← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 236 OF 292

Sashe 236

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

nan mun hadu da ita xan shigo ita xata fita, wllh duk a birkice take, sai naga ma kamar hadin bauta tayi" Inna ta gyada kai tana wani murmushi tace "Toh Alhmdllh da wnn magana ya fito fili, amma kinsan wani abu? Wllh yanxu a idon Ahmadu, Bukar da Hadiza bbu me tada fitina a gidan nan sai ni, nice dai fitinanniya gantalalliya" Ta Rasulu tace "Ke ma xai wllh ai wannan magana barinsa xa mu yi a ciki mu yi ta kallon ikon Allah, iyaka a tashi tsaye sosai da nema ma yarinyar nan Imaan tsari...." Inna tace "Ke da kika san komai, ai bbu wanda xai fara gwaleni a kan xancen nan sai Bukar, shi Ahmadu dama baxai ce komai ba amma ni nasan kallon jarababbiya yake min baxai dai yi magana ba, ita kuma wannan mata Hadiza sai dai ta xuba min idanu, a takaice dai Bukar ce min xai yi in daina haka shi ba ruwansa, to ya xan masu Ta Rasulu? To wllh tunda Rukayya ta ma jikata haka sbda bakin ciki da hassada tata ta kare duniyar nan gaba daya, kuma kwanaki kadan ya rage mata gidan d'a na wllh, ke dai kawai ki xuba min ido ni kadai na isheta sai ta gwammace kida da karatu, aure jikokina kuma mutu ka raba, ni nasan da tasan auren xai dawo kan Mujaheed da bata san yanda tayi ta hana ba, kuma mutuwa xata yi a banxa idan tace xata raba auren nan...." Ta Rasulu tace "Atoh, kuma fa har yanxun ba wai saduda tayi ba, ance min tana nan tana kokarin raba auren nan, da kyar fitan da tayi yanxu ba gun bokanta xata ba, wllh sai mun tashi tsaye an yi kokarin nisantar da Imaan sosai daga sharrinta, in sha Allahu in dai da ran mu sai ta fito da bakinta tana tona kanta, kada ki kuskura ko da wasa ki gaya ma ko Hadiza tunda lalacewa ta sami yaran naki, mu dai da muka san komai sai mu yi ta kan mu" Inna tace "Dama ba gantalallen da xan gaya ma, iyakata da su su ban kudi in rufa ma jikata asiri, sannan in sha Allahu a gaban Bukar asirin Rukayya xai tonu shi da baya ta6a ganin laifinta..." Ta Rasulu tace "Toh ynxu ya isilin bawan Allahn nan Bulasawa?" Inna ta marairaice kamar xata yi tace "Wai daxu aka sallamesu asibiti inji Ahmadu, ni dai xan shirya in siya lemo ko kwaya biyar inje har gida in duba sa wllh, dama can Imaan ba matarsa bace bani da rabon cin kaji da xabi dai" tana magana tana matsar kwalla, Ta Rasulu tace "Kya ci da kudin ki" cikin rawar murya Inna tace "A'a ki bari Ta Rasulu, wani hanin ga Allah baiwa ne, kuma ni da Bulasawa mutu ka raba har gidansa xan dinga xuwa kai masa xiyara...." Daddy ne tsaye jikin motarsa kofar gidansu Ammi, ya fi minti goma yana jiran fitowarta, jin an bude gate ya daga kai har ta fito, ta gaishesa, yana kallonta yace "Ban san ki da haka ba Aysha, wannan ba halin ki bane, why are u behaving this way pls?" Bata tanka sa ba, yace "Ko ba don ni ba don barrister ya kamata ki hakura haka nan, kar ki manta jininsa fa ya aura ma Imaan, sannan don't forget yayana ne shi din, jinin nasa kuma d'a na ne, beside all this Aysha Mujaheed bai yi deserving haka daga gare ki ba, wai kin mance wanene Mujaheed ne?" Ammi da hawaye ya kawo idonta ta girgiza kai tace "I am thinking of my daughters future, ban san rayuwar da xata yi tare da kishiya da uwar miji warce bata sonta duk da kai ba yarda da rashin son da take mata kake ba, kila sai ranan da xaka gani a xahiri, nasan abinda imaan xata iya jurewa da wanda baxata jure ba, this is too much for her, ga condition dinta...." Daddy ya sauke ajiyar xuciya yace "Baki yarda da kaddara ba kenan, Haba Aysha sai kace ba musulma ba, where is ur faith? All you need to do is wish ur daughter a peaceful and better married life, plss ki shiga kiyi ma gwaggwo sallama we are going home now" Girgixa masa kai tayi tace "No ka tafi gobe in sha Allah xan dawo" yace "Sure?" Tace "In sha Allah" yace "Toh Allah ya kai mu, we will talk later on phone" daga haka yyi mata sallama ya shiga mota ita kuma ta wuce ciki. Mummyn Sadeeq ce xaune makeken parlonta tare da aminiyarta Hajiya Batula, Hajiya Batula tace "To ke wa kike tunanin xai aikata hakan Hajiya" mahaifiyar Sadeeq Hajiya Khadijah, tayi murmushin karfin hali tana gyada kai tace "Ni nasan wacece ita tunda aka ce daga family din yarinyar take, sarai nasan wacece, kuma Billahil azeem xata san ita ce silan heartbreak din d'a na" mikewa tayi ta nufi window fuskarta a murtuke, da mamaki Hajiya Batula tace "Ba shakka, amma koma wacece ita din gaskiya ta xama abar tausayi yanxu, ta rasa wanda xata ma asiri sai Abba? Don me bata bar asirin iya 'yar su ba kadai, Wannan shine biggest mistake of her life, don da ta sani da bata fara ba" Mummy dai murmushi kawai take, aka bude kofar dakin duk suka juya, Sadeeq ne ya shigo dakin, Uwarsa ta dinga kallonsa don ba karamin rama yyi ba, yyi kasa da kai ya gaida aminiyar mum din tasa cikin sanyin murya sannan ya xauna saman kujera yace "Mummy, Ina son xan tafi Uk...." Katse sa tayi tace "Kaje kayi me a UK Sadeeq?" A hankali yace "I need rest Mum..." Shiru tayi tana kallonsa, lkci daya hawaye ya kawo idonta ta dauke kai tana kallon waje ta window.... Mikewa xaune Mujaheed yyi jin ringing din wayarsa, ya dauka yana kallon Screen din, Call din Umma ya gani, ya ji gabansa ya fadi sosai, yyi ta kallon screen din har ya katse, ta sake kira, kasa kin dagawa yyi, ya daga a hankali ya kai kunne yyi shiru, ko sallama babu tace "Mujaheed??" Yyi kasa da murya yace "Na'am, Ina yini Umma" Tace "Kana Ina ne?" Ya d'an yi shiru sannan yace "Ina gida" tace "Wani gidan?" Nan ma yyi shiru, cikin tsawan da ya ji har tsakiyar kansa tace "Baxa ka bani amsa ba ina tambayarka?" A hankali yace "Gidana Umma" strictly tace "Wani gidan naka a ciki?" Yace "Zaria" Tace "Toh" tana fadin haka ta katse wayar kitt, ya dinga kallon phone din xuciyarsa na bugawa, Imaan dai na xaune kan darduma har lkcn ta gama jujjuya shinkafar takeaway din gabanta ta bar sa, kazar ma tunda ya kamata tana ci ta ki ci kuma, sauka yyi saman gadon ya tafi ya bude kofar dakin ya fita, Safeenah na xaune parlor tana waya da Hajiyar su, murya can kasa tace "Haukatar da ita kuma Mummy, A'a gaskiya... idan aka yi haka ai bata kwashi takaicin da ya kamata ba, a dai yi wani abun daban Mummy" Safeenah tayi shiru tana sauraron uwar tata, sai kuma tace "Mummy na fa ce maki babu auren nan wllh, tunda muka xo bai ce min komai a kai ba, sun raba da suka ga bai so...." jin taku a stairs ta katse wayar da sauri, ta gyara xama ta wani hade rai tana kallon tv dake aiki, Mujaheed ya shigo parlon yana kallon ledan abincin da bata ta6a ba ya dauka yace "Ain't you eating?" yi tayi kamar bata ji sa ba, ya tafi kitchen ya wanko plate ya dawo parlon, ido hudu yayi da Imaan dake sakkowa stairs a hankali tana kallon Safeenah dake xaune idonta a kan tv har lkcn....
Chapter 236 · 0% Book details