Sashe 100
Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sadeeq yyi murmushi yace "Wani lkcn ai sai ki min kaka..." Inna tace "Toh in sha Allahu kuwa, yanxu ya maganar da muka yi ranan Bukar?" Sadeeq yace "Kaka Abbana baya kasar ne, ina jiran sai ya dawo in sha Allah sai ayi magana" inna tace "Toh da kyau, Allah maido da shi lafiya, ai dama Bulasawa bai fiye xama ba aka ce, baya can baya nan, to abun ka da babban mutum fitattce..." yar dariya kawai Sadeeq yyi, sun fi minti talatin da inna dake ta basa labarin da ya kamata da wanda bai kamata ba, daga karshe ya ajiye mata dubu ashirin yyi mata sallama, xaro ido tayi tace "Kai dai baka gajiya Bukar, wancan ma da ka ban har yau basu kare ba wllh suna can na adana su sbda yaran gidan nan, toh ni dai nagode Allah ya maka albarka, ya kara maka budi" yana murmushi yace "Ameen kaka, nima nagode" inna tace "Toh ka gaida uwarka ka ji, wataran duk xamu san juna idan Allah ya yarda, to ya sunan uwar taka?" Yana murmushi yyi kasa da kai yace "Hajiya Khadijah..." Inna tace "Lahh sunan aminiyata a da kafin ta xama abun gudu, Allah sarki Hadiza ko ana wace duniyar yanxu kuma" Dariya kawai Sadeeq yyi yana kallonta, Inna tace "Allah ya sa mu yi kyakkyawan karshe dai, amma Hadiza bata yi abun kirki ba, ga son abun duniya Allah ya dora mata, wai..." Kofa ya nufa yana nurmushi yace "Sai na sake shigowa kaka" ta mike da sauri tace "Toh Bukar a gaida gida, Allah maka albarka" ya amsa da "Ameen" ya fita, Kalle kalle compound din kawai Sadeeq ke yi bayan ya fito amma har ya kusa gate bai ga alamar Imaan ba gashi wayar ta har sannan a kashe, mota ce ta shigo gidan driver yyi parking, aka bude motar umma ta sakko tare da Hajiya Balaraba suka bude bayan mota suka dinga fiddo manyan ledoji, Gaishesu Sadeeq yyi, Umma ta kallesa ta amsa tana ci gaba da fiddo ledojin, ya wuce su, sai da suka nufi entrance din shiga gida Hajiya Balaraba tace "waye wancan kuma" Umma tace "Kila wajen Yusuf ya xo" Hajiya Balaraba yace "Dama Yusuf na gari, ni na xata bai nan, duk na xo bana ganinsa" Umma ta tabe baki tace "Yana nan, kinsan sa bai fiye faram faram da mutane ba, ko yana gidan ma to idan bai dakinsa yana bangaren fitinanniyar kakarsu" Hajiya Balaraba tace "Shi yasa, amma na fi ganin Mujaheed" Umma tace "ko kwana hudu ba ayi ba aka gama wani case a gidan nan, wai Yusuf ya rasa warce xai fito yace yana so sai yar wajen Aisha" Hajiya Balaraba ta xaro ido tace "Yar wajen Aisha kuma, to sai aka yi yaya?" Umma tayi wani murmushi tace "Ai ba xancen ma yanxu haka, kakarsu dai tace ko bayan ranta bata amince da auren ba, kuma a ranan na shirya na je wani waje aka ce in kwantar da hankalina ba matarsa bace ba ma, wannan dai Hafsar ita ce matarsa kuma wai kwanan nan xa ayi bikin, kila a hada tare da na Mujaheed, tunda gashi har mun kusa gama hada lefen nasa" Hajiya Balaraba tace "Ke ma dai da daukan ma kai, to meye xaki wani damu a kan lamarin d'an kishiyar ki??" Umma tace "Ashe ma baki gama sani na ba kenan duk kusancin mu Balaraba, ni xan so abu mai kyau ya ra6a Aisha da 'yar ta, Yusuf ai abu ne mai matukar kyau, idan ya auri yar wajen Aisha ai ba karamin dace yarinyar tayi ba, ga arxiki ga shi da hankali da natsuwa, toh ina xan yarda, kiri kiri fa kun ga bakin cikin da ta dinga nunawa lkcn bikin Seeyama, babu abinda ta ta6uka da bikin sai dai ta leko ta koma, da aka tashi kai Seeyama ma ita ce karshen tafiya sannan farkon dawowa duk sbda hassada, shine xan yarda abun kirki ya sameta ita ma, inaa ai tunda naji ance min ba matarsa bace hankalina ya kwanta, sai ga kakarsu ma tace samm ba da yawunta ba" Hajiya Balaraba tace "Toh Alhmdllh" Hajiya Balaraba ta shiga jera tulin inner wears din da suka siyo kasuwa a daya daga akwatina takwas dake dakin Umma, Umma tace "Dole ma Mujaheed ya xo ya kara kudi, don wannan da ya rage ba isa xai yi ba don har gwal ina son mu saka a kayan, ko da dankunne da sarka da xobe ne kawai banda awarwaro" Hajiya Balaraba tace "Gaskiya kam, xa ma su fi ganin lefen da mutunci, to shi gogan na duba kayan ma kuwa?" Umma tace "Idan an gama hadawa sai su duba tare da ubansa, in sha Allahu kafin karshen watan nan xa a gama komai, su tafi su kai gaisuwa tare da sadaki da ubansa" Imaan na tsaye kitchen tana wanke plates a sink Ammi ta shigo tace "Kina da card a wayar ki in kira daddy nayi missing calls dinsa, mine is exhausted" Imaan ta juya ta kalleta da farko rasa abinda xata ce mata tayi, can a hankali tace "Ammi wayana baya wajena tun 3 days ago fa" Ammi na kallonta da mamaki tace "Baya wajen ki? To yana ina?" Imaan tace "Yaya ne ya amshe, ni kuma ban tambayesa ba har yau" Ammi ta wani hade rai tace "Wato ke baxa ki ji magana ta a gidan nan ba ko Imaan, ban raba ki da Mujaheed ba?" Imaan tace "Wllh Ammi ni na daina kulasa a gidan nan ki tambayi Inna, idan ma yaje part din inna ni shigewa daki nake ko in taho gida, wllh na daina xaunawa inda yake ma, kuma da ya amshi wayar ni ban tambayesa ba har ynxu, ban ma san wayar kuma ko ya bani" Ammi tace "Toh yayi kyau, xan ji ko shi ya siya maki wayar" Imaan tace "Wai don sbda Sadeeq na kirana fa shine ya karbe" shiru Ammi tayi tana kallonta, can tace "Toh ina ruwansa da kiran Sadeeq din?" Imaan ta bude hannu alamar bata sani ba, Ammi ta juya ta fice daga kitchen din. Da rana Aunty ta shigo parlon su Imaan da sallama, Imaan dake cin abinci parlor tace "Sannu da xuwa Aunty" Aunty tace "Yauwa Imaan, Ammi fa?" Imaan tace "Tana daki" direct bedroom din Ammi Aunty ta wuce, Ammi dake jera kayan guganta a press ta ajiye kayan hannunta tace "Yanxu nake son gamawa inje in maki ban gajiya Hajiya sai kuma ga ki" Aunty tace "Nima ban gajiya na xo maki ai" gaisawa suka yi Aunty ta xauna gefen gadon Ammi tace "Halan daddy ya koma" Ammi tace "Ehh tun jiya ya koma, ya su Maimoon fa, kwana biyu ni ban ga Yusuf ba ko tafiya yyi babu sallama" Anty ta tayi murmushi don har sannan tasan Ammi bata ji abinda Inna ta masa ba tace "Yana nan kuwa, amma next week xai tafi Abuja ina jin, aiki ne fa ya same mu in gaya maki..." Ammi ta xauna tace "Wani aikin kuma?" Aunty tayi yar dariya tace "D'an ki ne yyi min transfer daxu yana son mu fara hada masa lefe" Ammi tace "Yusuf?" Aunty tace "Ehh fa" Ammi tace "Ikon Allah, toh Allah ya bamu iko, Hafsar ce dai?" Aunty tace "Ehh ita" Ammi tayi dariya tace "Allah yayi kenan, kwanaki fa da nake tambayarsa ita ce min yyi shi fa ba ita xai aura ba, nace to wacece sai yace tana nan wataran xa mu santa" Aunty ta d'an yi murmushi tace "Toh dai jiya ce min yyi Hafsah" Ammi tace "Toh Allah yasa albarka, ya kuma sanya alkhairi" Sun d'an taba hira daga karshe Aunty tayi ma Ammi sallama, Ammi ta rakata har balcony tana ce mata sai ta leko ita ma. Tun daga wannan rana imaan ta fara wasar yar buyan gaske da Mujaheed, part din innan ma gaba daya bata son xuwa sai dole shi ma kai mata abinci, tana ajiye mata kuwa ko xaunawa bata yi xata juya ta bar wajen, Kwata kwata ita dai ba ta son ma su hadu, da ta tuna maganganun su Aunty Halima da Rabi'ah sai wani haushin sa ya diran mata, wai yana sonta, kai ta ma san kawai labarin su Anty Halima ne, ta ya yaya xai so ta, yanxu kam Sadeeq ta wayar Ammi yake kiranta dama da taji ring din wayar xata tafi da sauri ta duba ko shi ne, tun Ammi na complain har dai ta gaji ta daina. Yau da daddare Imaan na kwance parlor suna kallo tare da Ammi dake xaune aka danna bell, mikewa tayi ta sa Hijab ta nufi kofar ta bude, ido hudu suka yi da Mujaheed dake tsaye bakin kofar, gabanta ya fadi sosai tayi saurin juyawa ta basa hanya, ya shiga parlon yyi ma Ammi kallo daya ya sunkuyar da kai ya ajiye ledan hannunsa yace "Ina yini" tace "Lafiya lau, ya aiki" Yace "Alhmdllh, dama Abba ne yace in kawo wannan" Ammi tace "Toh Allah amfana" Yace "Ameen, sai da safe" Daga haka ya juya ya nufi kofa ya bude ya fita ya kulle kofar, Ammi ta bude ledan taga gasasshiyar kaza ce babba, duk son imaan da kaza kin ci tayi wai ta koshi, har hakan ya ba Ammi mamaki sosai, Ammi ta debi kadan ta kai sauran fridge ta ajiye. Ana saura few days su yi resuming schl ranan Friday da yamma sadeeq ya kira ta wayar Ammi, Imaan ta dau wayar da ke dakin ta yawanci, bayan sun gaisa yace mata yana waje, xaro ido tayi a hankali tace "Toh" daga haka ya katse wayar, Fitowa tayi daga dakinta gabanta na faduwa ta tafi dakin Ammi ta makale bakin kofa tana kallonta a hankali tace "Ammi ana kirana a waje" Ammi tace "Wa ke kiranki??" sunkuyar da kai tayi ta rasa wa xa tace don tun ranan da ta ambaci sunansa a gaban Ammi Ammi tace mata bata da kunya sunan Mahaifin nata take kira gatsau, to yanxu kam bata san ya xata kirasa ba, Ammi tace "Toh kar ki dade a waje" d'an murmushi tayi tace "Toh Ammi" daga haka ta fita dakin, as usual Hijab dinta har kasa ta saka ta fito,