Sashe 214
Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
so na 'yan uwantaka unlike Yusuf da ya nuna interest a kanta da farko, Barrister what if mun shiga hakkinsa shi Mujaheed din?? Wani irin xama kake ga xa su yi baya sonta ita ma kuma haka?" Murmushi Abba yyi yace "Ae shi yasa nake ta neman sa ta waya domin ya xo ya datse auren amma ban samesa ba, yanxu haka daga gidansa nake baya nan, but in sha Allahu kar ka damu xa a raba auren" Daddy yace "It's not a matter of a saketa or not barrister, in har shi yayi na'am da auren shikenan, sai kuma mu san yanda xa mu yi da Inna, Imaan kuma I am hoping she learn to live with him as husband in sha Allah, Rukayya da Aisha kuma I don't think xa su iya saka xumuncin mu ya sa mu tangarda, in har Mujaheed yayi na'am da auren kuma Inna ta hakura shkkn Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi gare su gaba daya, I think you don't need to add anything to what I just said now barrister mu bar xancen haka...." Daga haka Daddy ya kira waitress don ta kawo masu abinci coz it's almost Asr. Tun da Safeenah ta farfado take bin duk mutanen dake xagaye kanta da kallo kamar me son tuna abinda ya faru, lkci daya ta mike a xubure kamar warce aka tsikara ta fasa wani ihu tace "Shi mijin nawa aka aura ma Imaan, innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku Hajiya Rukayya ta kai ni ta baro ta cuce ni, ta cuce ni, ta cuce ni, mijina ne ya auri Imaan daga karshe, wayyo na shiga uku...." Da gudu Inna ta karaso wajen ta Rasulu na biye da ita ta dalilin labari da aka je aka basu a bangaren ta wai Safeenah ta suma a tsakar gida, Inna na kallon Safeenah tace "Mu ma duk haka muka ji da aka mana kishiya Safara'u, sai dai duk na ki ya fi ciwo ke da kika tika rawa a bikin kishiya jiya, yau kuma tun safe kike ta yanke yanken kabeji da salak......" Safeenah ta fashe da matsanancin kuka tana jijjiga kanta kmr tababbiya tace "Wllh wllh baxan xauna da kishiya ba kishiyar ma Imaan, don ni kadai aka yi Mujaheed a duniya, don ni kadai aka yi sa, sai na nuna ma Rukayya ba ni ta yaudara ba, baxan fallasa ta ba yanxu sai ta fara sanin su waye family dinmu, sai ta san an aura ma Mujaheed Imaan ne saboda mugun halinta da bakin halinta wllh idan ban nakada ma Rukayya duka ba ban Haifu cikin Mansura ba....." Gate Safeenah ta nufa da gudu kamar mahaukaciya tana rusa kuka tana kiran mummyn ta, Inna ta bi ta da kallo da sauran mutanen wajen da suka bude baki da shock, Inna tayi wani dariya irin ta boss tace "Toh wllh babu tsinannen da ya isa ya raba auren nan da raina, auren nan mutu ka raba takalmin kaza, maxa a tafi a kwaso kayan da aka kai gidan barayi a fito da kayan Safara'u a feshe dakin a xuba na jikata, dama idan ba shi Mujaheed din ba waye ya dace da Imaan banda toshewar basirar mutane? Dama can hange hangen Imaan da kwadayin abun duniya yasa ta hango xuri'ar shegu barayi suka kuma yaudareta suka gudu, ni fa tun ba yau ba nake tunanin hada auren jikokin nan nawa biyu kawai dai Allah bai bani basiran yin magana bane amma yanxu kam faduwa ta xo daidai da xama bbu shegen da ya isa ya raba auren nan, ko shi Mujaheed din yyi yunkurin sakin Imaan ni sai in iya tsine masa ya bi duniya" tana gama fadin haka ta nufi part dinta tana cewa "Ku kira min Ahmadu da Bukar na canxa shawara gaskiya, wnn ai abun arxiki suka hada...." Sai kusan Magrib Umma ta dawo gida duk tayi xuru xuru tun safe banda ruwan shayi babu abinda ta xuba a cikinta, xuwa lkcn duk an watse a gidan sai yan uwa na jiki da suka rage, tana shiga dakinta ta dau wayarta don kiran Mujaheed taga missed calls din Hajiyan Marafa yyi goma sosai gabanta yyi mugun faduwa ta dinga kallon wayar, ta xauna gefen gado, Ummi ta biyota daki tace "Umma Hajiya Baturiya yayar Aunty Safeenah fa ta xo har sau uku daxu..." Umma ta hadiye abu da ya makale makogwaronta da kyar ta hade rai tace "Toh sai aka yi Yaya? Neman me suke min?" Ummi tace "Nima ban sani ba" Umma tace "Toh fita waya xan yi" Ummi na fita dakin Umma tayi dialing number Mujaheed ta ji sa a kashe, mikewa tayi hankali tashe tace "Me Mujaheed ke nufi da kashe wayarsa ne??" Hijab ta kuma sakawa ta fita gidan don xuwa gidan Mujaheed ta iskesa. Tsaye ta ga Inna tsakar gida kusa da apartment din su Ammi inda take shiga ba nan take fita ba, Aunty da Mama Hadiza sai Mama Hansai da few relatives na tsaye dai suna kallonta, rai bace ta ci gaba da cewa "Wllh idan bata yi hankali ba sai ince kar ta sake dawowa gidan nan ta sha xamanta gidansu, kuma a kai ni yanxun nan in dauko jikata ai ba uban wani yyi mata ciki ta haifeta ba, ta dauwama a gidansu kar ta sake dawowa gidan d'a na, mata kawai sai bakar xuciya, Bukar dai ya auri jaraba don Aisha jaraba ce wllh, shi jikan nawa take nuna ma k'i haka ba kunya ba tsoron Allah bata jin kunyata ba balle na ubansa sannan Bukar, shi Mujaheed din ne bata so sbda rashin tsoron Allah kamar wani barawo?? to kuwa har Bukar bata so tunda bata son d'an d'an uwansa, kawai ni dai Allah ya hada 'ya yana da fitinannun mata a duniya... Maxa a kai ni gidansu in dauko jikata yanxun nan" tana fadin haka ta tafi dauko Hijab, Daddy da Abba da shigowarsu gidan kenan su ma suka tsaya from afar suna kallon mahaifiyar tasu.