Sashe 58
Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri ta ke tafiya hannun ta rike da bakar leda da ke dauke da magunguna aciki da kullin rubutu.
Tana tafe tana jera tsaki...
"A ringa kiran ki kina 'kin daukar waya.. Na ta ko na zo kuma a hana ni shiga. Gaskiya na gaji... Yar gaba da iska kawai.."
Ta na isa gate din gidan ta gan shi wayam ba masu gadi. Ta dubi gabas ta dubi yamma bata ga masu gadin ba. Zuruf ta shige cikin gidan har tana hadawa da gudu ... Don kada maa su gadin su kora ta su hanata shiga.
Zuruf ta shige cikin gidan. Parlorn ma ba kowa aciki. Sai wata me aiki ta fito daga kitchen hannun ta dauke da wani bokiti zata hau sama.
"Ina wuni?" Me aikin ta gayshe ta.
"Lafiya... Ina hajiyan?" Suwaiba ta tambayi yar aikin .
"Kaman bacci take yi... "
Suwaiba ta daga kai ta sauke akan yar wayar da ke hannunta,
"Bacci yanzu?"
"Ai bata da lafiya ne shi ya sa."
"Tana sama?"
"A'a tana dakin ta na kasa."
"Okay to... Dan ban ruwa ko lemo na jika maqoshi na."
"Toh..."
Suwaiba ta nemj waje ta zauna akan kujera.. Yar aikin ta nufi firji ta dakko ruwa da lemo ta ajiye agaban Suwaiba..
Suwaiba ta dauki robar ta kafa a baki. Sai da ta shanye ta ajiye.. Ta sake daukar robar lemon ta zura shi ta ajiye acikin jakarta.
Mikewa tayi ta nufi dakin da yar aikin tace tana ciki.. hangota tayi a nannade da bandeji fari. Ta saki salati tana tafa hannuwa.
Hajiya Bintu sai sauke numfashi take dakyar..
"Hajiya meya same ki?"
Hawaye suka shjga kwarara daga idanun Hajiya Bintu..
"Hajiya meya same ki?" Suwaiba ta sake tambayar ta tana bin ilahirin jikin Hajiya Bintun da kallo.
Hajiya Bintu ta fashe da kuka tana jujjuya kanta ahankali..
Dakyar ta iya bude bakin ta da ke ta rawa tace,
"Hatsari nayi Suwaiba.... Ya ake ciki?"
Suwaiba ta sake wage baki tana kallon Hajiya Bintu da ke anannade kaman tsumma. Ta ja hannu ta daura a haba tana sake sallallami,
"Gaskiya na tausaya miki Bintu. Ko shi ya saka bakya daukar waya ta?"
Hajiya bintu ta daga kanta a hankali tana cigaba da zubar da hawaye .
"Duk yadda akai wani ko wata ne suka yo miki chune ya fada akan ki.. Sannu Bintu."
Hajiya Bintu ta cigaba da rera kukan ta tana girgiza kai.
Alhaji Hammadu ne ya ke sakkowa daga mattakalar benen gidan. Hannun sa daya yana gyara gaban rigar sa ...
Ya karasa sauka daga benen ya yi hanyar kofar fita. Har ya dora hannun sa akai zai bude kofar sai ya fasa. Tunowa da bai yi wa Hajiya Bintu sallama ya fita ba.
Ya nufi dakin da matar sa Hajiya Bintu ke jinya acikin sa. Tun daga baya baya ya fara jiyo maganganu duk daukar sa Hajia Bintun ce da 'yar ta Nabeelah..
"Ki sha kurumin ki Bintu... Ai na gaya miki aikin sa kamar yankan wuka yake... Da baki dauki wayoyin da nake ta kiran ki ba ai koma masa nayi nace ya dage mana... Yace uwar mijin na ki ma kwanan nan zata shantala lahira. Za'a raba kaunar da ke tsakanin ta da shi dan nata me gidan naki kenan, Sannan shi Rayyan za'a cire masa kaunar yarinyar nan a zuciyar sa ya dena son ta ... Mijin naki kuma sai yadda kikayi da shi kamar tandar waina.. Yace ko kara kika saka ba zai tsallake ba..."
Gaban sa ne ya tsananta bugawa. Idanuwan sa suka kada sukayi jazir. Wata doguwar jijiya da ke cikin kan sa ta fito rangadadau a goshin sa.
Ya danne leben sa da karfi tamkar zai fasa hakoran sa. Ransa yayi baki. Ya hau ya cika yayi fam kamar zai fashe.
Ya saka hannu zai bude sai ga Nabeelah 'yar sa ta sakko daga sama hannunta rike da littafi ta yafa mayafi akan ta.
"Bappah.."
Juyawa yayi da sauri ya hango ta. Ya kakaro murmushi ya sakar mata. Yana jiyo muryar Hajiya Bintun na cewa,
"Yi shiru Suwaiba za a shigo."
"Bappah ina kwana?"
"Ina gajiya...? Nabeelah"
"Alhamdulillah Bappah... Zan je makaranta ne na manta ban gaya maka ba jiya. Zamu fara registeration yau."
"Okay Nabeelah. Me kike bukata?"
"Bansan ko zanyi photocopy din takardun ba. Sannan da abinci ma ko za'a dade."
"Tohm Nabeelah.. Kaman nawa ne zai ishe ki. Ko kuma ungo dai." Ya karasa fada hadi da zaro kudi masu yawa ya mika mata ta sunkuya ta karba
Sa hannu tayi ta bude kofar dakin.. Tuni Suwaiba ta koma gefe ta rakabe tamkar mumina. Murmushi Alhaji Hammad yayi alokacin da Suwaiba ta gayshe shi cike da makirci har da su ce masa ya jikin matar tasa Bintu. ?
Ya saka kai ya shiga dakin bakin sa duake da sallama . Idanuwan sa fes akan Hajiya Bintu da ke runtse idanu irin ciwon nan yana cin ta..
Suwaiba ta mike da sauri tana gyara zaman mayafin jikin ta.
"To Hajiya ni zan tafi. Allah ubangiji ya baki lafiya yasa kaffarane."
"Nagode..." Cewar Hajiya Bintu.
Har ta kai kofa alhaji Hammadu ya dubi leda baka viva dake gefen bakin kujerar da ta tashi
"Wannan ba kayan ki bane?"
Suwaiba ta juya da sauri. Idanuwan ta akan ledar ta dauka ta ajiye daga karkashin gadon
"Gashi nan ba yawa Hajiya... Allah ya bada lafiya Amin."
Kallon ledar yayi bayan ta fice sum sum kamar tsohuwar annamimiya.
Har zai dauki ledar sai kuma ya fasa. Ya juya da sauri yabar cikin dakin bayan ya mata ya jiki.?
Kai tsaye ya wuce motar sa ya shiga dama direban sa na ciki yana jiran sa. Har sukayi njsa suna tafiya baki daya hankalin sa baya jikin sa. Duba da direban sai tambayar sa yake Ina suka dosa? Shiru Alhaji Hammadu baya magana.
"Ranka ya dade ina muka yi?" Direban ya sake tambaya a karo na ba adadi..
"Afuwan...Me kake cewa?"
"Ca nayi Ina zamu yi?"
"Muje gidan gonar chalawa...."
Gidan gonar suka nufa... Ran sa duk ba dadi. Sam ba shi da nutsuwa gaba daya maganganun da Suwaiba ke fadawa Hajiya Bintu ne suke masa yawo a cikin kan sa..
Kasa hakuri yayi ya ce da direban su juyar da kan mota su koma gidah . Direban ya juyar da motar suka dauki hanyar komawa gidah,
"Ranka ya dade lafiya kuwa?" Direban ya tambaye shi ganin yanayin da yake ciki..don Sam ha haka ya saba ganin sa ba tabbas yana dauke da damuwa.
"Ba komai kakka damu..."
Suna karasawa gidan ya fita da sauri ya shige ciki bakin sa dauke da sallama.
Kan sa tsaye ya shjga cikin dakin . Hajiya Bintu ta saki baki bacci ya dauke ta.
Bakar ledar na gefen ta ta rufe da zanin gadon da ta rufa da shi. Ya janye ledar da sauri ya fita daga cikin dakin.
Zazzage kayan cikin ledar yayi. Akwai wani dauri da aka kulleshi kulli biyu.an sossoka allura ajikin sa.
Sai wani kwado bayada rai shima an kulle bakin kwadon da zare da allura. Sai kuma wata laya me hatimi an saka ta acikin wata kwalba
Sai garurruka na hayakin turare. Da wasu kullin ledoji fal da rubutu ackin su an daddaure acikin leda kanana.
Girgiza kai kawai ya hau yi. Ya tuno sanda a baya ma'aikatan gidan ke kawo masa zancen Hajiya Bintun na yin haqa a gidan ta na bunne abubuwa.ko ta fito wajen gidan tana hayaki. Sam baya yadda da abubuwan da suke fada.
Ya saka hannu ya toshe bakin sa. Wai mahaifyar sa da ta kawo shi duniya ita akeson kashewa a kuma raba kaunar da ke tsakanin su. Tunanin sa ya gangaro kan san su na biyu Rayyan shima zaa raba shi da yarinyar da yake kulawa. Ko wacce yarinyar ce ma oho . Ya sake tunano maganar Suwaiba da ke cewa aikin bokan kamar yankan wuka yake. Kuma sai yadda Hajiya Bintun tace. Idan ta saka kara ba zai tsallake ba..
Ledar ya dauka bayan ya mayar da komai ciki ya fita ya koma ya zauna a mota ledar na gefen sa
Wayar sa ya janyo ya kira Rayyan. Bugu biyu Rayyan din ya dauka yana gayshe da shi.
"Kana ina ne?"
"Ina gida.... Amma yanzu zan fita "
"Okay to ka zauna gani nan."
"Toh. Bappah.." Ya zare wayar daga kunnen sa yana tunanin abunda mahaifin nasa zai ce masa.
Ko da Alhaji Hammadu ya karasa gidan kanin sa Alhaji Harith. A bakin gate yaci karo da Alhaji Harith din zai fita. Ya tsaya suka gaysa,
"Na tafi dakko Yaya Hadiyyah da yaran ."
"Okay sai ka dawo Ina ciki nima wajen Hajiya."
"Toh Yaya..."
Suna shiiga cikin gidan ya dauki ledar a hannun sa ya shjga sashen hajiyan da Hadiyyah ummy zasu zauna... an kawata shi sosai.tana kishingide akan kujera tana kalllon waje
"Hajiya barka da safiya."
"Barkan mu Hammadu. Yaran kalau?"
"Alhamdulillah Hajiya.,"
"To Allah ya temaka yabada saa ."
"Amin..." Yana karasa cewa Amin ya fashe da kuka. Kuka yake kamar karamun yaro. Kuka ne yake yin sa mai tsuma zuciya. Kuka ne yake yin sa gwanin ban tausayi. Kuka ne me dauke da sakwanni ga wanda akewa shi.
Hankalin Hajiya Fadila ya tashi sosai. Ta mike daga kishingidar da take tana duban sa
"Menene? Meya faru dan birni? Ka gaya mun don Allah damuwar ka."
Sai da ya zubar da hawayen sosai sannan ya samu sauki da sassauci a zuciyar sa. Ya bude baki ya sanar mata komaj. Hajiya Fadila tayi murmushi kawai,
"Don Allah kar wannan ya dame ka... Allah yana sane da komai .. shi zai mana sakayyaaa.. Kaga wasu ai tun a doron duniya suke fara daukar hukuncin Allah akan su...."
Ya karkada kai cikin tabbatar da hakan .. Hajiya Fadila tayi murmushi kawai tashiga kwantar masa da hankali har ta samu ya sakko ya kuma samu nutsuwa da salaama a zuciyar sa.
Cikin haka sai ga shigar Rayyan dakin. Ya tsugunna ya gayshe da su ya samu waje ya zauna. Alhaji Hammadu ya daga kai ya dube shi,
"Rayyan... Kana... Kana neman wata yarinya ne da mahaifiyar ka bata aminta da ita ba?"
Gaban Rayyan ya buga. Ya rasa ma abunda zai ce.
"Kayi shiru."