← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 181 OF 292

Sashe 181

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

sai kuma ya kalli Sadeeq yace "Is she a sickled cell patient?" A hankali Sadeeq ya girgixa masa kai yace "She is only carrying the trait" Likitan yace "Wani drugs kike sha a gida?" Cike da karfin hali tace "Suna da yawa" likitan yace "Did you know their names?" Sadeeq yace "I will get drugs for her now, amma ayi mata allura" daga haka ya juya ya fita ward din. Aunty ce ta sakko parlor sanye da hijab hannunta rike da purse, ta kalli Mujaheed tana amsa gaisuwar da yake mata a parlorn sannan ta kalli Umma tace "Xan fita sai na dawo Hajiya" Umma tace "Ina kuma xa ki da magariba" Aunty tace "Xan je dubiya asibiti ne" da mamaki Umma tace "Waye ba lafiya?" Aunty tace "Baki san su ba" Dai dai nan Abba ya shigo parlon yana kallon Aunty yace "Ba ku tafi ba kenan" Aunty tace "Ehh yanxu xa mu fita" Abba yace "Xuwa anjima idan anyi isha xan leka asibitin" Umma na kallon Abba tace "Wai waye ba lafiya" Abba ya kalli Aunty yace "Bata sani ba ne dama?" Aunty bata tanka sa ba ta nufi kofa, Abba ya girgixa kai yace "Imaan ce suka je duba kanwar yaron nan dake nemanta a asibiti shine Asthma dinta ya tashi, ita ma dai tana asibitin yanxu" Kallonsa kawai Mujaheed yake ko kiftawa babu, Umma ta saki salati tana tafe hannu tace "Shine ake boye min, shi ciwon Amina ke boye min fisabilillahi? Meye amfanin xaman munafurci Alhaji, wato ita ta ji xata tafi dubata a asibitin ni kuma sai uwar yarinyar da Inna su kullace ni su xata naji xuwa ne bana son yi, toh xuciyata bai kai haka lalacewa ba, kuma nima yanxu xan shirya mu tafi, sai dai ita ta ji kunya, ban taba ganin munafuka irin Amina ba wllh, duk ita ke hada ni da Aisha na lura" Shi dai Abba ko tanka ta bai yi ba ya wuce parlon sa, Umma ta wuce sama da sauri don dauko hijab, Mikewa Mujaheed yyi ya fita parlon ya bi bayan Aunty, tare ya gansu suna tahowa da Ammi dake sanye da hijab ita ma, yana tsaye har suka iso, ya gaida Ammi ta amsa tana tambayarsa ya aiki, yace "Alhmdllh, ya mai jiki" Ammi tace "Toh da sauki" a hankali yace "Toh mu je in ajiye ku" Aunty tace "Toh ka kyauta" dai dai nan Umma ya fito parlon sanye da hijab ita ma, tana kallon Aunty tace "Toh Amina xuciyata bata kai inda kike tunani ba lalacewa, rashin lafiya Kuma da ke kan kowa kike boye min fisabilillahi??" Aunty ko kallonta bata yi ba ta nufi gate, Ammi dai bata ce komai ba ita ma tafiyar take, Umma tace "Munafurci dai bashi da amfani a rayuwa, kuma tare kika shigo gidan nan kika ganmu da Aisha" daga haka ta kalli Mujaheed tace "Kai xaka kai mu ne" ba tare da ya kalleta ba yace "Ehh" har suka shiga motar tasa babu wanda yace komai, Aunty ta gaya masa asibitin bayan sun hau saman titi. Maimoon ce ta fito ta kai su har ward din da imaan take, Mummy na xaune saman kujera kusa da gadon da imaan take kwance tana bacci, sai kannin Sadeeq biyu da kanwarta da Mariya, Su Aunty na shiga ward din Mummy ta fara welcoming din su, a ka shiga gaisawa fara'a, Umma dai sai kallon Mummy take, Mummy tace "Jikin ma da sauki sosai, kawai drip din ne da bai kare ba, don sunce biyu ne" Aunty tace "Toh Alhmdllh, Allah ya sauwake, ku kuma Allah ya bada lada" Mummy tayi murmushi tace "Toh Ameen, Allah ya bata lafiya" Mujaheed dai na tsaye daga bakin kofa yana kallon Imaan dake bacci tana sauke numfashi a hankali, da sallama Sadeeq ya shigo ward din....
Chapter 181 · 0% Book details