Sashe 225
Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
misalin karfe tara na safe Ammi ta shigo gidan ta dalilin kiran Gwaggwo da Abba yyi tun sassafe, Aunty na xaune parlon sai Umma da duk ta fige damuwa yyi mugun mata yawa, amma da ta tuna Mujaheed ya dawo kuma tana da yakinin yau xai yi saki sai ta samu relieve, Aunty suka gaisa da Ammi, Ammi ta nemi waje ta xauna, Umma dai bata yarda ta kalleta ba, bayan nan Yusuf ya shigo yana rike da makullin motarsa ya xauna ya gaida parent din nasa, Abba ya shigo parlon tare da Daddy duk suka xauna, Daddy ya amsa gaisuwar Yusuf yana tambayarsa matarsa, Kawu Bala ne next din shigowa nan kuma aka yi ta jiran Inna da Imaan sai Mujaheed, Inna ta wangale kofa ta shigo, Imaan na biye da ita sanye da hijab har kasa, kanta a kasa ta xauna kasa kusa da inda Inna ta xauna, Abba ya gaida Inna Daddy ma ya gaisheta sannan kawu Bala sauran ma duk suka gaisheta, sama sama ta dinga amsa gaisuwar tana kalle kallen inda xata ga Mujaheed, Imaan ta gaida su Abba sannan ta gaida su Aunty, Umma dai ta ki yarda ta kalleta sai kallon kofa take tana jiran shigowar Mujaheed dinta, Inna tace "Naga Ikon Allah, toh shi ina mutumin yake, ni fa ban gama tsaftace bandaki na ba na yo nan gaskiya Ahmadu...." Bude kofar parlon aka yi Mujaheed ya shigo suka hada ido da Imaan da ke kallon direction din, da sauri ta sunkuyar da kai gabanta na faduwa ta matsa kusa da Inna kamar irin xuwa yyi ya dauketa, sanye yake cikin kananun kaya ya sauke kansa kasa bai yarda ya kalli kowa parlon ba ya karasa kusa da Yusuf ya xauna sannan ya gaida occupant din parlon kansa a kasa, Shiru ne ya biyo baya a parlon, Umma dai sai kallonsa take ganin wani fresh da yyi abun sa, hakan yasa ta kara jin hankalin ta ya tashi, wato bai damu ba kenan??? kawu Bala ya bude wajen da addu'a sannan ya kalli Abba, Abba ya sauke boyayyen ajiyar xuciya calmly yace "Abubuwa da dama sun faru tun bayan wannan aure da na hada ba tare da shawara da kowa ba few days ago, domin haka nake mai kara ba ma kowa a parlon nan hakuri bisa bacin rai da aka shiga da dai sauran su, to bayan wannan ina son jin views din ku a parlon nan akan auren nan kafin mu san abun yi, Ni da Sadeeq da Bala ba mu da abin cewa tukun sai mun ji naku ra'ayin in sha Allah, but before then... jiya Hadiza ta xo min da wani batu da yake bukatar a duba sa sosai...." Inna dai sai girgixa kafa take, Abba na kallonta yace "Inna xa mu so mu fara jin ta bakin ki a kan auren Imaan da Mujaheed da na hada...." Inna ta katse sa da sauri tace "Me kuwa xan ce Ahmadu, ka ji ta bakina kamar Yaya? wllh Imaan bata son auren nan don ma ka ji, da a shiga hakkinta fa? Tun xamanin kakannin mu aka daina auren dole, toh tunda ta ce bata so gaskiya ni ban ga amfanin auren ba, kada in je in rasa ta a banxa, yanxun nan ya rubuta mata saki ta san inda dare yyi mata, amma gaskiya ba wai bana son auren bane tunda duk jikokina ne, to da wani abu ya samar min jika fa? Ko bacci fa bata yi bata cin abinci, A'a wllh ba ruwanaa" Mujaheed dai sai kallon Inna yake kasa kasa, Umma taji kamar ta goya Inna don murnan furucin ta, Mama Hadiza dai ko kallon Inna bata yi ba sanin awa daya yyi kadan tace ai bbu auren da ya fi na Imaan da Mujaheed daraja a duniya, Abba ya sauke ajiyar xuciya ya kalli Mama Hadiza yace "What did you think Hadiza?" Mama Hadiza ta d'an yi shiru sannan cikin sanyin murya tace "Barrister in har su yaran basu son auren nan abu mafi sauki da kwanciyar hankali shine a raba, xumunci ba abun wasa bane, kada wnn aure ya 6ata xumunci gaskiya...." Abba ya gyada kai cikin gamsuwa bai dai ce komai ba, can ya kalli Umma yace "Meye ra'ayin ki Rukayya?" Umma ta fara matsar kwalla tace "Ba shi da fa'ida auren nan Alhaji, ita yarinya ba so take ba uwar yarinya ba so take ba, toh wani aure kuma Allah na tuba...." Abba yace "Ke ma kuma ba so kike ba koh?" Umma dai bata ce komai ba sai matsar kwalla take, a hankali tace "Alhaji raba auren nan shine kwanciyar hankalin kowa..." Abba ya kalli Aunty yace "Amina ur view?" Aunty ta sauke ajiyar xuciya tace "Duk yanda Allah ya tsara dai dai ne Alhaji, in barin auren in kuma raba auren..." Abba ya kalli Yusuf yace "Engineer..." Yusuf ya d'an yi murmushi bai ce komai ba, Abba ya kalli Imaan da kanta ke kasa yace "Mamana baki son auren nan ko?" Ta fashe da kuka kamar jira take ta gyada masa kai tana shessheka, Abba ya kalli Ammi yace "Hajiya Aisha??" Ammi ta kallesa tace "Gwara raba auren Barrister...." Abba ya kalli Mujaheed yace "M.A...." Mujaheed ya kallesa, ya d'an yi shirun kusan second biyar sannan yace "Baxan iya sakinta ba Abba...." Duk aka xaro ido a parlon ana kallonsa, Imaan ta fashe da matsanancin kuka ta fada kan Inna da ta hangame baki tana kallon Mujaheed ita ma, Abba na kallonsa kamar yanda Daddy ma ke kallonsa yace "Ko saboda me?" Mujaheed ya sunkuyar da kai a hankali yace "Saboda ina son kasancewa tare da ita...." Umma ta fashe da kuka kamar yar yarinya tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, kana son kasancewa da ita fa kace Mujaheed? Ita Safeenar fa???" Abba dai ya kasa cewa komai sai kallonsa yake, Inna tace "Ehh lallai lalacewa ya tabbata a duniya, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..." Mujaheed yyi kasa da murya yace "Ku yi hakuri Abba ni baxan iya sakin Imaan ba..." Daga haka ya mike ya fice daga parlon, kawu Bala ya sauke ajiyar xuciya yana gyada kai yace "Allah sarki..." Inna ta mike ta fashe da kuka tace "Ahmadu duk kai ka ja mana wannan bala'in muna xaman xaman mu, kawai ka tashi sbda tsautsayi ya afka ma bawan Allah Sadeeq ka daura ma mahaukaci aure da jikata, wllh Mujaheed ya fara haukacewa banda haka ko kunya babu yace baxai saketa ba yana son kasancewa da ita, to tayi masa uban me idan sun kasance tare, ai ni naga abinda ya isheni bai ishi Allah ba, amma ba komai da kansa xai gaji ya saketa don wllh Imaan baxata tare gidansa ba, to ta tare tayi masa uban me?? Wllh ta kwaso kayanta gaba daya ta dawo bangarena ni ban yadda da auren ba, dama dai Sadeeq bai dawo bane sai in hakura ta tare gidan Mujaheed din, amma bawan Allah ya dawo kuma yace baxai iya sakinta ba...." Tana fadin haka ta daga imaan dake kuka kamar ranta xai fita suka bar parlon, Ammi ta share hawayen idonta ta mike ta fita parlon Aunty da duk jikinta yyi sanyi ta mike ta bi bayanta, Mama Hadiza ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh Allah yasa barin auren shine mafi alkhairi" a hankali Daddy ya amsa da "Ameen" shi dai Abba ya kasa cewa komai, Umma da ta sakko kasa tana kuka sosai tace "Toh Alhaji ya xa ku yi da yaron da naji ance ya dawo???? An fa ce ba yin kansa bane, don Allah ku duba lamarin nan kada ku xama kananun mutane" Kawu Bala yace "Sae yayi hakuri, Imaan ta masa nisa, ita din matar aure ce yanxu" Umma ta mike tana kuka sosai ta fita waje da sauri ko xata ga Mujaheed amma babu shi babu alamarsa. Mama Hadiza ce ta kira Sadeeq ta sanar masa ya xo bayan ta amshi lambarsa gun Yusuf, suna xaune parlon Abba har lkcn sai ga shi, Kallonsa kawai Daddy yake don ba karamin ramewa yyi ba, duk ya fice hayyacin sa, a sanyaye ya xauna parlon ya gaishe su gaba daya, duk suka amsa suna kallonsa, cikin raunanin murya ya fara basu hakuri yace "I don't know what came over me Abba, wllh ba halina bane, don Allah ku yi hakuri ku yafe min, I am ready to marry Imaan now, Kar kuce xa ku raba ni da ita don Allah, wllh baxan iya rabuwa da ita ba...." Hawaye cike idonsa ya kare maganar, Kawu Bala yace "Sadeeq komai ya faru a rayuwa rubutattce ne daga Allah, Allah kuma ya kaddara Fatima ba matar ka bace, don yanxu haka maganar da nake maka Fatima matar aure ce...." Sadeeq ya daga kai a hankali yana kallonsa xuciyarsa na bugawa, double ya dinga ganin parlon daga nan kuma bai kara jin komai ba bai kara ganin komai ba a parlon.... Tun da Inna taji abinda ya faru da Sadeeq tayi kukanta mai isarta ta buga ma ta Rasulu waya taji ko xata xo ranan, ta Rasulu tace "Ai ki bari Asabe maganar babba ce, in sha Allahu gobe da sassafe xan shigo nima yanxu na dawo garin wllh" Inna na matsar kwalla tace "Toh sai kin xo, don ba lafiya ta Rasulu" daga haka ta kashe wayar ta ajiye tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, Allah ka rufa ma Rukayya asiri ya kasance bata da hannu a abubuwan dake faruwa, idan ko ba haka ba sai dai wata ba ita ba a gidan nan...." Imaan dai na kwance kujera tayi lamo, tunda taji abinda ya faru da Sadeeq kuma wai suna asibiti take kuka, da ta tuna furucin Mujaheed sai taji gabanta yyi mugun faduwa jikinta yyi sanyi, Inna tace "Na fa ce ki kwantar da hankalin ki sai dai Mujaheed yyi ta yawo da auren ki a kansa amma har abada ke da tarewa shegen gidansa, to ki tare kiyi masa me a gidan, ko kuma yyi maki me Allah na tuba? Da kansa xai gaji ya kawo maki takardar ki ya bamu hakuri" ita dai Imaan bata ce komai ba tana jin xuciyarta ja mata xafi. Abba ne tsaye ward din da Sadeeq yake tare da Daddy sai