Sashe 110
Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
fa" yace "Sai in daga ki sweet" boye fuskarta tayi ya nufi kofa yana murmushi ta xaro ido tace "Ka manta ledan ka" ba tare da ya juyo ba yace "Na ki dai" shiru tayi tabi sa da ido sannan ta bi bayansa, kamar mai tausayin kasa ta isa kusa da shi don tsaye yyi yana jiranta, a jere suka dinga tafiyar yana kallonta ita ko ta ki yarda ta kallesa, Ni kam nace waow perfect couples they will make... Lol, A dai dai bangarensu Maimoon Umma ta fito ta nufi parking space kana ganinta kasan fita xata yi, Sadeeq ya kalleta yace "Ina yini" tace "Lafiya lau" Imaan tayi kasa da kai a hankali tace "Ina yini?" Banxa Umma tayi mata ta bude back seat xata shiga, Imaan dai bata kalleta ba suka fita tare da Sadeeq, ido hudu tayi da Mujaheed dake xaune gun Mai kiosk dake kusa da gate din su, Dauke kai tayi da sauri, Sadeeq bai ma lura da shi ba, ya isa gun motarsa tana biye da shi, Yana kallonta yace "Keep on greeting her xata amsa wataran, you will loose nothing don kina gaisheta...." murmushi kawai Imaan tayi, ya kafeta da manyan idanuwansa, murya can kasa yace "Plss ki dinga cin abinci da yawa sweet, kin rame fa" ta wara ido tace "A'a ni dai haka nake" kallonta kawai yake bai ce komai ba, ta sunkuyar da kai tana wasa da fingers dinta, underneath his breathe yace "I have always loved you from day 1 imaan..." kasa kallonsa tayi gabanta ya dinga faduwa, kamo hannunta yyi a hankali ya lumshe ido xai kai lips dinsa ta kwace hannun da sauri tana satan kallon inda Mujaheed yake, kallonsu taga yana yi, Sadeeq ya kalli inda ta kalla suka yi ido hudu da Mujaheed, dauke kai yyi a hankali yace "We will talk later dear" daga haka ya shiga motar ta juya ta nufi gate gabanta na faduwa tana satan kallon Mujaheed da ya bi ta da ido fuskarsa dauke da wani expression, rufe gate din tayi tana kara kallonsa sannan ta wuce part din su da sauri. Mujaheed na gama parking ya juya yana kallon ummansa dake Bayan motar sai danna waya take, ta daga kai da sauri tace "Au, har an kawo ashe" bude motar tayi bayan ta ajiye wayar tace "Ka jira ni ba dadewa xan yi ba" yace "Umma aiki nake son wucewa don Allah kar ki dade" tace "Na sani baxan dade ba Mujaheed" daga haka ta fito motar ta shiga gidan Hajiya Balaraba, ita kadai ce babban gidan duk kishiyoyinta dama ta rabasu da gida, Hajiya Balaraba dake parlor xaune tace "Daga Ina haka Hajiya Rukayya" Umma tace "Daga gida Ina son kai ma Hajiya Saude kudin da ta ranta min na ba mutumi, sannan ku dai xauna da shiri sati mai xuwa xa a kai lefe gidansu Safeenah" Hajiya Balaraba tace "Toh Allah dai ya kai mu lafiya, amma ya ku ka kare jiya ina ta son in kira ki ko inje gida in sameki" Umma ta tabe baki tace "ya dai sa in rubuta masa abinda nake so ya faru, na kuma rubuta yace min in sha Allahu an gama, abu ne mai matukar sauki.... Kar ki so ki ga irin farin cikin da nake wllh Hajiya, idan hakan ya faru ae har Aisha ta mutu baxata rabu da ciwon xuciya ba" Hajiya Balaraba ta xaro ido tace "Toh me kika rubuta halan?" Umma ta rike ha6a tace "Cewa yyi kar in gaya ma kowa, ki sha kurumin ki aminiya, komai xai fito fili xa ki gani" Hajiya Balaraba tace "Amma xa su yi auren kuwa" Umma tayi dariya tace "Ehh to yace yaga da auren, amma ban jin abinda xai faru xai sa ayi auren nan... Kinga bari inje na bar Mujaheed yana jirana a waje" sallama tayi mata ta fita tana murmushi.