← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 233 OF 292

Sashe 233

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

ta dade bata ji farin cikin da take ji ba a lkcn, ta xauna gefen gado bayan ta sa kayan tana kallon Hajiyarsu dake waya tana cewa "Ehh dama shine abu na farko da nake son ayi mata, Ehh sunanta Rukayya, xa mu yi waya anjima" daga haka ta katse wayar, Safeenah ta xaro ido tace "Hajiya Mujaheed ne fa a parlor" Hajiyan Marafa tace "Mujaheed Kuma? To me ya xo yi??" Safeenah ta bata rai ta mike ta nufi gaban madubi ta feshe duk jikinta da turare sannan ta dau karamin gyale ta fita, tana shigowa parlor ganinsa a xaune ta nufesa da sauri ta fada jikinsa ta rungumesa gam, sai kuma ta fashe da kuka tace "I've missed you a lot Mujaheed, don Allah ka xo ne mu koma gidanmu mu ci gaba da xamanmu mu kadai??" Yace "Tafi ki hada kayan ki" ta xaro ido tace "Da gaske??" Yace "I am waiting" gaba daya su Hajiya Baturiya dama sun kwaso kayanta daga gidan Mujaheed bayan abinda ya faru, ta mike da sauri ta tafi daki tana kallon Uwarta tace "Mummy yace in hado kayana wllh" Hajiyan Marafa tace "Babu inda xa ki je sai an gama aikin da ake yi..." Safeenah ta fashe da kuka tace "Ni dai wlh Mummy ki Bari in bisa gida fa xa mu wuce ya ma saki yarinyar Ina ji, don Allah ki bar ni mu je" Hajiya Marafa tace "Cewa nayi ki bari sai an gama aikin da ake yi tukun, ke ana kokarin kwatar maki yan ci kin kasa ganewa sbda son miji" Safeenah tayi kamar xata yi kuka tace "Ni dai Hajiya tafiya xan yi daga karshe sai in dawo idan an gama aikin, amma ni kam da baku bata kudin ku ba ni kadai na isa Hajiya Rukayya a duniyar nan, wllh sai na rabata da d'anta, Auren ma da aka masa Ina jin babu shi yanxu" daga haka ta fita xuwa dakinta ta hau hada kayanta a jaka, cikin few minutes ta gama ta jawo jakar downstairs, Mujaheed ya dinga kallonta har ta iso parlon, Sajida ta dinga mata wani kallo tana girgixa kafa, Mujaheed yace "Hajiya fa?" Safeenah ta koma sama da sauri ta shiga dakin uwarta tana murmushi tace "Hajiya wai ki fito ku gaisa" Hajiya Marafa tace "Bai kai wannan matsayin ba, banda ma kin nace ina mu Ina hada xuri'a da Rukayya? Waye bae san Rukayya da abinda take yi ba, in sha Allahu ta ja ma kanta abinda ba shikenan ba tunda har ni tayi ma haka, xan kuma nuna mata mu bama xama da kishiya, Ana gama aikin da ake dama xan tako gidan da kai na" juyawa Safeenah tayi ta fita dakin tana cewa "Bayan nace maki babu auren yanxu wace kishiya kuma, ai sai dai mu gwada mata hankali kawai..." Tana dawowa parlor ta kalli Mujaheed tace "She's in the bathroom mu je kawai dear" mikewa yyi ya nufi kofar fita ta bi bayansa tana kallon Sajida tace "Sai mun yi waya Aunty Sajida" ko kallonta Sajida bata yi ba har ta fita, sai da suka shiga mota Mujaheed yace "Zaria xa mu je" Safeenah ta xaro ido cike da farin ciki tace "Ae ya fi dear nah, gwara mu yi nisa da gida kawai, after some months sai mu dawo kaga bbu wanda xai kara tada wani maganar, wllh hakan ya fi, har naji hankali na ya kwanta sweetheart" shi dai bai ce mata komai ba ya tada motarsa don duk hankalinsa yyi kan Imaan da ya bari tana bacci....
Chapter 233 · 0% Book details