Sashe 78
Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
ya dokeni ni dai Allah na kallon ki Inna, ni ban ce naki saurayina bane, abokin yaya Muhsin ne ni ban san shi ba" Inna dai na ta cin bread dinta tana shan shayi, Imaan ta gaji da kukanta ta mike xata fita inna tace "Toh aniyar ki dae dama ya bi ki a baya, ba ruwana. Ni nasan wani yaya Muhsin" imaan bata tanka ta ba ta fice hankali tashe. Tsaye Imaan ta ga Mujaheed dai dai inda xata sha corner xuwa part din su, xata gudu ya kamo hannunta, a tsorace tace "Wayyo yaya don Allah kayi hakuri inna sharri take min...." Fingers biyu ya daura kan lips dinsa yana mata wani kallo, haka yasa tayi shiru tana kallonsa gabanta na faduwa, ya nuna mata dakalin dake wajen fuska daure yace "Xauna" Ba musu ta xauna kamar xata fashe da kuka, yace "What did I tell you about standing outside with guys?" Hawayen dake makale idonta ya gangaro tace "Don Allah kayi hakuri yaya" yace "Me yasa baki jin maganata?" Tace "Ina ji fa yaya" yace "Toh meye tsakanin ku da mutumin?" Ta girgixa kai da sauri tace "Ba komai, abokin yaya Muhsin ne?" Yace "Me yake xuwa yi wajen ki?" Ta sunkuyar da kai ta rasa abun cewa, strictly yace "Answer me now before I give you an unclean slap" Ta fashe da kuka a hankali tace "Ba komai fa yaya, kayi hakuri plss" dauke kai yyi na few seconds, sai satan kallonsa take, ganin yanayinsa gabanta ya tsananta bugawa, can ya kalleta ya durkusa gabanta calmly yace "Abba da daddy xa su kira ki su tambayeki what's between you and the guy, me xa ki ce masu?" Ta sauke idonta a hankali tace "Xance masu abokin yaya Muhsin ne" Ya wani hade rai yace "No, kalleni da kyau" Daga kai tayi tana kallonsa, sosai gabanta yyi mugun faduwa, a hankali yace "You tell them babu komai tsakanin ki da shi, kin ji ni?" Ta gyada masa kai kawai, yace "Good, ko baki son ki gama karatu kamar Seeyama? Baki son ki tafi university" Ta turo baki ta boye fuskarta da hannunta murya can kasa tace "Ina so mana yaya" Jin bai ce komai ba ta xame hannunta a hankali ta ga kallonta yake, dauke idonsa yyi murya can kasa yace "Idan ma yace son ki yake kice masu ke baki sonsa" Yar dariya tayi, ya jefa mata wani kallo xai yi magana sai ga Abba da Daddy xa su part din Inna, mikewa yyi da sauri, Daga Abba har daddy kallonsu kawai suke, Mujaheed yyi kasa da kai yana gaida daddy, daddy ya amsa da murmushi yace "Ya aiki Muhammad" Mujaheed yace "Alhmdllh" Abba yace "I called ur line baka daga ba" Mujaheed yace "Na bar wayar can daki naje gaida Inna ne" Abba yace "Ohk" a hankali Imaan ta gaida Abba ba tare da ta yarda ta dago kanta ba, Abba ya amsa daga haka suka wuce tare da Daddy da ko kallonta bai sake yi ba, mikewa Imaan tayi tana kallon Mujaheed, yace "Kin ji abinda nace maki koh?" Kai ta gyada masa a hankali, daga haka ya wuce ya bar ta wajen a tsaye, Mujaheed bai karasa part din su ba mota ta shigo gidan, Driver na parking Umma ta fito, suna hada ido gabansa ya fadi sosai ya juya da sauri to make sure Imaan bata biye da shi a baya, driver ya sakko motar ya xaga ya bude booth, set biyu na boxes masu d'an karen kyau da tsada ya fiddo a booth din yyi cikin gida da su, Tuni Umma ta wuce ciki ita ma, Mujaheed ya bi su da ido. Tare Abba suka shigo parlon da Daddy, Inna tace "Naji dadi da ka ba lamarin nan muhimmanci ka taho Bukar, ina fatan kuma kayi murna da jin wannan abun arxikin?" Daddy yace "Ina kwana" tace "Lafiya lau, ya ka xo?" Yace "Alhmdllh" tace "To madallah" Daddy yace "Jiya Barrister ya min bayanin komai...." Ta washe baki tace "Toh Alhmdllh" yayi kasa da murya yace "Amma inna, Imaan yarinya ce sosai sannan ga ta ba lafiyayya ba...." Inna ta katse sa tana kallon Abba tana nunasa tace "Kai dai wllh Ahmadu baka yi ba, yanxu sai da ka xugesa sannan xaku shigo min nan?" Daddy yace "Aa baki fa jira na kai aya ba inna" mikewa tayi a fusace tace "Babu wani xancen kai aya Bukar, ni kai da d'an uwanka xaku munafurta daga taimako, ni xa ayi ma cin dunduniya, waye baya son nasa ya huta a xamanin nan, koko xan ma Imaan xa6in da xae cuceta ne ko ance maku ban san abinda nake bane, ku kuka haifeni ko ni na haifeku, to wai ma ku tsaya tukun, wai idan aka yi auren nan tare za mu tare gidan da ita?? duk girman gidan naga dai nata ne ita kadai ba tare da ni xata more rayuwar xaman gidan ba, iyaka bai fi a sati inje sau biyar ko shidda ba, to idan baku aurar da ita ba jik'a ta xa kuyi ku shanye ko enlargement xa ku yi da ita kuna kallo a parlor, yau naga abinda ya isheni bai ishi ubangijina ba" Daddy yace "Kiyi hakuri, bai kai haka ba inna, sai ki hada mu da yaron ayi magana ta fahimta" Inna ta goge xufan da take yi tace "To yanxu naji batun kirki, sai dai kuma ban san inda za a samo sa ba, amma ita imaan din ai baxata rasa lambarsa ba, ku kira ta ta taho a kwashe min a wayata in kirasa" Abba dai sai kallon mahaifiyar tasu yake, Daddy ya ciro handkerchief din aljihunsa ya share xufar goshinsa, Abba ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya yace "Toh xa a amshi lambar nasa a gunta in sha Allah" Inna tace "Toh idan kun kirasa me xa ku ce masa?" Abba ya d'an kalli daddy, Daddy yace "Ce masa xa mu yi ya turo magabatan nasa" Inna ta xauna kan kujera tana murmushi tace "Toh Allah maku albarka, ya buda maku" mikewa Abba yyi, daddy ma ya mike yace "Toh anjima xa mu shigo in sha Allah" tace "Toh shikenan amma kar fa ku ce xa ku ja lokacin don yaron yace a matse yake yyi auren" Babu wanda ya tanka ta cikinsu har suka fita parlon.