Sashe 176
Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
managing and just enjoying...." Sai kuma ta yi shiru da sauri, Bai san lkcn da yyi wani murmushi ba har sannan yana kallonta ya dago kanta taki yarda su hada ido yace "Enjoying what?" A rikice tace "A'a ba haka xance ba fa...." Ya lumshe ido yana shakan kamshin gashinta daga cikin hijab din jikinta murya can kasa yace "I will enjoy soon with my lil sis, amma ba da Safeenah ba...." imaan ta bude ido da sauri ta kallesa tace "Wacece?" Ya bude ido shi ma yace "Ita warce nake so mana" imaan tace "Toh are you paying me to help you out?" Yace "Ko nawa kike so kuwa, amma before then sai kinyi kokarin sa su Abba a dakatar da maganar kawo sadakin ki next week" da mamaki tace "Why? My being betrothed won't stop me from helping u out yayana" Ya girgixa kai cikin sanyin murya yace "Shine babban abinda xai sa ki kasa taimakona Imaan" Ta xaro ido tace "Yaya kai fa ka riga kayi auren ka, to ni baka son nayi auren?" Ya kalleta yace "Auren dai kike son kiyi ki bar ni" dariya tayi sosai tace "Kai ma ai ka yi" yace "Amma ai ina xuwa ganin ki kullum" tace "A'a ni dai ba wajena kake xuwa ba, wajen Inna kake xuwa" yana kallon kwayar idonta a hankali yace "Wllh duk ranan da na xo gida ban ganki ba bana iya bacci da daddare" Da mamaki Imaan ke kallonsa tace "Saboda me?" Ya sauke idonsa bai ce komai ba, tayi murmushi tace "Kaga da matarka na sona sai in koma gidan ka in yi waec a can" ya kalleta da sauri yace "A'a ba ruwanki da ita ki dawo kiyi waec din ki kawai" ta make kafada tace "Bana so, Ni fa da gaske Yaya bana son matar nan taka, I so dislike her" Yyi shiru bai ce komai ba, can tace "Yaya na fara jin yunwa fa, xaka bani lambar yarinyar ne yanxu in kirata mu yi magana?" Ya girgixa kai yace "A'a sai dai in kai ki wajenta" tace "When?" Yace "Ko xuwa gobe" tace "Toh Allah ya kai mu" da sauri ta daga kafarta tana kakkabe hijab dinta tace "Wllh Yaya sauro a nan" Mujaheed ya kunna fitilar wayarsa yana haska kafar yace "Sorry dear" yayi stretching legs dinsa ya daura nata a kai bayan ya daga hijab din yana duba inda sauron ya cije ta, shafa smooth leg din nata ya shiga yi yana kallonta, ta xaro ido ta buge hannunsa tace "Aa ni bana so Yaya" a hankali yace "Why?" Ta turo baki tace "Uhn ni bana so" tana fadin haka ta sauke kafarta kasa ta mike tace "Toh sai goben Yaya" ya mike yana kallonta yace "Mu tafi eatry tunda kina jin yunwa?" Ta juyo da sauri tace "Da gaske Yaya" yana murmushi yace "Sure, tafi ki jira ni gun mota a waje" tana murmushi tace "Toh" daga haka ta wuce ya bi ta da kallo har tayi nisa, ya lumshe ido ya bude, kamar mai tausayin kasa ya dinga tafiya har ya fita compound din ya sameta kusa da motarsa tana jiransa, yana bude motar ta shiga front seat, shi ma ya shiga maxaunin driver tana kallonsa tace "Yaya ni kaza nake son ci da drink kawai" yace "Ba sai mun je eatry ba knn" tace "A'a can xa mu je" suna isa wani eatry babba yayi ordering abinda tace, suna xaune wayarta a hannunsa tana kallon hotuna shi kuma sai kallonta yake, hotunan da suka yi tare ne kadai a camera dinsa, sauran duk WhatsApp images ne, hoton Safeenah ko kwaya daya babu a wayar tasa, Imaan ta daga kai suka hada ido, ta xaro ido tace "Why are u staring at me that way?" Bai ce mata komai ba yana kallon waitress dake ajiye masu gasasshen kaza daya da aka yayyanka sae kamshi yake, Mikewa Mujaheed yyi ya tafi ya wanke hannu ya dawo, imaan har ta bude drink din ta fara sha, ya xauna ya dau tsoka daya yana kallonta yace "Bude bakin" dariya tayi tace "Cikin mutane??" Yayi shiru yana kallonta, a hankali ta bude bakin ya kai mata naman dai dai lkcn da suka hada ido da Sadeeq dake xaune eatry din da wani frnd dinsa.