← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 200 OF 292

Sashe 200

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranan lahadi da karfe sha daya Mama Hadiza ta iso gidan tare da autar ta Maryam, a part din su imaan suka sauka as usual, sai bayan azahar sannan suka taho part din Inna, Inna dake xaune ta gama hada ma Imaan kwadon rama da ya ji kayan hadi a bowl kenan tayi masu kallo daya ta dauke kai ta rufe bowl din raman ta ajiye a gefe, Maryam ta tabe baki ta xauna tana kallon TV, Mama Hadiza ta xauna kusa da Inna tana murmushi tace "Sannu Innata" ba tare da Inna ta kalleta ba tace "Yauwa, a rufe min kofata kada k'uda su biyo bayan ku su shigo min parlor" Mama Hadiza ta mike ta rufe kofar ta dawo ta xauna tana murmushi tace "Ina yini Inna? Fatan mun same ku lafiya" Inna tace "Lafiya lau, ai naji labarin tun sassafe ku ka shigo nan dai ne ba ku xo ba sai yanxu" Mama Hadiza tayi dariya tace "Mun d'an kintsa ne Inna, ya shirye shirye?" Inna tace "Atoh suna can suna yi, ko shawara ma basa yi da ni wllh ban ya ake ciki da maganan bikin ba, nasan dai ta Rasulu xata gayyato kawayenmu gaba daya sai a kafa mana katon rumfan nan da kujeru mu xaxxauna a tsakar gida" Mama Hadiza ta sunkuyar da kai tana murmushi, Inna na kallon Maryam tace "Toh ita wancan har yau ba manema ne yarinya ta xama sangamemiya ban ji ana batun aure ba Hadiza, kina gaba tana biye da ke fa a baya" Maryam ta hade rai ta gaisheta, Inna tace "Lafiya lau, baki da samarin ne?" Maryam dai bata ce komai ba ta dauke kai, Mama Hadiza dai sai murmushi take tana kallon uwartata, Inna ta tabe baki tana gyara daurin dankwalinta a hankali tace "Ni dai ba ruwana" Mama Hadiza tace "Toh Ina amaryar, ango dai shi ya dauko mu airport daxu?" Inna tace "Isuhu ai ya lalace ya daina shigo min nan kwata kwata sai dai mu ci karo a tsakar gida, Ita kuma Imaan suna can bandaki tare da mata mai gyaran jiki, ke kya ce canja mata fata xata yi, ni kada garin neman ido a rasa gira a kona min jika in shiga uku, iyayin matar yyi yawa wllh, gashi duk tayi ta ajiye min kaya ta ko Ina kamar tababbiya, ni ko in tattara in jibge mata su a kan katuwar jakarta, ni dai na gaji wllh" Dariya Mama Hadiza ta dinga yi, can tace "Mujaheed fa inna?" Inna ta kalleta tace "Ai Mujaheed ya daina xuwa gidan nan, ni na fi wata ma ban gansa ba, ba laifin xaune balle na tsaye ban san me na masa ba ya dauke kafa" Mama Hadiza ta fiddo wayarta a jaka tace "Toh yanxu ai dole ya xo, jiya ma mun yi waya da shi kafin in taho..." Tana magana tayi dialing number Mujaheed, har ya gama ring bai dauka ba, Inna tace "Atoh, ko dai an sace wayar tasa ne, nima har na gaji da kira ba a dauka fa" Imaan ce ta fito daki sanye da Hijab har kasa, ta wara ido ganin Maryam ta nufeta da sauri ta rungume ta cike da jin dadin ganinta, Maryam ta wara ido tace "Waoww sis kinga yanda kike glowing kuwa? Wllh kin yi kyau sosai" Imaan na murmushi ta koma gun Mama Hadiza ta durkusa ta gaisheta, Mama Hadiza ta jawota jikinta smiling broadly tace "Maa sha Allah, my daughter kinyi kyau sosai, ya shirye shirye" Imaan ta boye fuskarta jikinta a hankali tace "Lafiya lau mama" Inna tace "Ai dama ita Imaan da kyanta, wannan gyaran kyanshi dama Ummi, ita ce mummunan gidan, gaskiya ban san inda Rukayya ta samo ta ba..." Dariya Mama Hadiza tayi tana kallon Inna, Inna tace "Allah kuwa" Mama Hadiza na kallon Imaan tace "Toh tafi ki goge jiki ki shirya" Imaan ta mike tana murmushi ta wuce daki Maryam ta bi ta da kallo don kyau ba na wasa tayi ba. Imaan na xaune tare da Maryam a bedroom din Inna bayan la'asar, Maryam dake ta kallonta a hankali tace "Kina nufin ba events da xa ayi Imaan?" Imaan ta bude hannu tace "Nima ban sani ba sai dai ki tambayi Maimoon, daxu dai ya kawo IV, su xa suyi dinner" Maryam tace "Toh dress code fa? Kuma wani kayan yace xa ki sa?" Imaan tace "Oho ni bai gaya min ba" Maryam tace "Kamar ya, ba ku shirye shiryen tare ne?" Imaan ta tabe baki kamar baxata ce komai ba, sai kuma tace "Ni ko waya fa bama yi" da mamaki Maryam tace "Saboda me?" Imaan tayi shiru tana kallonta, Maryam ta kamo hannunta tace "Talk to me, what's happening?" Imaan ta sauke idonta tace "Nima ban sani ba, baya kirana sai dai in ni na kirasa, kuma ba xuwa yake ba" Maryam ta xaro ido tana kallonta da mamaki, Imaan ta d'an yi murmushi tace "In xubo mana abincin ynxu?" Maryam tace "Plss mu yi magana ki ajiye batun abinci, toh ke kina ga babu abinda kika masa Imaan?" Imaan ta girgixa kai a hankali tace "Ba abinda na masa wllh, he just changed all of a sudden, I don't know why...." Sai kuma tayi shiru lkci daya hawaye ya kawo idonta, Maryam ta kasa daina kallonta lkci daya jikinta yyi sanyi, can cikin sanyin murya tace "Kuma kin tambayesa abinda kika masa? Kila kin yi offending dinsa baki sani ba" Imaan tace "That doesn't warrant him to change his attitude, ko don yaga few days ya rage a daura mana aure shi sa yake min haka" sai kuma ta fara kuka a hankali, Maryam taji gaba daya hankalinta ya tashi ta rungumeta tace "Plss kar kiyi kuka, we have to find out why d sudden change of attitude, be strong plss" Imaan dai bata ce mata komai ba, bayan wani lkci ta mike a hankali tace "Bari in xubo mana abinci" daga haka ta fita dakin. Bude Ido Sadeeq yyi don ganin wanda ya shigo masa bedroom dinsa that is almost out of bound for everybody except his mum, Mikewa xaune yyi yana kallonta, Mummy tace "Sai yaushe xaka kai masu kayan da ka bari parlor na ga lokaci na ta wucewa Abba, today is Tuesday, or do they have any other alternative?" Yace "Mum xan ba Mariya ta kai anjima" Da mamaki Mummy tace "Mariya kuma, kaga ina involving din su a harkata a gidan nan?" Sadeeq ya koma ya kwanta yace "Kawarta ce fa Mum, ta san gidansu ai, I don't think I am going out today" Mummy tace "You tell me what's wrong with you this days Sadeeq, meye matsalar ka" Mikewa xaune yyi yace "Mummy frankly speaking gaba daya naji bana son auren nan kuma, am I even supposed to get married now? Isn't it too early? Sure Ina sonta amma bana son auren ynxu gaskiya" Wani kallo ta dinga masa, kafin tace "You are stupid..." tashi yyi ya wuce bathroom ya rufe kofar gbam, ta fi minti biyar tsaye dakin mamaki fal xuciyarta kafin ta juya ta fita. Sadeeq ne xaune parlon Dad dinsa da yammacin ranan, tun shigowar sa parlon bai yarda ya daga kansa ba, Mummy ma na xaune parlon sai kallonsa take, Alhaji Ahmad Bulasawa dake tsaye ya gama duk fadan da xai yi kamar xai ari baki daga karshe ya xauna yana kallon Sadeeq da kyau yace "If you think I have a son that will tarnish my image here in my mother's land... you are mistaken Abubakar, ban haifi wannan d'an ba, kindly get out from my sight now, aure ba fashi tunda ba wani ya nema maka yarinyar ba, kuma ba wani yace ka fito da xancen aure ba yanxu" A hankali Sadeeq ya mike ya nufi kofa ya fita parlon Mummy ta bi sa da kallo, Alhaji Ahmad yace "In sha Allah daurin aure babu fashi ranan juma'ah..... No one is tarnishing my image" direct Sadeeq part din Step mum dinsa ya wuce, Aunty na dakinta ya sameta, ta ajiye abinda take yi tana kallonsa tace "Ango kayi scarce, ya shirye shirye" ya karasa kusa da ita ya xauna ya rike kansa, da mamaki tace "Me ya faru Abba?" Da kyar ya dago yana kallonta da idanuwansa da suka kada yace "Pls Aunty kiyi ma Abba magana a daga bikin nan, wllh naji gaba daya am not ready to be a family man, wani lkcn sai ayi amma ba yanxu ba" Bude baki Aunty tayi tana kallonsa, da wani expression tace "Are you alright Sadeeq? Kana da hankali kuwa, biki saura few days kace a daga, waye kake son maidawa kananun mutane, ubanka dai koh? Kai ma kasan Abban ka will never support this, wani laifi fatiman tayi maka ne?" Ya girgixa kai a hankali yace "Ni bata min komai ba, kawai naji bana ra'ayin aure yanxu, ba cewa nayi a fasa ba, a daga kawai nake so... " Aunty ta saki baki tana kallonsa with much surprise, can ta girgixa kai tace "Don Allah ka rufa mana asiri, kada ka maida mu kananun mutane a idon jama'ah Abba, haba Sadeeq this is very unusual of you, me ya same ka haka, ko dai gantalallun frnds dinka ke xuga ka??" Rasa ma me xai ce mata yyi, can ya mike kawai ya fice daga dakin ta bi sa da kallo baki bude. Mummy ta gama hada duk kayan da suka ma Imaan kala uku masu tsada, daya na dinner biyu kuma na events idan xa su yi a gida, immediate din Sadeeq Annur ta samu a dakinsa ta mika masa tace "Gashi ka kai ma yayanka yana garden, kace nace ya tafi ya kai masu yanxun nan" daga haka ta fita dakin. Bayan Magrib Sadeeq yyi parking kofar gidansu Imaan ya kashe motar ya fito ya dau ledan kayanta dake bayan motar, ya fi minti biyar tsaye jikin motarsa ya ki kiranta a waya, can kawai ya shiga cikin gidan kamar mai counting steps dinsa, direct part din Inna ya nufa, yayi sallama bakin kofar parlon, Inna ce ta amsa sannan ya shiga, Mama Hadiza dake xaune parlon tana cin abinci suna hira da Hajiya Bilki mai gyaran jiki, ta rufe
Chapter 200 · 0% Book details