Sashe 95
Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read
yake, gaba daya she was uncomfortable, Inna ta shigo tace "Allah maka albarka, kai kadai dama xance ka siyo ka siyo" kitchen ta tafi ta dauko plate biyu ta xauna kan tabarma tana gogewa ta bude ledan kazar ta raba biyu, daya nata daya nashi, can dai ta kallesa tace "Toh ita kuma warcan matar ya xa mu yi da ita, tunda ba da ita aka siyo ba" shi dai Mujaheed bai ce komai ba, Inna ta tabe baki ta dauko wani plate din ta dau cinya daya da tsoka daya ta dangwala a plate ta mika ma imaan tace "Toh gashi dai, ido guba...." Ba tare da imaan ta kalleta ba ta girgixa kai gently tace "A'a baxan ci ba" Kallonta Mujaheed ya dinga yi da mamaki, inna ma ta saki baki tana kallonta tace "Dama baki da lafiya shine kika yo min nan salon ace a nan ciwo ya tashi ni patuu?? don cuta kadai ke hanaki cin kaza ni dai na sani" Imaan bata ce komai ba bata kuma kalleta ba, can ta mike ta nufi kofa tace "Ni fa a koshe nake" daga haka ta fice a parlon.