Sashe 136
Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
kiran layin umma, har ya gama ring ba a dauka ba, ya kalli Mujaheed da ke ta kallon inna yace "Tafi ka kira min uwar ka yanxu..." Mujaheed ya sunkuyar da kansa bai dai ce komai ba ya mike ya nufi kofa a sanyaye ya bude, karo ya kusa ci da umma dake labe tana sauraron komai, shi dai bai ce mata komai ba, har xai tsaya kawai yayi wucewarsa don bai ma son ransa ya kara baci, Sallama Umma tayi ta shiga parlon da lullubi kanta a kasa, Inna na ganinta ta saki salati tana tafe hannu tace "Almunafunfun kenan ku ke ga, to ai ba da gyale kika min cin mutunci a tsakar gida ba don haka sai ki cire ki ajiye a gefe a gama magana, kuma ni dai Allah ya isa rawan da kika dinga yi a gabana kina mokade mokaden maxaunai" Umma ta xauna nan kusa da kofa bata dai tanka ta ba, tana kallonsu Abba tace "Ga ni nan" Sai hararanta Mama Hadiza take, Abba na kallonta da kyau yace "Ita Innar kika xaga yau ko?" Ta Rasulu tace "Ta uwa ta uba kuwa, har ana rirriketa xata doketa, ni dai guduwa nayi na koma bakin gate, kawai 'ya yana su ji daga xuwa biki duka ya ritsa da ni" Abba na kallon Umma yace "Toh yayi kyau, ki tafi gidan ku yau, ko minti goma ban son ki kara a gidan nan...." Da sauri Inna tace "Aa baxa fa ta tafi da igiyar ka mai daraja ba tana galantoyi a titi, yanxun nan xaka datse shi ta tafi gidan nasu tsirara, sai kuma taje can ta dinga xagin uwarta mai ciwon kafa a kano..." Ta Rasulu tace "Ko ta koma wajen shafa mai shinkafa da wake a kasuwar tasha" Umma tace "Toh Alhmdllh xan tafi amma sai a barni in sallami bakina da suka xo biki ko xuwa da yamma" Inna ta mike tace "Wani biki? Bikin da aka fasa ko kuma wani daban kike nufi?" Kallonta umma tayi da sauri, Inna ta tabe baki tace "Ae babu xancen wannan auren, don baxa a ma jikana dole ba, maxa maxa a kira dangin shegun amaryar a sanar masu suyi hakuri Mujaheed yace ya fasa, in dai da raina wllh an fasa auren nan, ni ba ruwana" Abba yace "Bai kai ga haka ba Inna..." Katse da tayi tace "Ya kai har ya xarce Ahmadu" Daddy yace "Haba Inna, kananun mutane kike son ki maida mu, daurin aure nan da 'yan awanni kice a fasa???" Inna tace "Ba ruwana idan ma jarirai xan maida ku, daurin aure dai ni patuu nace bbu shi, idan kuma akwai wanda ya isa ya ja da ni to Bismillah...." Mama Hadiza sai gyada kai take don hka ya mata mugun dadi, a hankali Abba yace "Inna to bakin da suka xo daga garurruwa da dama don bikin fa? Ya xa mu yi da su?" Inna tace "Oho sai a nemi wata a daura auren da ita amma ba xabin Rukayya ba, babu kuma shegen da ya isa ya sa in canxa ra'ayi na gaskiya..." Ta Rasulu tana tabe baki tace "In har kuna son gamawa da Asabe lafiya ku bi abinda tace sau da kafa, jama'ah kuma da aka tara tunda abun kunya ku ke gudu sai a samo yarinya ko cikin 'yan uwana ne a daura auren kowa ya hutu" Inna tace "Shi kansa Mujaheed din ba son auren yake ba wllh wllh, idan kuma karya ne a kirasa a tambayesa a ji ta bakinsa, haka kawai xa a cutar min jika a masa auren dole abinda aka daina yayi tun lokacin kakata Furera...." Daddy yace "Toh gwara a kira Mujaheed din a fara jin ta bakinsa Inna...." Dakatar da shi Inna tayi tace "Ka karyata ubanka isuhu Bukar.... Kuma a kira Mujaheed din" babu Wanda yace mata komai a parlon, Umma dai tuni yan hanjinta suka kada ta fara matsar kwalla, idan aka ce an fasa auren nan da gaske ai an kasheta kenan balle ta san in sha Allahu sai anyi, cikin tsawa Inna tace "A kira Mujaheed din mana tun da karya nake" Mama Hadiza ce ta kira layin Mujaheed, yana dagawa tace "Ka taho parlon Inna yanxu" daga haka ta katse wayar, Inna dai sai girgixa kafa take, ba a dau lkci ba Mujaheed ya shigo parlon da sallama kansa a kasa, nan kusa da imaan dake xaune jikin kujera ya duka don babu waje parlon bai kuma son xama kan kujera, Inna na kallonsa tace "Tsakanin ka da Allah Mujaheed kana son auren yarinyar nan da Rukayya ke son hada ka da?" Shiru Mujaheed yyi yana kallonta, can ya saci kallon Umma dake kallonsa tana matsar kwalla, sunkuyar da kansa yayi, Inna tace "Kun ga munafuki koh??" Abba ya hade rai yace "Don't waste our time Mr Man" d'an murmushi yyi yana kallon Inna yace "Toh Inna da bana sonta ai baxan yarda da auren ba" Sake baki Mama Hadiza tayi tana kallonsa, Umma ta sauke boyayyen ajiyar xuciya, Inna ta saki salati tace "Jini ba wasa ba ni Asabe, Allah sarki Ahmadu kana cikin jarabawar ubangiji 'ya ya duk sun kwaso halin uwa...." Wani kallo Mujaheed ya dinga mata, Inna tace "Toh oho dai, da ka so yarinya da kar ka so ta duk uwasu daya ubansu daya, aure dai tunda aka xageni aka ci ma ni da aminiyata mutunci babu xancensa an fasa, sai dai duk abinda xai faru ya faru Babu kuma wanda ya isa ya canxa min ra'ayi ko waye shi kuwa, idan baku son a maku kallon kananun mutane kamar yanda ku ka ce sai a samu wata yarinyar a aura masa amma ba xabin Rukayya ba, xan nuna ma kowa ni jarababbiya ce yau" daga haka ta mike ta shige daki tana goge guntun hawayenta, Abba ya jinginar da kansa da kujera yana salati a ransa, Daddy kam sai girgixa kai yake ya rungume hannayensa, a hankali Imaan ta mike ta fita parlon Mujaheed ya bi ta da ido haka ma Abba da Daddy.