← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 260 OF 292

Sashe 260

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Rukayya ya kamata ta cuci yar sa kwaya daya da Allah ya basa? Me yayi mata da xafi haka, banda ma kyautatawa da tsaya mata da yake yi a lamarinta?? idan ma tana jin haushin Aisha ne Imaan baxata ci albarkacin ubanta Bukar mutumin kirki ba..." Kuka inna ta fashe da har da shessheka tace "Ni Mujaheed ne ma abun tausayi, sam yaron bai yi dacen mahaifiya ba, gashi yaron kirki da yasan ya kamata ga tarbiya kaca kaca, ko ya xai dau wannan xancen oho, Ni dai Allah ya isa tsakanina da Rukayya bakin cikin xuwa makka duk shekara da ta min, shari'a ta da ita sai gaban ubangiji don wllh wllh ban yafe ba, uban wa gareni dama da xai kai ni makkan duk shekara banda Sadeeq din....." Daga haka ta fita parlon tana share idonta. Ammi na xaune dakin Imaan tun bayan fitar Umma, Banda hawaye babu abinda Imaan ke yi har da shessheka, Ammi dai tayi tagumi ta ma rasa abun cewa, cikin rawar murya Imaan tace "Ammi ko don saboda Yaya ai bai kamata Abba yayi haka ba, I don't know how he will take this, why will all this happen because of me?" Ammi dai tayi shiru bata ce komai ba, Imaan na son gaya ma Ammi abinda ya faru ranan Thursday a zaria da ya sa suka dawo gida amma ta kasa gaya mata sbda alkawarin da tayi baxata fada ba a gida, da ta tuna ita ce dalilin mutuwar auren Umma sai ta ji wasu sabbin hawayen sun xubo mata, Ammi ta girgixa kai a hankali tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un...." mikewa tayi ta fita dakin a sanyaye, duk da tasan babu sauran aure tsakanin Umma da Abba ta fita xuwa parlon Abba. Karfe biyar saura kamar yanda Abba yace babban motar da xai kwashe kayan Umma tass ya shigo gidan, Umma na can dakinta tare da Rahma da Ummi da Maimoon dake taya ta kuka kamar ransu xai fita, Seeyama ma na xaune dakin ta kasa cewa komai sai hawaye, Aunty dai na tsaye jikin mirror tayi tagumi ba uhm ba uhm uhm.... Har parlor Mujaheed ya samu Abbansa ya duka nan kasa cikin sanyin murya yace "Abba dama nace don Allah a bar kayan yanxu ko daga baya sai ni in kwashe" shiru Abba yyi yana kallonsa, can Abba ya gyada kai a hankali yace "Toh ba damuwa, do you have any idea of where she will be going now?" Mujaheed ya sunkuyar da kansa yace "Xan kai ta Zaria yanxu" Abba yace "Ur home?" Mujaheed ya gyada masa kai, Abba yace "Ina xaka ajiye Imaan?" A hankali Mujaheed yace "Nan kaduna" Bayan few seconds Abba yace "I am sorry Mujaheed, I also Neva saw this coming but I think this is the best, ga can abubuwan da kace min sun faru a gidan ka wanda har ya janyo ka saki matarka bbu sauran aure tsakanin ku, sannan ga wannan, sure i was frustrated, but na shanye abubuwan da mahaifiyar ka take min shekara da shekaru, Ina barin ta tana cin albarkacin ku, but today's own is beyond me, I think this is best, Allah kuma yasa hakan ya fi alkhairi, Ina me baka hakuri coz I know this is sad, sannan abinda yasa nace ta tafi yau saboda wannan mata ta Bulasawa, kaga ko da xata dawo bata ganta ba komai xai xo da sauki, mu kuma sai mu basu hakuri, sai kaga albarkacin mu ta hakura..." Mujaheed bai iya yace komai ba hawaye ya kawo idonsa, Abba ya mike ya shiga daki ya dauko kudi ya mika masa yace "You give her this, sae ta rike a hannu, Allah ya maka albarka" mikewa Mujaheed yyi kansa a kasa yace "Toh ngd Abba" daga haka ya fita parlon.
Chapter 260 · 0% Book details