← Book details Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 66

Sashe 62

Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_

A shagon Nawal's grills and more (08039122194)ya tsaya ya sayi kaji da kilishin su mai dadin dandano... Ya hado da fura da yoghurts harda pizza ma duk ya saya da drinks. Da kayan tea da biredi me yanka yanka😂🤌

Kai tsaye ya zuba su a bayan motar sa ya nufi gidan sa. Wani nishadi na dada dawainiya da shi sai murmushi yake..

Wai yau shine a matsayin angon Madeeha Sufyan zubair.. Yarinyar data sace ZUCIYAr sa ta MALLAKe ta tun ranar daya dora idanun sa akan ta yake ta burin sake ganin ta da son KULA ta.... Daga karshe Allah ya cika masa burin sa ya sanya Madeeha ta zamo mata agare shi..

"Alhamdulillah Yaa Rabbi. Forever grateful!!" Ya fada ahankali yana murmushin gefen bakin sa haka ya karasa gate din gidan sa.

Yadanna horn... Mai gadi ya taso a guje ya bude masa gate din. Rayyan ya shiga da motar sa ciki bayan ya tsaya sun gaysa....

..
_INA JAMA'AR TA MU? KU MARMATSO KUSA . GA TAGOMASHIN ARZIKI. SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI. MUN GWADA DOLE MU BADA SHEDA_

_INA AMARE, UWAYEN GIDA, YAMMATA? IYAYE MAZA DA KE SON FARANTA RAYUKAN MATAN SU DA YAYAN SU DA MA KANNEN SU?_

_ALBISHIRIN KU. GA GORO. DOMIN WANNAN DADDADAN LABARI DOLE MU BAKU ALBISHIR DA ALHERIN GORO. GORON MA FARI KAL KAL_

_WAI AKACE KAMSHI RAHAMA NE... KAMSHIN MA MUSANMAN ME SANYAYA ZUCIYA DA RATSA MAGUDANAR JINI DA TSOKA._

_INA MASU NEMAN KAMSHIN TURAREN SAUDI ARABIA? T'CHAD DA MAIDUGURI? IRE IREN KAMSHIN DA BAYA BIN ISKA YANA KAMA WAJE YA RIKE GIDAH..._

_KAMSHIN TURAREN KAYA, TURAREN GIDA, TURAREN JIKI, TURRARN GASHI, TURAREN TSUGUNNO, TURAREN WANKA, TURAREN WANKI, TURAREN MOPPING, TURAREN BANDAKI, TURAREN LABULAYE DA ZANNUWAN GADO, AIR FRESHENER DA TURAREN AKWATUNA DA DRAWER DA MOTA... KAI HAR MA DA TURAREN DA KE CIRE BACIN RAI YA MUSANYA DA FARIN CIKI SABODA TSANANIN SANYAYAWAR SA DA YAYE DUHU DA DAMUWA_

_BA ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNADA NAU'IKAN TURARUKA NA KHUMRAH KALA KALA. SUNADA TURAREN RUWA NA FESAWA DANA MAIKO. SUNADA KAYAN GYARAN JIKI.._

_SUNADA KULACCA DA SAURAN BODY BUTTERS MASU YAYE WARI KODA KUWA AN YI KWANAKI BA WANKA BARE WANKI._

_SUNADA KABBASA TA TURARA KAYA DA KASAKEN TURARUKAN WUTA NA KARFE DANA KASA DAMA NA ZAMANI YAN WAJE._

*_YERWA INCENSE AND MORE_*

_YERWA INCENSE AND MORE_

_YERWA INCENSE AND MORE_

_MASARAUTAR KAMSHI KENAN. KAYAN SU NA AKAN FARASHIN SARI DA SAYA DAYA DAYA.. SUNA YIWA AMARE HADI DA UWAYEN GIDAH DAMA YAMMATA. SUNAYIN NA TARON SHAGULGULAN BIKI DUK AKAN FARASHI MAI RAHUSA_

_BA'ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNA DA TARIN KAYAYYAKI MASU KYAU DA RAHUSA HADI DA INGANCIN DA ALKALUMA SUNYI KADAN WAJEN BAYYANA MUKU._

_SUNA TURA KAYAYYAKIN SU FADIN NAJERIYA DA KETARE BAKI DAYA._

_ADIRESHIN SU. SUNA GARIN KANO DAURA DA TITIN DA ZAI SADAKA DA GARIN MAIDUGURI_

_SUNA KAN MANHAJOJIN SU DAKE KAFAFE DA DAMA KAMAR:_

_INSTAGRAM: @yerwaincense_and_more_

_FACEBOOK:yerwacollection_

_WHATSAPP: 08095215215/09044191709_

_A YANZU HAKA KAMFANIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE SUNA SALES DIN KAYAN SU NA 250ML NA TURAREN WUTA DA KUMA 240 DA 190ML NA KHUMRAHS_

_IDAN ANJE ACE DAGA ZAFAFA NE AKWAI RAGIN KUDI DA HADI NA MUSANMAN DA ZAA YIWA DUKKANIN KAYAN DA KUKA SAYA._

_KYAU!! INGANCI! RAHUSA!! KAMA JIKI DA GIDAH!! AIKI!! ADADE ANA MOREWA SAI KAYAYYAKIN TURARUKAN KAMFANIN:*YERWA INCENSE AND MORE*_

_____
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥

0022419171
Maryam sani
Access bank

*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

*Thanks for choosing us*🔥

_𝕂𝕀 𝕂𝕌𝕃𝔸 ℕ𝕀!!_
_(𝕄𝔸𝕃𝕃𝔸𝕂𝕀ℕ ℤ𝕌ℂ𝕀𝕐𝔸)💕_

_ℕ𝔸ℕ𝔸 ℍ𝔸𝔽𝕊𝔸𝕋_
_𝕄𝕀𝕊𝕊 𝕏𝕆𝕏𝕆_

_ℙ𝔸𝕀𝔻 ℙ𝔸𝔾𝔼: 52_

_ZAFAFA BIYAR 2023_

_____
    Bayan ya faka motar sa awajen adana motocin gidan. Ya dakko duk siyayyar da yayi ya rike a hannun sa ya rufe motar.

Tsayawa yayi yana bin harabar wajen da kallo. Anyi shuke shuke masu kawatarwa a gefe da gefe..

Can daga can barin gate kuma wani babban abune na mazubin shara har da tayoyin sa.

Ya dan ja kasan leben sa ya cije kafin ya tunkari babbar kofar da itace zaka shiga ta sadaaka da cikin gidan.

Bakin sa dauke da sallama ya shiga. Hadadden turaren wutan Chadian khajingru na kamfanin turaren yerwa incense and more (08095215215) ne ya daki kofofin hancin sa. Ya lumshe idanu ya bude yana mai sake shakar kamshin...

Rufe kofar yayi ya saka mata key hadi da zuge labulayen ya cire takalman sa ya saka na yawo acikin gidah. Suna a jere guda biyu acikin abun takalma. Daya pink da ya kuma blue. Hakan ya tabbatar masa da blue din na sa ne. Saboda babban size ne kuma shape din maza ne.

"Assalamu alaikum wa rahamatullah..." Yayi sallama yana sake tura kansa cikin gidan.

Daka shigo wani babban parlor ne mai dauke da kayan furnitures da sukayi matukar dacewa da tsaruwar jeren gidan

Screen din wayar sa ne yayi haske. Ya daga ya dubi screen din. Sakon message da T-Boy ya tura masa,

"Mun gama siyaan baki mun biya yammatan amarya kudin da suka fada... Abokina Allah ya baku zaman lafiya. Ka dai bi yarinyar mutane a hankali."

Siririn tsaki Rayyan ya saki yana murmushi. Alokacin daya karasa karanta sakon T-Boy.

Hannun sa ya saka ya bude dakin daya da ke kasan gidan. Ba kowa aciki ya bude bandakin da ke ciki. Komai a tsaftace a kuma gyare sai kamshi ne ke tashi. Gadon ya kawatu da wani hadadden zanin gado kirar Saudi royal.

Janyo kofar yayi ya rufe ta ruf. Ya fara haura mattakalar benen yana hawa sama. Wani daki da ke kallon kafar benen ya bude shi ahankali. Ya tura kai ciki...

Tun daga bakin kofar hancin sa ke jiyo masa daddadar khumrar da ke tashi daga jikin ta. Kamshi ne mai dadi a hanci da saukar da ni'ima da sanyaya zuciya.

Tana zaune a bakin gadon. Sanye take a lullube cikin laffaya kanta a kàsa. Ba kadan ba tayi masa kyau. Hakama shigar kayan jikin ta sun tafi da shi. kalar purple me duwatsu bakake.

"Assalamu Alaiki... " Ya sake fada a kasan makoshi. Hadi da komawa can dayan gafen gadon da ke lullube cikin zanin gado da bargon sa farare. Masu dauke da kwalliya kalar ja. A jiye kayan yayi...

Ya saka hannu ya bude dan karamun fridge din da ke gefen gadon ya ciro su furar da wasu daga cikin lemuka da yoghurt ya zuba su acikin fridge din..

Ya sake fita ya sauka kasa ya bude wata kofar da yake da tabbacin kitchen ne. Ai kuwa yana budewa kitchen dinne.

Tray ya dauka ya saka plates guda biyu da fork da wuka. Ya dakko cups suma ya saka su akan tray din.

Saman ya haura yanata sauri ya bude kofar dakin ya shiga. Madeeha na jiyo dukkanin motsin sa. Ta sake dunkulewa waje daya tana tamke laffayar jikin ta tamau...

Jajjere komai yayi akan plates wasu akan karamun tray. ya mike bayan ya ajiye komai ya hade hannuwan sa waje daya yana matsawa. Yama rasa ta ina zai fara..?

Gefen ta ya koma ya zauna. Taja baya da sauri ya sake matsawa daf da ita. Ya sanya hannun sa ya kamo kafadun ta tanata mutsu mutsun kwacewa ya hanata ta hanyar rarumo ta baki daya ya kwantar da kanta akan kafadar sa. Hadi da riko ta sosai.

Ya dora labban sa akanta ya sakar mata sumba da ta saka tsigar jkkin ta tashi..

"Madeeha.... !! I've the right..." Ya rada mata a kunnenta daya ...hadi da busa mata iskar bakin sa aciki mai zafi cikin wani salo..

Ta shiga takurewa hadi da dunkulewa... Yasaka hannun sa daya a hankali akan gadon bayanta yana shafawa,

"Madeeha.... ki dena tsoro na please ..Ni fa mijin ki ne Madeeha. Ko..? Uhm?" Ya fada yana lakuce mata karan hancin ta.

Ita dai kanzil bata cewa komai.. Yasa ka hannun sa ya shiga yaye mata laffayar data lullube fuskar ta da shi. Yana ja tana ja.

"Madeeha.. Please... Cire hannun ki." Ya fada yana janye hannuwan nata.

"Zo ki ci abinci...."

"Na koshi..."

"Kika koshi a'ina? Daure dai... Sai da ruwan ciki ake jan na rijiya..."

Tanata turjiyewa a haka dai yayi nasarar yaye mata laffayar da ta lullube jikin ta da fuskar ta baki daya..

"Ta so mu ci abinci... Kinji?"

"Na koshi." Ta amsa shi kanta a kàsa.

Murmushi yayi. Wani dadi na sake ratsa shi yau, Madeehan sa ce a gefen sa su biyu kadai sannan kuma a matsayin matar sa. Idan mafarki yake Allah yasa karya farka.

"Temaka mun ki ci dai my love."

Riko ta yayi suka sauka kasan carpet . Ya daddeba mata komai a plate ya ajiye a gaban ta.

Ya dan langabar da kansa yana kallon fuskar ta da tayi kasa da ita tana matsa hannuwan ta..

"Madeeha .. Zuciyata na dauke da farin cikin da ba zai taba gushewa ba da yardar Allah... Hakika Allah ya cika mun buri na samun ki da nayi a matsayin matata ta sunnah Madeeha..Ina fatan daga rana irin ta yau Allah ya dawwamar mana da farin ciki mai dorewa. Har karshen rayuwar mu. Amin... Ba ki ce Aamin ba.…?"

Madeeha ta kasa cewa komai. Rayyan ya riko hannun ta daya ya saka akan setin zuciyar sa.

"Kinji yadda zuciyata ke bugawa ko? Da kaunar ki na ke kwana na ke tashi Madeeha.. bugun zuciyata kan canza a duk lokacin da idanuwana suka sauka akan na ki., Ina kaunar ki fiye da yadda alkalami zai rubuta. Ina kaunar ki fiye da yadda kwakwalwa zata tariyo.. Ina kaunar ki fiye da tunanin me tunani. Ke kadai nake so.. ke kuma nake burin mallaka. Ke kadai nake kauna na ke kuma adduar Allah ya wanzar mana da zaman lafiya a tsakani... Aamin"

Naman ya babbare ya ciccire kashin da ke jikin sa. Ya matsa daf da ita ya sake kamota tana kwacewa ya saki karfin sa baki daya adole ta hakura ..

"Bude bakin..." Ya rada mata yana kai mata naman bakin ta.
Chapter 62 · 0% Book details