ya dafa ma ku . Ya bada sakamakon jarabawar me kyau."
"Aamin Ummy."
"Aamin.."
"Yauwa je ki to."
Juyawa Madeeha tayi ta shige cikin dakin su. Bandaki ta shige ta watsa ruwa . Wunin ranar haka tayi shi sakaka duk ba dadi. Cin mutuncin mahaifiyar Rayyan nata dawo mata a zuciya. Haka ma wanda saj-jeedah tayi mata.
Tana zaune akan yar katifar ta sai ga shigar Fareeha dakin. Tayi sallama ita kuma ta amsa mata.
Ta zauna daga gefen tata katifar tana bin ta da kallo.
"Kin ki gayamun yadda kukayi da ita datazo "
'duk abunda ummy tafada..Hakan ne ya faru."
"To ai ummy bata futo ta fadi komai ba ca dai tayi na fita a harkar Rayyan din da sauran su. Ke kuma gundarin abun na keso ki gayamun. Yadda komai ya wakana."
Fareeha ta sauke nannauyar ajiyar zuciya kafin ta ce,
"Fitowa ta kenan daga sashen su Hibba . Ummy datayi funkaso ta aike ni na kai musu. To na fito kenan jna kokarin zare sartsen daya shigemun yatsaa sai ga shigowar matar. Tana tafe tana waige waige. Sai na gaishe ta. Don na dauka ma bakuwar maman su Hibba ce tunda naga yar gayu ce. Sai ta amsa gaisuwa ta a gadarance wai lafiya.? Can kuma tace nanne gidan su Madeeha ? Sai gabana ya fadi dai. Sai nace mata Madeeha kuma? Tacemun eh. Wajen maman su nake son zuwa. Sai nace to biyoni . Ina gaba tana biye dani a baya. Muka karaso nan din . Sai naji tana cewa to fa a boys squatter ma suke. Lalle Rayyan yana neman bacin rai na. Nide bance mata komai ba . Muka karaso nayi sallama na shjgo da ita,
"Ummy na daki ma lokacin na shiga na kirawo ta. Tanata kalle kallen parlorn tana yamutsa fuska . Ummy tafuto ta gayshe ta ta amsa a wulakance. Kawai sai jiyo ta nayi tana cewa, Malama kike ko iya zance ne. Ki jawa yar wajen ki kunne. Madeeha take ko wa? Ta fita a harkar da na Rayyan. Ai ruwa ba sa'an kwando bane. Banda tsabar reni irin na talaka. Taya yar ki zatayi soyayya da 'da na rayyan. Ku ba masu mulki ba ko sarauta. Kaskantattu da ku da ke cin arzikin karkashin wasu. Yar ki na cikin inuwar wasu tana daga kai a makaranta. Wallahi summa tallahi tafita a harkar Rayyan. Zan iya sadaukar da komai don raba shi da ita. Idan maular kudi ce ya kawo ta har ta likewa 'dana ku fadi adadin kudaden da kukeso. Daga dubu dari biyar zuwa million biyu. Idan ba haka ba kuma hukuma ce zata rabamu da ku. Na tsani talaka ya shiga rayuwata wallahi. Ba abunda kuka sani sai wahala da fankama. Wannan shine gargadi na na farko kuma na karshe akan alakar ta da rayyan.... Zan salwantar da rayuwar ta idan har ta cigaba da hulda da shi. Sai da ta gama fadan komai tsaf sannan ummy tace da ita,
"Allah sarki... Iya sani na Madeeha ba ta hulda da yaron wajen ki. Sai dai idan shine ke bibiyarta. Maganar kudi ki dena ma taso ta Allah ya wadaata mu da wadatar zuciya. Kullum cikin hamdala muke da godiya agare shi domin shidin mubuwayi ne gagara misali. Dare daya Allah kan azurta bawa ya kuma talauta shi. Sa aran ki da gamin ki daga rana irin ta yau Madeeha ta dena hulda da shi yaron wajen na ki. Idan ta tafi Fareeha ki rufo kofar saboda sauro. Ummy na gama fadar haka ta mike ta shige daki.. Matar taja kafafun ta tabar gidan. Ina tattare wajen ne fa shine kika shigo ba dadewa da tafiyar ta.."
Madeeha ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi tana jinjina kai. Hadu da cewa,
"Allah ya kyauta. "
"Aamin Aamin. Ya kukai da shi Rayyan din?"
Madeeha ta tattare komai ta fada mata ta karkare da,
"Na goge number dinsa ma na saka a block list."
"Allah yasa haka shi yafu alkhairi ."
"Aamin Yaa rabbi "
Haka dai suka yita mayar da maganganu har dare yaja sosai sannan suka kwanta kowane da abunda yake sakawa acikin zuciyar sa. Musanman Madeeha data kasa bacci tanata juye juye abubuwan nata dawo mata .musanman abunda akace mahaifiyar Rayyan tayi. Hawaye suka shige reto a fuskar ta. Cin mutuncin har gidah wajen mahaifiyar ta da batasan komai akai ba.
MX WRITES✓✓✓
_𝕂𝕀 𝕂𝕌𝕃𝔸 ℕ𝕀!!_
_(𝕄𝔸𝕃𝕃𝔸𝕂𝕀ℕ ℤ𝕌ℂ𝕀𝕐𝔸)💕_
_ℕ𝔸ℕ𝔸 ℍ𝔸𝔽𝕊𝔸𝕋_
_𝕄𝕀𝕊𝕊 𝕏𝕆𝕏𝕆_
_ℙ𝔸𝕀𝔻 ℙ𝔸𝔾𝔼: FORTY (40)_
_ZAFAFA BIYAR 2023_
✓°✓°✓°✓°✓°✓°✓°
Cikin kwanaki kalilan zukata da yawa sun shiga halin qaqanika ni. Musanman ZUCIYAr Rayyan da baki daya rayuwa yake yi gaba gadi.
Kwanaki uku kenan rabon sa da ya sanya Madeeha a idanun sa. Duk wata hanya data san zata hadu da shi ko da kuwa hangenta ne daga nesa. Madeeha ta hani kanta da hakan.
Rayyan ya sha ruwa leda biyu da rabi a asibiti sakamakon rashin karfin jiki da zazzafan zazzabi da yake damun sa. Dukkanin lalure-Laluren nasa ba akan komai yake ba fache rashin sanya idanun sa akan Madeeha.
Domin wata iriyar kauna yake mata wadda alkalami yayi kadan wajen rubutawa. Hakama labba sunyi kadan wajen furtawa. Gangar jiki tayi kadan wajen dauka. Hakama zuciya ta disashe da kaunar ta mai madaukakin fassarawa.
Tana zaune a kujerar dake cikin twin theatre. Tana mamakin abinda ya hana su Nour karasawo ciki bayan sun ce mata an sauya dakin lakcar zuwa wanda take a zaune acikin sa.
Tayi mamakin ganin ba kowa acikin ajin tun dazu sai ita daya. Ta waiwaya ta sake ganin tabbas ita kadai ce. Ba wanda ya sake shigowa bayan ita. Gashi duk ta kira wayar su Nour din a kashe.
"Rashin mutunci...." Ta fada ahankali tana jijjiga kai.
Sai ga shigar sa cikin dakin karatun. Yana shiga ya saka makulli ya kulle kofar.
Tana dago kai domin ganin waye? kawai ta sauke idanun ta akan sa. Mikewa tayi da sauri jikin ta har yana rawa ta fara hada littafan ta ta zuba acikin jaka. Sai yanzu ta gano dalilin da yasa ita kadaice a hall din. Su nawal shiryawa sukayi da Rayyan suka mata karyar an fasa lectures a ajin baya kenan don kawai yayi magana d ita. Taja tsaki hadi da sake daure fuskar ta tamau.
Kanta tsaye ta wuce wajen kofa ta saka hannu zata bude ta jita gagam a rufe. Tasan za'a rina. Jikinta ya bata dazunbdaya tsaya mukulli ya saka kenan. Takaici ya sake tukwikwiye ta. Ta koma can gefen kurya ta rakabe.
Ya rame yayi fayau da shi. Asalin kyawun sa ya sake tsatsowa. Idanuwan sa sun sake fitowa luhu luhu tubarkAllah.
Sanye yake cikin manyan kaya. Riga da wando . Bai saka hula akan sa ba. Sumar kan sa ta kwanta luf ta fulanin usul.
Ya kasa ce mata komai. Ya tsaya a tsaye kawai yana bin ta da kallo. Tamkar wanda ya shekara bai hadu da ita ba.
Tana sanye cikin doguwar riga ta blue black. Ta zura jilbab shima blue black. Tayi kyau kwarai matuka. Kamar ya cinye ta danya haka yake ji.
"Madeeha....." Ya fada ahankali yana saukar da idanun sa akan tah.
Bata amsa shi ba. Kanta akan window ta murtuke rai tana sake cin magani.
"Madeeha.."
"Budemun na fita." Ta fada a tsawance.
"Madeeha. Please kiyi hakuri ki saurare ni."
Hannuwanta ta saka a kunnenta tana rufe kofofin kunnuwan tah...irin bataji dinnan .
Ya danyi murmushi tattausa hadi da sake matsawa dan kusa da ita. Ta matse kanta a bango tana banka masa harara.
Madeeha please... Hear me out."
Nanma tayi shiru batace masa komai ba. Ta sake shigewa cikin kuryar lungu.
"Madeeha dan Allah kiyi hakuri. Ki dena ganin laifi na wallahi wallahi bani da masaniya akan abunda suka aikata sai bayan sunyi."
"Ka budemun na fita."
"Zan bude idan mun fahimci juna."
"Ni Ina bin maganar iyayen na. Ka budemun na fita."
"Nima.. Ina bi... Please ki saurare ni."
Banza ta sakeyi da shi batace komai ba. Rayyan ya sake tarairayar muryar sa cikin kulawa da ban hakuri ya cigaba da cewa,
"Wannan abun ba sabon al'amari bane akai na..Madeeha wannan labari da zan baki dagaske ya faru ba shiryawa nayi ba....Kamar dai yadda kika sani da fari sunana, Rayyan Hammad. Na taso a hannun kakata Hajiya Fadila wato mahaifiyar babana. Ita ta yaye ni. Da Tare muke da ita da iyayen na wa agidah daya . Lokacin kafin kakanmu ya rasu wato mijin ita kakar tawa. Mai suna owais. Har yau sunan layin gidan da sunan shi marigayi kakan nawa ake kiran sa. Late Owais avenue . (Lt. Owais avenue), Shine mahaifin Bappah Harith...