Sashe 84
Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
jira cewar Muhsin ba ya mayar da glass dinsa ya bude motar ya fita, sanye yake da kananun kaya da suka yi matukar amsan jikinsa, Muhsin ya fito motar yana kallonsa yace "Ehh lallai Abokina ya xurma da yawa" Sadeeq dai bai tanka sa ba ya gama danne danne wayarsa ya kai kunne, bayan wani lkci yyi kasa da murya yace "Abba gani a waje" Abba dake xaune parlonsa tare da Daddy yace "To madallah bari they will lead you in now" Ba a dau lkci ba Yusuf ya fito kofar gidan, Kallon Sadeeq ya dinga yi har ya isa inda suke, suka gaisa Muhsin yace "Ashe dai Engnr kana gari?" Yusuf yyi murmushi yace "Sure ina nan, ya aiki" Muhsin yace "Alhmdllh" Yusuf ya shiga da su compound din har xuwa parlon Abba, Sadeeq na shiga parlon ya cire glass yyi kasa da kai har xai xauna saman kujera sai kuma ya fasa ya xauna kasan rug ganin nan Muhsin ma ya xauna, har sannan bai dago kansa ba ya gaida su Abba da Daddy, duk suka amsa suna masa sannu da xuwa, Daddy yace "Muhsin abokin ka ne dama kenan" Muhsin yace "Ehh Abba abokina ne" Daddy ya gyada kai yace "That's good" Abba ya kalli Yusuf da ya xauna yace "Where is M.A?" Bude kofar parlon aka yi sai ga Mujaheed ya shigo parlon da sallama can ciki, kansa a kasa ya xauna kusa da Yusuf sannan ya kalli Sadeeq da idanuwansa ke kan TV, gaisawa yayi da Muhsin, sai a sannan Sadeeq ya kallesa yace "Barka da yamma" Mujaheed yace "Same to you" Abba na kallon Sadeeq yace "Can I know you plss son" Sadeeq ya sauke idonsa kasa yace "Sunana Abubakar Sadeeq Ahmad, ni haifaffen garin Kaduna ne, mahaifina asalinsa d'an kano ne, na gama karatu na and I am working as a medical practitioner now" Abba yace "Maa sha Allah, a wani anguwar ku ke?" Yace "GRA muke" Abba yace "Ohk can i know ur dad?" Sadeeq ya d'an yi Shiru kafin yace "Alhaji Ahmad sunansa, d'an kasuwa ne Abbana, yana kuma xaune nan Kaduna" Abba ya gyada kai cike da gamsuwa, bayan few seconds yace "What is ur intention toward my daughter Abubakar?" Sadeeq ya kasa dago kansa, Daga Mujaheed har Yusuf kallonsa kawai suke, can ya dago kansa a hankali yace "Abba sonta nake da aure...." Mikewa Yusuf yyi yana kallon Abban nasa yace "I want to excuse my self plss..." Abba ya gyada masa kai ya juya ya fita parlon, Abba yace "Toh naji dadin jin hakan daga gare ka Abubakar amma kasan ajin da Imaan take yanxu?" Ya gyada kai a hankali yace "Na sani Abba" Abba yace "Ohk good, wani xancen kuka yi da kakarta last time da ka xo?" Murmushi yyi ya sunkuyar da kansa, Abba yace "Yes go on" Yace "Abba ce min tayi idan tayi magana da ku xata sanar min in turo magabatana" Abba yace "Ohk, kai d'an wajen Ahmad Bulasawa ne?" Sadeeq ya gyada kai kawai, Abba yace "To yayi kyau, yanxu dai I want to ask for a favor from you Sadeeq" Sadeeq ya daga kai a hankali yana kallonsa, Abba yace "But before then bari in maka wannan alkawarin, Sadeeq in dai Imaan ta amince tana son aurenka, wato ta yarda da kai, sannan iya binciken da xanyi idan ban ga wani flaws dinka mara kyau ba ni nayi maka alkawarin xan baka Imaan in sha Allah, yea it's a promise I am making" mikewa Mujaheed yyi yana kallon Abba yace "Abba I want to pick a call" bai jira cewar Abba ba ya fita, Sadeeq dake kallon Abba yace "Toh nagode Abba" Abba yace "Toh favor da nake son ka min ynxu shine.... Kakarta nake son ka samu amma ba yau ba, but cikin satin nan, sai ka ce mata mahaifin ka bai kasar yanxu kuma xai dau lkci kafin ya dawo, yana dawowa kuwa xaka sanar masa xancen auren... Am doing this to allow my daughter finish her secondary schl, wato na da shekara daya, kasan yanda tsoffin nan suke, there is nothing da xan gaya mata da xata fahimce ni, amma kai idan kace mata haka to an gama komai, kaga ko da tana gamawa ne sai ayi magana amma yanxu kam I don't think xan iya bada ta tana ss2, that aside.... my promise of giving u my daughter's hand in marriage will count only on one condition ko da ta gama secondary schl, the condition is that xaka yarda ko bayan kun yi aure ta ci gaba da karatu a dakinta" Sadeeq ya d'an yi murmushi yace "In sha Allah Abba" Abba yace "Toh Allah ya mana xabi mafi alkhairi" Sadeeq yace "Ameen Abba na gode sosai, Allah ya kara girma" Abba yace "Allah maka albarka" daga haka Abba yace masa xai iya tafiya, nan suka yi sallama da Daddy da Abban sannan suka fita parlon. Muhsin na kallonsa yace "Mu je in gaida Mum dita" Sadeeq ya xaro ido yace "No kai dai kaje zan jira ka a waje" Muhsin yyi dariya yace "Common Mum dita fa na ce maka..." Da kyar ya ja Sadeeq suka nufi part din su imaan, Bell Muhsin ya danna, Ammi na kitchen xata fito Imaan ta bude kofar dakin ta, Wani kallo Ammi tayi mata tace "Kika san waye bakin kofar xa ki tafi a haka?" Imaan ta xaro ido ta juya ta koma ta dau Hijab dinta ta sa ta fito ta nufi kofar, bude kofar tayi, lkci daya tayi still tana kallon Sadeeq, Muhsin yace "Toh ko mu bi ta kanki" da sauri ta juya ta bar wajen, kafin su shiga parlon har ta koma dakin ta ta kulle, Dariya Muhsin yyi ya xauna, Sadeeq that was uncomfortable shi ma ya xauna, Ammi ta fito kitchen ganin Muhsin tace "Ka shigo anguwar kenan" yayi dariya yace "Ammi takanas nan fa na xo wllh" tace "Keep quiet kai din" yace "Ki tambayi abokina Ammi" Ammi ta karasa shiga cikin parlon tana murmushi tace "Toh sannun ku da xuwa" Muhsin ya gaidata, tun da Sadeeq ya kalleta sau daya bai sake yarda ya kalleta ba shi ma ya gaisheta, ta amsa da fara'a tana masu sannu da xuwa, Muhsin yace "Kawai ce masa nayi ya rakani in gaida Mum dita" Ammi tace "Toh kun kyauta kuwa nagode, sai dai abokin naka kamar d'an uwan mu ne Bafillatani" Dariya kawai Muhsin yake, Sadeeq dai yyi murmushi bai dago ba, Ammi ta tambayi Muhsin yayanta sannan ta tambayi Sadeeq iyayensa, Sadeeq yace "Duk suna lafiya lau" Ammi na kallon kofar dakin Imaan tace "Imaan" Muhsin yace "Kawai daga gani na shine ta shige daki saboda bata da gaskiya bata gaida mutane ko a waya" Dariya Ammi tayi tace "Ae ban san yanda xanyi da ita ba, ko nace tayi sai tace ta manta" Sai da Ammi ta kara kiranta ta fito da kyar, wannan karan Hijab har kasa ta sa, Ammi tace "Baxa ki gaida yayanki ba kika shige daki?" Bata yarda ta daga kanta ba har ta iso cikin parlon kamar munafuka ta xauna kasa kusa da kujera tace "Ina yini Ya Muhsin?" Yana murmushi yace "Lafiya lau Imaan, ya gida?" Tace "Lafiya lau" ta saci kallon sadeeq da yaki kallon inda take tace "Ina yini" yace "Lafiya lau" Ammi tace "Ki dauko masu ruwa fridge" mikewa tayi ta wuce kitchen, Ammi tace "Jiya mun yi waya da yaya yace gobe xai dawo" Muhsin yace "In sha Allah, haka yace min" Imaan ta shigo cikin parlon ta durkusa ta ajiye tray din ruwa da lemon five alive sai glass cups biyu, Ammi tace "Na gama girki bari in xubo maku" Muhsin yace "A'a ki bar shi kawai Ammi a koshe mu ke..." Ammi tace "Idan kai baxa ka ci ba sai abokin naka ya ci, ya sunansa ma dai?" Dariya Muhsin yyi yace "Sunan Daddy garesa" Ammi tayi murmushi tace "Ikon Allah, mai gida ne ashe" Muhsin ya kasa daina dariya, Imaan na ajiye drinks din dama ta shige daki ta kulle kofa, Ammi na shiga kitchen Sadeeq yyi kasa da murya yace "Don Allah ka rufa min asiri mu wuce Muhsin" ko kallonsa Muhsin bai yi ba ya mike ya bi bayan Ammi kitchen, har ta fara xuba masu abincin a plate yace "Ammi kinsan waye muke tare da kuwa?" Ammi ta juya tana kallonsa tace "A'a, waye?" Kasa daina dariya yyi yace "Wllh surkin ki ne, saurayin Imaan" Ammi ta saki serving spoon din hannunta tana kallon Muhsin baki sake tace "Amma baka da kirki Muhsin shine ka bar ni ina ta xuba a parlor?" Dariya kawai Muhsin yake, Ammi tace "Ni dai ba ka kyauta min ba, haba naga yaro ya ki sakin jiki, ita kuma Imaan sai na ci mutuncin ta..." Da sauri ya dakatar da ita yace "Wllh bata sani ba, baki ga ita ma duk ta ki sakin jiki ba" Ammi tace "Ni dai ka cuce ni, har kasa naje ina ce masa mai gida" Shi dai bai fasa mata dariya ba, ta gama xuba abincin tace "Ai sai ka daukar maku, ni kam na wuce daki" bata kara sauraransa ba ta fita kitchen din ta wuce bedroom dinta, Muhsin ya ci abincinsa ya koshi, Sadeeq kam ruwa kawai ya sha ya mike yace "I am waiting for you outside" duk yanda Muhsin ya so tsayar da shi kin saurarensa yayi har ya fita, nan Muhsin ya kira Ammi a waya yace "Toh ya dai fita Ammi ki fito mu yi sallama" Ammi ta fito parlon tace "Bai ci abincin ba kenan" Muhsin yace "Ae baxai ci ba, Ammi Abbansu Mujaheed ne fa ya kirasa yana nemansa shine muka taho tare" Ammi tayi shiru tana kallonsa da mamaki, can tace "Toh ya aka yi da ku ka je?" Muhsin yace "Ba wani matsala wllh, Ai nasan daddy xai maki bayanin komai idan ya shigo, yanxu dai xan wuce kinga yana can waje yana jirana" Ammi tace "Toh shikenan ka gaida Hajiya da Hajjo" Yace "In sha, kice ma Imaan ta fito mu dai mun wuce" daga haka ya fita parlon yana murmushi, a can kofar gida ya tadda Sadeeq xaune cikin mota yana jiransa, Muhsin