← Book details Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 66

Sashe 60

Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ya zo a cikin Qur’ani mai girma in da Allah Subhanahu wa Ta’ala yake cewa:
[كَانَ النَّاسُ أُمَّةً وَاحِدَةً فَبَعَثَ اللَّهُ النَّبِيِّينَ مُبَشِّرِينَ وَمُنْذِرِينَ وَأَنْزَلَ مَعَهُمُ الْكِتَابَ بِالْحَقِّ لِيَحْكُمَ بَيْنَ النَّاسِ فِيمَا اخْتَلَفُوا فِيهِ......] ( سورة البقرة الآية 213 ).
Tarjamar Aya: Mutane sun kasance al’umma guda daya, sai Allah ya aiko Annabawa masu ba da bushara da gargadi, kuma ya saukar da littafi da gaskia a tare da su domin ya yi hukunci a tsakanin mutane cikin abin da suka sassaba wa juna a cikinsa… (suratul Bakara aya ta 213).
Ya zo a cikin tafsirin Allama Tabataba’i (Al-Mizan fi Tafsiril Qur’an) bayanin cewa: Wannan ayar tana bayani ne a kan dalilin shar’anta addini tun a asali, da kuma yadda aka kallafa wa mutum bin shari’ar addinin, kuma abin da ya kawo sabani a tsakaninsu yana bukatar bayani kamar haka: Cewa lallai shi mutum – wanda yake wani nau’i ne na hallita da aka dora shi a kan fitira ta zaman tare da taimakon juna – ya kasance a farko-farkon haduwarsa al’umma ce da ke dunkule waje guda, sai daga baya a bisa tsari na fitira dinsa da kokarinsa na ganin ya handame abubuwa ga kansa shi kadai ya sassaba da juna, to daga nan ne sai bukatar samar da dokoki wadanda za su kawar da wannan sabanin da rigingimun da ya shiga tsakaninsu ya taso, kuma wadannan dokokin sai suka dauki wani nau’i na addini, suna masu yin bushara da kyakkyawan sakamako da gargadi ga yin ukuba, haka nan ma saboda a samu dacewa sai aka shar’anta yin ibada, aka aiko da Annabawa da Manzanni, amma sai sannu a hankali suka shiga sassabawa game da ilimomin ko sanin addini (ma’arifuddin), al’amuran mafara da na makoma (mabda’u da ma’ad). A dalilin haka sai aka samu sabani a cikin haduwar kai da ake da ita ta addini,..."

Haka dai daya bayan daya suka yo ta yiwa juna fadakarwa akan zumunci da muhimmancin saada zumunta..

Aka tafu hutun awanni biyu da za'ai sallah a Kuma ci abinci. Komai an tanada a tsaftace a kuma killace.

Buffet/self service.... Kowa shi ke zuwa ya diba abunda yake so yaci da kan sa. Rayyan ya mike ya koma wajen Hajiya Fadila da ke bantarar goro.

"Hajjaju na..."

"Na'am dan yaye na.."

"Ai yanzu bakya ji da ni Hajiya."

Hajiya Fadila ta kalle shi tana murmushi..

"Ai ba wanda zai kamo fadar ka dan yaye."

Rayyan ya girgiza kai yana mrumushi.

"Yakumbo Hadiyyah itace ta gaban goshin ki yanzu."

Ummy da ke gefe tana jinsa tayi murmushi kawai bata ce komai ba.

"Dan yaye ga fa yan uwan ka kunyi magana?" Hajiya Fadila ta nuna masa Fareeha da Madeeha.

"Na san su farin sa ni Hajiya."

"To pha... Anya aina?"

Rayyan ya yi murmushin dayake na gefen Baki . Ya daga yatsa zai saukar akan su kenan Madeeha ta mike zata bar wajen. Ya sake sakin wani murmushin mai sauti kadan...

"Madeeha ban ruwa please...Ba na sanyi ba."

Ji take inama kasa ta tsage ta fada.ita baki daya ta rasa ta yadda yake ganeta itada Fareeha..

Ta wuce wajen ruwan da ke cikin katon wani bucket an cika sa da kankara..

"Gashi...." Ta mika masa..

"Madeeha ba munsan juna a makaranta ba?" Ya sake fada yana kashe mata ido.

"Uhm..." Ta nemi waje ta zauna tana jan mayafin ta kunya duk ta cika ta.

"To dai ko kunsan juna a makaranta wannan daban. Daga yau ku din yan uwa ne na jini. Iyayen ku yan gidah daya ne. Ku dau kanku daya. Banda wariya ... Kuyi zumunci saboda Allah ku sadashi yadda ya dace. Allah ya muku albarka."

"Amin Hajjaju..."

Ko da suka karasa cin abincin. Aka kira sallah. Mazan suka fita masallaci. Matan kuma suka yi tasu a cikin parlorn...

Bayan sun idar da sallar... Suka cigaba da saada zumuncin su na ranar ta hanyar daukar hotuna. Ta hada group chat da ke kan manhajar WhatsApp

Alhaji Harith ya saka rayhan dan gidan Bappah Hydar ya sayo manyan wayoyi guda hudu. Yakumbo Hadiyyah daya. Junaid daya. Sai fareeha da Madeeha kowannen su daya daya. ... Sai bayan isha'i tukun sannan taro ya waste . Kowanne ya nufi gidajen sa. Ya yinda su ummy kuma kowanne ya shiga dakin da yake mallakin sa.

Sai sha'awar gidan sukeyi... Ya matukar tafiya da su. Komai da aka zuba agidan me tsada ne da kawatuwa hadi da inganci gangariyyah. Su ummy sunyi santin komai. Don farin ciki ummy fashewa tayi tana kuka sosai . Hajiya Fadila nata baki. Haka suka kwanta cike da annushuwa marar misaltuwa. Lalle Allah me azurtawa ne a dare daya...Sun tashi daga halin rashi sun koma na samu. Ko'ina na'urar air conditioner na ce ke busawa. Ranar bacci harda saleba.. Lamarin sai godiyar Allah kawai...

_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_--_-

Haka rayuwa ta cigaba da garawa. Driver ne takanas saboda su aka dakko shi kan kai su makaranta ya dakko su. Wataran kuma Rayyan ne ke tafiya da su ko ya dakko su.

Junaid shima Bappah Hydar ya mallaka masa mota ya kuma sanya shi a makarantar koyan mota cikin sati na uku ya iya tsaf. Bayan Junaid ya karasa koya.. asabar da lahadi kuma aka saka su Madeeha su ma suka fara koya sannu ahankali suka iya Suma. Amman dai basa zuwa makarantar da motar sai dai unguwa ta kusa.

Haka dai abubuwa suka cigaba da tafiya. Rayyan na kokarin bayyanawa Madeeha soyayya ko agaban waye amman Madeeha taki amincewa. Sai sake nisantar da kanta take daga gare shi..

Lamarin da ya hasala Rayyan kenan ya samu Hajiya Fadila kakar su ya gaya mata shi fa yana kaunar madeeha. Ya samu Bappanin su ya gaya musu duka yana son madeehan itace yarinyar da mahaifiyar sa ta samu ta ci mata mutinci ta je wajen ummy ma ta ce Madeeha ta fita daga harkar danta Rayyan . Ya karkare da ummyn ce tun a wancen lokacin ta hana Madeeha cigaba da kula shi.

Alhaji Hammad ya mike a hasale yana cewa sai ya cikata wa Hajia Bintu cikon sakin ta guda daya tabar masa gidah hakiya Fadila mahaifiyar sa ta hana shi. Ta bashi hakuri hadi da sake tausasar sa. Daman ita ta hana ya sake ta alokacin daya hau doron zuciyar ba zai sake zama da ita ba akan magungunan daya gani ya kuma ji sunyi maganar da Suwaiba. Har gidan Suwaiba ya aika hukuma ta mata kashedin ta fita ahakar zuriyar sa ko ta samu kanta agidan kurkuku. Ya yinda ita kuma Hajiya Bintun ya fita a harkar ta baki daya bayan ya mata saki biyu.

A kuma ranakun ne su Rayyan suka kammala digirin su na farko a jami'ar Birmingham university Nigeria..

Dau dai lokacin da akayi tambayar Yazed da Fareeha. Aka sanya aure nan da wata biyu masu zuwa. Rayyan ya matsu shima ayi maganr sa da Madeeha. Ko ta kanta baya bi don yasan ba kaunar aure take masa ba. Shi kuma duk duniya baki daya ita yake burin kasancewa da ita.

Ya sake neman bappanin sa da maganr ranar da aka kawo lefen Fareeha... An taru an cika iya su yan uwa gwanin ban sha'awa. Bappah Harith na jan kunnen su akan martabar aure da darajar sa.

"Bappah auren zumunci fa?" Ya jeho tambayar sama ta ka.

"Auren zumunci kamar yadda jama"a suke cewa idan yayi kyau to ba shakka yafi komi, idan kuma ya baci to lallai matsalar kan shafi wasu da basu ji ba basu gani ba a duka bangarorin biyu. Muna fatan duka Allah ya baku abokanan zama na gari. "

Bakj daya parlron ya gauraye da '

"Aamin..."

Duk kawo kudi da kayan da akayi kanzil kawu Ashiru yaki zuwa. Sunce aje can a karba yaki.. sukace to yazo a karba anan nanma yaki sai ya tura aqeel wai ya wakilce sa. Gashi ummy duk ta damu ta kance sa su da uba ake ado...Ba a canzawa tuwo suna. Duk abunda zasu zama a rayuwa kada su manta da kawun na su da iyalin sa.

Hajiya Fadila da kanta ta samu Hadiyyah ummy da maganar Madeeha da Rayyan. Da farko ummyn ta nuna bata raayi saboda mahaifyar sa bata son madeehan. Don har dubiyar ta taje ta matukar bata tausayi ganin ta zama nakashaaahiya . Dakyar sai ta hakura ta kuma kiea Madeeha tace mata ta amince su ci gaba da hulda da Rayyan. Duk kuwa da Rayyan din baya gaban Madeeha.

Haka aka yi tambaya aka kawo kudin ta abunka da tuwo na mai na ce duk sune suka hallara. Aka shirgo mata kayan lefe fal kamar na yayan shugaban kasa. Babu ce kawai babu a lefen nan. Daga nan suka je sukayi aune aune da gwaje gwajen jini da sauran gwajin da ake so ayi idan zaayi aure. San samu ma ayi kafin maganar aure ta shigo ciki...

Suna tafe a mota... Radio nayi ahankali da shuuu din tafjya. Garin damuna yayi tsit sai ni'imar Allah a ko'ina... Ciyawa tayi koriya. Ko'ina shar shar da shi..

Ya daga idanun sa ya sauke akanta. Kanta a window tana kallan waje. Ya danyi murmushi hadi da gyaran murya kafin yace

"Sonki ne kadai akan tsarin dukkan tunanina komai nisan dare da tsawon wuni Iya wuya tunaninki ne akan kwakwalwata..kallon tsakiyar Idanuwanki suna saukar da sabuwar ni'ima acikin jikina ta hanyar hakane nake Kara kaimi wajen ganin nasamu ganinki akowace rana dauki ki amsa.. Sunankine nake ambato tsananin sonkine yake tsuma zuciyata shiyasa bana gajiya wajen waki da dukkan wata damuwarki.... Madeeha..." Yana sunanta daga karshe ..

"Na'am .." ta amsa shi tana matsa yatsun hannun Tah

"I have no more zest to continue in this one-sided love relationship. I am so interested in being with you and being the love of your life. I am saying it now before it is too late; I love you and want to be with you...."

Sake kaudar da kanta tayi kawai. Daman yasan ba zatayi magana ba. Don haka ya juyar da kansa shima ya kara gudu suka dauki hanyar gidah

Ranar jumu'ah bayan masallaci dubban mutane suka sheda daurin auren,

"Yazed Abdulrashid da amaryar sa Fareeha Sufyan zubair... Sai Rayyan Hammadu da amaryar sa Madeeha Sufyan zubair....
Chapter 60 · 0% Book details