← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 187 OF 292

Sashe 187

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

ba ruwana, shi kuma Mujaheed gaskiya sai mun tashi tsaye kansa don idan aka rasa sa ni nayi asara ba wani ba, idan ma auren ne bai so gaskiya sai a raba yau yau din nan, ba ruwana a kai ni a baro in shiga uku" Sai a sannan Abba ya kalleta yace "Xaxxabi fa kawai yake, amma ai yana jin sauki yanxu..." Tsaki Inna ta ja tace "Tunda ba jikin ka bane ba dole kace yana jin sauki ba Ahmadu, gansamemen mutumi da ya dinga min rawan sanyi jiya sai da na rufa sa da katon bargo shine xaka ce yana jin sauki, ku dai ku dinga jin tsoron Allah, wlh ku ji tsoron Allah, tunda ba wani ya min wahala da shi ba to ni xan je yanxu inji abinda yake ciki, idan ma matar ce mayya duk xan gani" Da mamaki Abba yace "Subhanallah, haba Inna ya kike irin wannan magana haka, wannan fa babban magana ne ka ce ma mutum maye...." A fusace Inna tace "Na ce mata mayyar, idan ba mayyar bace ina dawowa ai xan ce ba mayya bace, tsoron ubanwa aka ce maka xan ji banda Allah, shi kadai ne abun tsoro dama, kuma ni da shi nayi imaani" dai dai shigowar imaan parlon, kanta a kasa ta gaida Abba, Abba ya amsa yana tambayarta jiki domin jiya yini tayi ciwon kafa, Inna tace "Ya jiki?? Ce maka aka yi bata da lafiya, Ga dai bawan Allah me ciwo can a kwance xaka tambayi lafiyayyar mata ya jiki" tana fadin haka ta tabe baki ta mike tace "Toh yanxu xa ka kirasu ka sanar masu d'an ka na fari ba lafiya a bar kawo lefen da kudin aure sai wani satin koko?" Da sauri Imaan ta kalleta, Abba yace "Haba Inna, ae wannan bai shafi ciwon Mujaheed ba, Ina ruwansu da wannan, shi Mujaheed din yaro ne, don Allah ki yi hakuri ki bar xancen nan Inna bai ma kamata ba, ga yanda dai muka yi da mutane kuma ki kawo wata magana daban" Inna tace "Atoh ni dai duk abinda ya sami jikana Allah ya isa wllh...." Daga haka ta fice daga parlon a fusace, Imaan tace "Abba sai mun dawo" ya gyada mata kai kawai ta bi bayan Inna, har suka isa titi Inna bala'i take idan abu ya sami Mujaheed ya sami kowa, ita dai Imaan sai turo baki take tana tsaye gefenta, Inna ta tsayar da adaidaita ta shige yana tambayarta inda xata a fusace tace "Don Allah ka rufa min asiri yaro ka ja mashin dinka mu je, meye kuma Ina xanje kamar yar yarinya, jikana ne fa ba lafiya rai a hannun Allah gidansa na can unguwar dosa ana ma kyautata xaton matar ce mayya, kuma kana ta cewa ina xan je" Mai adaidaitan bai tanka ta ba, Imaan ta hade rai ta shige adaidaitan. Har suka isa gidan Mujaheed mita take ita kadai daga imaan har mai napep babu mai ce mata komai, suna sauka kafin ta fiddo hamsin ta mika masa Imaan ta basa dari biyar din hannunta don bata ma son dogon xance, ya ciro dari biyu ya mika mata, Inna ta saki salati tace "Nawa ka cire bawan Allah?" Imaan tace "Toh ai ba kudin ki bane Inna, kayi wucewan ka kawai" Mai adaidaitan ya ja napep dinsa yyi gaba Inna ta dinga jaraba tana kiransa barawo tuni imaan ta shige cikin gidan ta bar ta tsaye a bakin gate, dai dai balcony ta tsaya ta rungume hannu tana jiran shigowarta, Can sai ga ta ta shigo compound din tana cewa "Babu abinda kudin Bukar xai masa a rayuwar nan ta duniya, iyaka ma ya gudu ne da wahala da Bala'i tunda bamu basa ba" bata ko kalli Imaan ba ta murda kofar parlon ta bude ta shiga, Imaan ta turo baki ta bi bayanta, Umma ce ta leko daga kitchen tana soya kwai da dankali, Inna ta rike ha6a tana kallonta a hankali tace "Wacece wannan?" Umma dake sanye da hijab har kasa ta gaisheta a dakile ta koma kitchen din, Safeenah ce ta sakko parlor sanye da doguwar riga na material hannunta rike da tray na cup, ganin Inna ta dauke kai ta hade rai hade da tabe baki tace "Sannu da xuwa" Inna tace "Ina Mujaheed din???" Safeenah tace "Yana sama an sa masa drip" Inna tace "Ai ni na shiga uku, abun har ya kai an fara sa drif... Toh aniyar kowa xai bi sa wllh babu abinda xai sami jikana" Kallon Imaan tayi tace "Ke mu je in gansa..." Imaan ta nufeta, da sauri Safeenah tace "Inna a can dakinsa yake fa...." Inna ta juya tana kallonta tace "Dakinsa kuma? Toh da ina nace maki xan je banda dakin nasa? Ko nace maki dakin ki xan shiga Safara'u?" Safeenah tace "A'a da naji kince ku tafi, idan ma tafiyar ne ke da kike matsayin kakarsa ai sai ki tafi dakin" Inna ta gyara tsayuwa tace "Toh ita Imaan din fa??" Safeenah ta d'an hade rai tace "Wannan ba hurumin ta bane gaskiya shiga dakin mijina, bata da wannan hurumin, dakinsa sirrina ne da nashi" Salati Inna ta xabga ta xauna kan kujera tayi tagumi tace "Naga abinda ya isheni ni Asabe... Safara'u kinsan me kike cewa kuwa, wani sirrin ku ke da shi ke da Mujaheed da ba mu sani ba, kinsan wacece kike kokarin hana shiga dakin nasa kuwa???" Umma ta fito kitchen bbu yabo bbu fallasa tace "A'a inna, xancen gaskiya ayi ta, dakinta ne da na mijinta fa kuma kice wata daban ta shigar masu, a kan wani dalilin?? sai kace dai a garin ga6a ga6a muka taso, ko a musulunce ai hakan haramun ne ma wata ta shigar maki turakan miji..."
Chapter 187 · 0% Book details