Sashe 90
Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bayan fitar su, haka kawai suje su ja mana girgixan kasa a gidan" Mikewa inna tayi tace "Har naji sanyi da na gaya maka wllh, ni dai bari in kada shayina in sha, ba ruwana da wahala" Daga haka ta shige kitchen, Mujaheed ya dafe kansa, lkci daya ya dago yyi murmushi, da cup biyu ta fito tace "Ko kai ma in kada ma ka shayin ne?" Mujaheed ya kalleta yace "Toh" Imaan ta gama goge balcony din ta tafi cikin parlor tana cire mask din bakinta, Breakfast Ammi ta mika mata a tray ta ajiye ma Daddy a dinning table, karasawa tayi ta amshi tray din tana ajiyewa dinning sai ga Daddy ya fito, imaan na kallonsa ta marairaice a hankali tace "Daddy xan je gidan gwaggwo yanxu, sai in dawo bayan bikin Aunty Halima" Daddy ya ja kujera ya xauna yace "A'a sai dai ku dinga xuwa kuna dawowa da mamarki" Ammi tace "Sae kace handbag, kawai ka barta ta tsaya can har bayan bikin mana" yace "kin dai fi ni sanin condition dinta, so I don't need to talk much" Ammi tace "Imaan fa ba yarinya bace yallabai, she can take very good care of her self" daddy bai kuma ce mata komai ba. Duk yanda Ammi ta so Imaan ta jirata su fita tare kin yarda tayi don tuni ta kira Sadeeq bayan daddy ya amince ta tafi gidan gwaggo ta sanar masa, sai gashi ko 15 mins ba ayi ba ya kirata wai yana saman layin nasu yana jiranta, Ammi ta dinga kallonta da mamaki ganin ko gama rufe karamin trolley din bata yi ba amma xata ja haka ta fita, cikin tsawa Ammi tace "Wai saurin uban me kike haka Imaan??" Waigowa tayi da sauri tace "Ba komai fa Ammi" Ammi tace "Rashin natsuwa ce kenan, ke kam yaushe xaki yi hankali ne irin na sauran jama'ah, dubi fa yanda kike jan jaka a bude saboda hankali ya maki kadan" Daddy dake xaune dinning yace "Komai dai ace sai anyi fada, this isn't fair" Ko tanka sa Ammi bata yi ba, Imaan ta durkusa a hankali ta karasa rufe jakar, Ammi tace "toh xaki iya daukar jakar har bakin titi?" Imaan tace "Ai ba nauyi Ammi, kuma ja xan yi tunda titin layin na da kyau" Ammi tace "Toh Allah ya kiyaye" daga ma Daddy dake kallonta hannu tayi ta fita, ta rufe kofa kenan sai ga Mujaheed ya taho daga part din inna, kallonta ya dinga yi tayi saurin dauke kai gabanta na faduwa, kallon Sashin su yyi sannan ya kalleta yace "Ina xa ki?" Backing dinsa tayi, tayi kamar tana gyara jakar ne ta turo baki tace "Gidan gwaggwo" Jin bai ce komai ba ta leka sa daga durkushen da take, kallonta taga yake yi har sannan ta kara turo baki, jin tafiyarsa ta saci kallon gefenta taga gate ya nufa, sai da ta jira taga fitarsa gaba daya, bayan few minutes ta ja jakarta ta xuwa gate, tsaye ta gansa jikin motarsa ya rungume hannu, gabanta yayi mugun faduwa, ji tayi kamar ta rushe da kuka, tayi saurin dauke kai xata nufi saman layin yace "Xo ki sa jakar a mota" Da sauri ta kallesa sai kuma ta fashe da kuka ba hawaye tace "Yaya Ammi da Daddy fa cewa suka yi in tafi da kai na kar wanda ya kai ni wllh" Wani mugun kallo ya mata yace "Before the count of 3 do what I said now" jingina tayi da gate hankali tashe tace "Don Allah yaya ka wuce wllh bana son ka kai ni xan je da kai na" hade rai yyi sosai ya daga finger dinsa daya yyi indicating da one, sannan two, bata jira ya nuna third finger din ba ta ja jakar hawayen gaske na xubo mata ta bude back seat ta ajiye ta rufe, cikin rawar murya tace "Xan dauko hand bag dina" bai tanka ta ba ya xaga ya shiga driver seat ta koma cikin gidan ta fashe da matsanancin kuka, parking space ta tafi ta tsaya ta yi dialing number Sadeeq, yana fara ring ya katse ya kira ta, ta kai kunne cikin sanyin murya tace "Don Allah kayi hakuri Yaya xai fita aiki yanxu shine yace xai yi dropping dina, ni kuma baxan iya cewa A'a ba kar ya min fada" Sadeeq yace "Ohk no problem imaan, anjima da yamma xanje can gidan in sha Allah" a hankali tace "Kayi hakuri don Allah" yace "Noo ba komai dear, ai yaya ne, kar mu yi laifi ko" tace "Toh nagode" daga haka yyi mata sallama ya katse wayar ta nufi gate fuska daure ta fita, bude motar tayi ta shiga tana cika tana batsewa, ta gefen ido ya kalleta ya tada motar ya bar layin. Sun yi nisa sosai kamar mai counting words dinsa yace "I told u what to tell Abba... but you told him a different thing saboda kin raina ni koh?" A d'an tsawace ya kare maganan, Kin cewa komai tayi sai ma kauda kai da ta yi tana kallon waje, parking yyi ganin haka ta juya da sauri tana kallonsa kamar xata yi kuka tace "Don Allah kayi hakuri yaya, ai ya ma daina kirana, tun shekaranjiya ni bai kira ni ba ma" Fuska daure Mujaheed yace "In ga wayar ki?" Xaro ido tayi tace "Yaya ai yana gida" tana magana tana kokarin boye wayar a jikinta, fixgota yyi, ta yi wani kara ta riko hannunsa tace "Wayyoo yaya me nayi maka..." Ya dage Hijab din jikinta ta xaro ido tace "Yayaaa ka bari" bai saurareta ba har sai da ya kwace wayar, dubawa yyi yaga ta sa password, ya mika mata yace "Bude..." Make kafada tayi tana wani murmushi, ya dinga kallonta kafin ya daura wayar kafarsa ya ci gaba da driving din, har suka iso gidan gwaggwo bai sake ce mata komai ba, ita ma bata ce masa komai ba, yayi parking kofar gidan, bude motar tayi ta fita, shi ma ya fito, ta bude back seat ta dau jakarta ta rufe motar, danna lock yyi ya wuce cikin gidan ta bi sa da kallo kamar xata yi kuka, can ta bi bayansa, Gwaggwo ce xaune parlor tare da wasu yan uwanta duk maxa, Mujaheed ya xauna kasa ya gaisheta sannan su ma ya gaishe su, Gwaggwo da fara'a Gwaggwo ta amsa tana cewa "Ikon Allah, yau Mujaheed ne gidan namu, dama kana garin Mujaheed" ya d'an yi murmushi yace "ina nan Gwaggwo ya kwana da yawa" tace "Lafiya lau... Ka guje ni Mujaheed" Har sannan yana murmushi yace "Kiyi hakuri gwaggwo yanayin aiki ne, xan je anjima da yamma in dawo tun da kina da baki" Imaan ta xaro ido jin abinda yace, Gwaggwo tace "Ka tabbatar Mujaheed" yace "Xan dawo da gaske" tace "Toh madallah, sai ka dawo, Allah ya kiyaye hanya, ina nan ina jiran ka" Imaan dai na makale jikin kofa ta ki shiga gidan, Mujaheed ya fito, kallo daya yyi mata ya dauke kai ya nufi gate, ta bi sa da sauri tace "Don Allah yaya ka ban wayata" wani kallo da ya tsoratata ya mata, ta koma baya a hankali, ya nufi gate ya fita gidan. Tun da yamma yayi hankalin Imaan ya tashi, tasan yanxu kila Sadeeq ya kira ta wayar Mujaheed kila kuma ya daga, sannan ga Ammi tana gidan, duk abun ya taru ya mata yawa, ita kadai ce kwance dakin Gwaggwo don anty Halima na tare da kawayenta, ana idar da la'asar sai ga Halima ta shigo dakin ta mika ma Imaan wayarta tace "Imaan gashi abokin ya Muhsin xai maki magana" da sauri Imaan ta mike daga kan darduman da take xaune bayan ta idar da sllh ta amshi wayar Anty Halima ta juya ta fita, xaunawa tayi gefen gado tayi masa sallama a hankali, ya amsa yace "Is ur fone down?" Xaro ido tayi da farko ta rasa abun cewa can tace "Um, ka kira a kashe koh?" Yace "Sure" ta langwabar da kai tace "Ehh a kashe yake" yace "Ohk, ina waje fa" ta wani xaro ido again, a hankali tace "Toh ina xuwa" yace "Ohk I am waiting dear" mikewa tayi ta fita, rasa wanda xata gaya ma ana kiranta a waje tayi don tsoron sanar da Ammi take, gwaggwo ta shiga nema, ta sameta a Wani empty room tare da Ammi da maman Halima, ta gaida maman Halima da ta amsa mata da fara'a tace "Ya Abban ki Imaan?" Imaan tace "Yana lafiya mama" daga haka ta nufi gun Gwaggwo ta durkusa murya can kasa tace "Gwaggwo wai Sadeeq yana waje yana jirana" Ammi dai sai kallonta take don bata san abinda take gaya ma mahaifiyar tata ba, Gwaggwo tace "Sadeeq dai da na sani abokin Muhsin?" Imaan ta sunkuyar da kanta, Gwaggwo tace "Ikon Allah, saurayin ki ne kenan" imaan ta boye fuskarta, gwaggwo tayi dariya tace "A'a gaskiya naji dadi, Sadeeq ai yaro ne mai hankali da sanin darajan mutane, tashi ki tafi ina gaishesa, ko kwana uku da suka wuce ya xo gaisheni da Muhsin, gaskiya nayi farin ciki da wannan al'amarin" Ammi dai sai kallon Imaan take, mikewa imaan tayi a hankali ba tare da ta yarda sun hada ido da Ammi ba ta fita, tana fitowa parlor ta ji sallamar Mujaheed, still tayi inda take tsaye, Gwaggwo na jin muryar sa tace "Ashe dai da gaske yake xai dawo" Mamaki ya sa Ammi ta kasa cewa komai jin muryar sa ita ma, mikewa Gwaggwo tayi ta fito parlor murmushi dauke fuskarta tana amsa sallaman tare da few mutanen dake parlon, shigowa yyi suna hada ido Imaan ta juya masa baya da sauri kamar xata yi kuka, ya nufi kujera ya xauna Gwaggwo na masa sannu da xuwa, ta kitchen imaan ta bi ta fice daga gidan. Sauke glass Sadeeq yyi ganin ta, ta sunkuyar da kai har ta isa jikin motar, ya fito ya jingina gefenta smiling cikin cool voice dinsa yace "Good evening" kasa kallonsa tayi, a hankali tace "Ina yini?" Yace "Lafiya lau Imaan, ya Ammi fa?" Ta kalli cikin gidan tace "Tana ciki" yace "Amma ba tare ku ka xo ba ai?" Ta girgixa kai tace "Na riga ta" har sannan ta ki