← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 291 OF 292

Sashe 291

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

take tana murmushi don hatta muryarsa kamar Mujaheed dinta yana karami, tana rike da hannunsa ta nufi kofa jin horn din mota a compound tace "Kiyi sauri tunda ya fara horn Imaan" fesa turare Imaan tayi ta gyara fuskarta sama sama ta bi bayan Umma da sauri, Mujaheed dake xaune mota rungume da little sister din Musaddeeq ya fito motar yana kallon Imaan yace "I told you it's late already kar mu yi missing flight..." Umma ta hararesa tace "Tunda barin kasar xa ku yi ba.." murmushi kawai yayi ya shafa kansa, Mai aikin Umma ta iso wajen da jakan Imaan da kids dinta ta saka a booth, ta koma ta dauko wani jakan ta saka a booth tana kallon Imaan tace "Mum Ilham Allah ya kiyaye hanya" Imaan na murmushi tace "Toh Aunty faiza sai mun sake dawowa" Umma na kallon Imaan tace "Inji baku mance komai ba dai" Imaan tace "Idan ma mun manta Umma wani lkcn sai mu dauka idan mun dawo" Umma ta dau Musaddeeq tana kallonsa kafin tace komai ua manna mata kiss a goshinta yana murmushi yace "We are going to miss you granny" Dariya tayi tace "I will miss you more sweetheart ka gayar da old woman da grandpa and grandma a gida ka ji?" Gyada mata kai yayi ta sa shi back seat, ta amshi Ilham dake hannun Mujaheed tace "Teemah will be staying with me" Mika ma imaan hannu yarinyar tayi da sauri tana 6ata fuska xata yi kuka, imaan tayi dariya tace "Baxa ki xauna gun granny ba..." Umma ta saka ta cikin mota tana dariya tace "Allah ya kiyaye hanya, a gaida kowa da kowa a kaduna" Driver ne ya taho wucewa da su airport din, Mujaheed ya shiga motar bayan ya kara yi ma mahaifiyarsa sallama Imaan ma tayi mata sallama sannan suka bar gidan. Satin Imaan biyu kenan a kano wajen Umma da kids dinta, jiya Mujaheed ya taho daga kaduna mayar da su gida, Shekaru uku da suka wuce Umma ta koma kano da xama gaba daya, yanxu fita take Dubai duk bayan wani lkci, business take sosai wanda cikin kankanin lkci ta fara tara abun duniya bbu abinda ta rasa, Rahma kadai ce gabanta har lkcn bata yi aure ba tana karatu amma Ummi tayi aure da Maimoon 2 years back. Cikin lkci kadan suka shigo garin kaduna a flight, duk inda Mujaheed ya bi da little Ilham mai sunan Inna sai an tanka ta don kyakkyawa ce sosai yarinyar gashi kwata kwata bata son mutane, Ammi kadai take makale ma don har suka gama xama kano bata wani yadda da Umma, Suna fitowa daga cikin airport kamar ance Imaan ta waiga ta ga Sadeeq yana jan trolley yana danna waya da alama saukansa kenan kasar don ba waje daya suka fito ba, da sauri ta dauke kai don bai ganta ba, Mujaheed dai na waya yana rungume da Ilham, Ita kuma Imaan tana tafe tana jan trolley Musaddeeq na rike da hijab dinta a gefenta, tuntube yayi da trolley din hannunta ya fadi wanda hakan ya ja hankalin mutane da yawa ciki har da Sadeeq, bai yi kuka ba yaron Imaan ta sake jakan hannunta ta dago sa da sauri tana ce masa sannu, Kallonsu Sadeeq ya dinga yi, bai san lkcn da yace "Imaan" juyawa tayi ta kallesa da sauri, Mujaheed ma ya juya da sauri jin an kira sunanta, Sadeeq ya nufeta yana murmushi yace "Waow is this ur son Imaan??" ta kirkiri murmushi ta gyada masa kai, daukan Musaddeeq yayi ya rungumesa ya manna masa kiss a goshinsa yace "He is soo cute, ya sunansa??" Tana murmushi tace "He is Abubakar Sadeeq" Sadeeq ya kara rungumesa yace "Ohhh takwara na kenan, where is his dad?" sai a lkcn ya ga Mujaheed dake kallonsu shi ma, Sadeeq ya nufesa still smiling ya basa hannu, nan suka gaisa yana kallon Ilham ya ja Cheeks dinta yace "Waow little imaan kenan" murmushi kawai Mujaheed yyi yana kallonsa, Sadeeq yace "It's been long, over five years yanxu...." mujaheed yace "Sure, where are you coming from" Sadeeq yace "I am coming from Uk now, ya Kaka?" Mujaheed yace "Tana lafiya lau" Sadeeq ya shafa kai yace "Xan dai je in gaisheta in sha Allah Maryam ta bani sako in kawo mata, you know we are not far from each other a can UK, driver ya xo daukan ku ne?" Mujaheed yace "Not at all, xa mu hau taxi" Sadeeq yace "Driver ya taho min da mota yanxu, muje sai mu yi dropping din ku" Har kofar gida Sadeeq ya ajiye su bayan ya siya ma Musaddeeq bindiga na wasan yara a hanya, Ilham kuma ya siya mata babban doll, Imaan na kallonsa tana murmushi tace "Baxa a hadani da Madam muyi xumunci ba?" Shafa kai Sadeeq yyi yace "Madam... tukunna dai in sha Allah" Imaan ta xaro ido tana kallonsa da mamaki, yace "Ko xa ki sama min madam din?" Dariya tayi ta sauka motar tace "Ni kuma" Sadeeq yyi murmushi yana kallon Mujaheed yace "Ae gaskiya ne, ko in jira little Imaan kawai?" dariya Mujaheed yyi yace "Lkci dai na ta wucewa Sadeeq, try and settle down" Sadeeq yyi murmushi yace "In sha Allah, A gayar min da Kaka soon xan shigo" A haka suka rabu da Sadeeq, Tun da suka shiga compound duk da Ammi dake tsaye tana shanya Musaddeeq bai bi ta kanta ba ya nufi part din Inna da gudu yana kwala mata kira yana cewa "Old womannn, old womannn, where are you" Ammi ta bi sa da kallo tana murmushi, Imaan ta sauke Ilham ta nufi Ammi da gudu tana murmushi dimples dinta na lotsawa Ammi ta dauketa ta rungumeta, Imaan ta karasa ta rungume Amminta tayi mata kiss a goshi tana murmushi a hankali tace "Nayi missing dinki Ammina" Inna da ta fito da duk kwanukan kitchen dinta da tukwane bakin pampo xata wanke wai sun yi k'ura ta daga kai ganin Musaddeeq tace "Waye kuma wannan?" ya kyalkyale da dariya ya saita mata bindiga har da kulle ido daya, xaro ido tayi tana kallon bindigan da yayi kama da na gaske daga nisa, da gudu ta shige parlonta jikinta na rawa tana cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Mujaheed ya haifi jaraba" Mujaheed da tahowansa kenan ya dinga dariya yana kallon son din nasa da ya bi bayan Inna da gudu yana cewa "I missed you old woman...."
Chapter 291 · 0% Book details