← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 160 OF 292

Sashe 160

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daddy ne xaune parlon Inna bayan su kawu Bala, Umma da kawunnanta sun fita, Inna ta tace "Wlh wllh Bukar ka ji rantsuwar musulmi ko, to Rukayya ta ci albarkacin ka ne, don ina jin kunyan ka ainun, amma idan ta sake ko da min kallon banxa ne a gidan nan to aurenta da Ahmaduna ya kare ba ruwana, xan nuna mata ni na haifesa ba wani shegen ya haifa min shi ba, yanxu ma ni wllh darajar ka da na Mujaheed ta ci, tunda ni nayi wahala da shi kuma yana min biyayya, kai ma kuma kana min biyayya, matar da ma ba wai son matar ka take ba amma ka dinga tsayawa tsakanin ka da Allah kan lamuranta, ita bata ki ba ma ta cutar da Aisha ba wllh, kai kuma duk ka damu da lamarinta, duniya dai ba gaskiya" Shi dai daddy bai ce komai ba yana sauraranta, tabe baki tayi ta mike tace "Ni dai ba ruwana, kawai mata ta wani taho min da rubabbun mutane su ban hakuri, wllh ta ci albarkacin Mujaheed da sai na masu koran kare ba kunyar kowa xan ji ba, ba ruwana, matar da ba tsoron Allah gareta ba balle a raga mata" Daddy dai ya bi ta da kallo har ta shiga daki sai ga ta ta fito ta xauna tana kallonsa tace "Kana ji na Bukar, ni dai duniyar nan kaf ba wanda bai san imaan takwarata bace, kuma kowa yasan ita kenan Allah ya baka, ita kenan jikata a wajen ka, Toh ya dai fi babu ai, sabili da haka gaskiya ni dai ga dubu ashirin dina da nake ta tarawa a samo tikeken rago da ya kusa d'an mariki a yanka mata na saukan nan, Allah kuma yasa na tsoron Allah xata yi, yayi mata albarka ya hada ta da mijinta na gari wato wannan yaro Bulasawa...." Shiru Daddy yayi yana kallon kudin da take mika masa, tace "Haba ka amsa mana yaro, ka bar min hannu a sagale" d'an murmushi yayi yace "Amma Inna kin fa san ba ita kadai xata yi sauka a gidan nan ba" tace "Toh ai shi sa nace takwarata" ya girgixa kai yace "Ai Ummi ma takwarar ki ce" Bude Baki tace "Yau naga abinda ya isheni, ji Bukar da wani xance, to cewa nayi ban sani ba, ai xuciya ma na son mai kyautata masa, Ummi ko gaisuwar kirki tana min a gidan nan balle in dinga tuna cewa takwarata ce, ni dai ba ruwana a dinga jin tsoron Allah, yanxu meye ma'anar hakan da kafada salon Ahmadu ya ji ya kullace ni, ni dai gashi ka tafi bakin ka a leko ka siyo mata tikeken ragon da nace a kawo mata" mikewa Daddy yyi yace "Toh Allah ya saka da alkhairi, sai anjima" tace "Toh kai dai ka ja bakin ka kayi shiru, abinda naman ma duk xa a tsakura ma kowa da kowa a gidan" shi dai daddy bai ce komai ba har ya fita. Washegari asabar da wuri aka tashi a gidan aka fara girke girke, Ammi da Aunty ne ke girkin a nan bayan kitchen din su Aunty, abinci kala uku xa suyi, sae soye soye, tun daren jiya dama Ammi tayi samosa da spring rolls, Aunty kuma tayi cakes da doughnuts, Umma sai kai wa da kawowa take kamar dai me neman abu fuska a daure, ta shiga ta fita, babu dai wanda ta ce ma sannu da aiki cikinsu, su ma babu wanda ya kalleta, Maimoon ne da Ummi suka shigo kitchen ko wanne sanye da Sabbin dinkin da Daddy yayi masu na atamfa gaba daya su uku masu saukan har da imaan, da Hijab dinsu ash colour yana jan kasa, sosai suka yi kyau, Aunty tace "kun yi kyau sosai, amma kuna kallon agogo dai koh" Ammi tace "Allah ya sa ita wancan ta gama shiryawan" Maimoon tace "Shayi kawai xa mu sha sai mu je mu kirata" Muryar Umma suka ji bakin kofar kitchen din tana kallon Ummi cike da masifa tace "Kin wuce kin cire kayan nan na jikin ki ga lace can na dinka maki ko sai na 6ata maki rai???" Ummi ta kalli atamfar jikinta sannan tace "Lace umma?" Xagi umma ta kunduma mata tace "Don uwarki xo ki fita ki cire kayan nan, ko ubanki ne yayi maki" Ummi ta nufi kofa ta fita, Ammi dai sai aikinta take, Aunty ta tabe baki ita ma ta ci gaba da aikinta, tsaki Umma ta ja ta bar bakin kofar kitchen din, Maimoon ta hada masu shayin cup biyu ta fita, karfe bakwai da kusan rabi Imaan ta taho part din su Maimoon sanye da nata atamfar da well ironed hijab dinta har kasa, sosai tayi kyau Aunty tace "Iyye daughter tayi kyau sosai, amma ko yar powder baxa ki shafa ba Imaan" Yar dariya Imaan tayi ta gaida Aunty, Aunty ta amsa tace "Ki tafi daki ki dau powder Maimoon ki shafa kin ji?" Tana murmushi ta juya ta fita ta wuce sama, dakin su Maimoon ta shiga ta dau powder dinta dake gaban mirror ta shafa, ta goga chappete a lips dinta mai two colour, sosai tayi wani sanyayyen kyau kamar warce tayi wani kwalliya, juyawa tayi ta fita dai dai fitowar Umma dakinta, Sosai gaban Imaan ya fadi ta sunkuyar da kai har xata wuce maganan Sadeeq ya fado mata, a hankali tace "Ina kwana" Umma na mata shegen kallo tace "Kin sa6a gaisheni a gidan nan ne ko kuma gulma da kinibibi irin na uwar ki, to ko da mistake kika sake gaisheni a gidan nan wllh sai na gaura maki mari munafuka kawai sauran ciwo" Ita dai Imaan bata ce komai ba ta dinga sauka stairs, Umma ta bi ta da kallon tsana karara, har wani tafarfasa xuciyarta yake... Imaan na komawa kitchen Aunty tace "Ba gashi kin kara kyau abin ki ba, don kana da kyau kuma baxa ka kara da wanka ba" Imaan dai murmushi kawai tayi, Aunty tace "Kin dai karya koh?" gyada mata kai tayi, Aunty tace "Toh maxa ki tafi suna jiran ki a mota, sai mun xo in sha Allah" Imaan har ta nufi kofa ta juyo ta marairaice tace "Aunty xa ku taho da Inna?" Aunty ta d'an yi dariya tace "Tabb, to ban dai sani ba, amma kila mu taho tare" Ammi dai sai kallonta take ganin yanda ta rame kamar warce tayi ciwo na sati daya, Imaan tayi masu sallama ta fita kitchen din, ta tadda su Maimoon har sun shiga mota suna jiranta, ita ma ta shiga motar aka wuce da su islamiyyar su, Imaan dai sai Muraja'ah take a xuciyarta har suka iso islamiyyar tasu, Da yake islamiyyar sananne ne, kuma duk yawanci yaran masu shi sosai ne a makarantar, manya manyan mutane ba na wasa ba ne suka halacci taron waliman saukan, ciki kuwa har da 'yan gidan Bulasawa gaba daya, da shi kan sa Bulasawan, duk da yaran second wife dinsa kadai ke xuwa islamiyyar wato su Mariya da kanninta banda kannin Sadeeq don su tasu islamiyyar daban, amma hakan bai hana Mahaifiyar Sadeeq xuwa wajen saukan al-qur'anin ba, su Daddy da Abba da kawu Bala da Kanin Inna Audu d'an tsut kamar yanda ta kirasa duk sun xo gun saukan su ma, Sai da dalibai uku suka yi karatu sannan su Aunty da Ammi suka iso wajen, Imaan ta ji dadin ganin Amminta don ita ce seventh xata yi karatu Mariya kuma ta shidda, Maimoon ta goma, Tunda Imaan ta hada ido da Sadeeq dake wajen tare da mahaifinsa gabanta ya fadi bata sake yarda ta kalli direction din da suke ba, lkci daya duk mood dinta gaba daya ya canxa har aka xo kanta a karatun... And Sadeeq couldn't take his eyes off her even for a second, both her tajweed and kira'ah were more than perfect, babu wanda bai mayar da hankali kan karatun da imaan take na Surah Ad-dukhan ba.... Soo maa sha Allah, ta kuma burge kowa na wajen, first 20 Aya ta karanta na suran, Nan take kuma Bulasawa ya rubuta Check na 500 thousand ya mika ma Sadeeq dake kusa da shi yace "For her, she recited very well" Sadeeq ya amsa yana kallon mahaifin nasa, ba Bulasawa kadai ba, mutane biyu a wajen sai da suka ma Imaan kyauta, domin suran da ta karanta is perfectly talking about Islam, and those are who passed all their times playing, smoking, drinking, infact committing all such of sins, idan kuma Allah ya aiko da Dukhan daga sama su nemi gafara su tuba, daga ya dakatar su koma gidan jiya, Sadeeq ya mike ya je ya sami daya daga malamansu dake co-ordinating wajen ya mika masa check din yace "Daga Alhaji Ahmad Bulasawa xuwa ga dalibar ku Fatima Abubakar Imaan" Malamin ya amsa da jin dadi yana masa godiya yace "In sha Allah xai isa gareta" Mujaheed bai iso gun saukan ba sai karfe sha daya tare da Safeenah da ta cakare cikin tsadadden lace sai xuba kamshi take, Umma na ganinta ta dinga washe baki tana mata sannu da xuwa, ta mike daga kujerar da take xaune tace "Xauna ga kujerah Safeenah" Safeenah dake taunar cingam tace "A'a kiyi xaman ki Hajiya ga wani kujera can bari in je in xauna" Mikewa Umma tayi da sauri ta dauko mata kujeran tace "Gashi xauna" Safeenah ta ja kujerar duk da ido hudu da suka yi da Ammi da Aunty dake wajajen a xaune dauke kai tayi ta xauna tana kas kas da cingam, umma taji wani shegen dadi ganin abinda ta masu don sai murmushi take tace "In ji dai gidan lafiya Safeenah?" Safeenah na juya ido tace "Qlau wllh Hajiya" Da yake dalibai 20 ke saukan kafin karfe sha biyu da wani abu na rana duk suka gama karatun, A nan kuma malaman suka yi announcing kyaututtukan da Fatima Abubakar ta samu da wasu daga cikin daliban, tunda Imaan ta ji wai Bulasawa da kansa yayi mata kyautan kudi gabanta ya dinga faduwa, Umma dake wajen kuwa da taji amount din gaba daya hautsinewa cikinta yayi a wajen, ta kasa xaune waje daya sai mutsu mutsu take, Aunty kuwa sai murna take tana sa albarka,
Chapter 160 · 0% Book details