← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 292

Sashe 27

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da ya kasance Friday tun da Imaan ta dawo schl take xaune balcony dinsu tana assignment dinta na maths, Ammi ta kwalo mata kira for the second time ta ajiye pen din ta amsa, Ammi tace "Idan baxa ki ci abincin ba ki shigo ki mayar min kitchen nace" Tace "Ammi fa na kusa gamawa saura biyu" Daga haka ta ci gaba da assignment din, kamar ance ta daga kai taga wata budurwa da baxata wuce shekaru ashirun da biyu ba tana tahowa, xaro ido tayi ta ajiye pen din ta mike ta fito tace "Lahh Anty Farida" murmushi kyakkyawar budurwar tayi tace "Imaan ta mance ni" Rungumeta Imaan tayi tace "Wllh ban mance ki ba Anty farida, yaya ne yanxu baya bani waya mu gaisa" Farida tace "Toh ke ba sai kice ya ba ki ba" Imaan ta tabe baki tace "Ai to yanxu babu ruwana da shi shima ba ruwansa da ni" dariya Farida tayi tace "Toh saboda me" Imaan na murmushi ta amshi ledan hannunta tace "Ae yanxu yaya ya xama mugu, wajen inna xa ki?" Farida tace "Ehh na xo layin kusa da wannan ne nace bari in shigo yau dai mu gaisa da inna" Imaan tayi dariya tace "Amma yaya yasan xa ki xo?" Farida tace "A'a bai sani ba" Imaan tace "Last time da kika xo gaida inna ai tare ku ka je da shi to me yasa yau ma baxa ki bari ku je tare ba?" Tayi murmushi tace "Na fa ce maki bai ma san na xo anguwar ba, Ammi tana ciki?" Imaan tace "Ehh tana ciki" Farida tace "Toh bari mu gaisa" daga haka ta nufi parlon Imaan na biye da ita, Da fara'a Ammi ta tarbeta tace "Kin guje mu Anty Farida" banda murmushi babu abinda take tace "Ammi karatu ne wllh, kinga yanxu ma hutu na xo" Ammi tace "Allah sarki, Allah ya bada sa'a, ya kuma bada abinda aka je nema" Farida tace "Ameen Ammi" daga haka tayi mata sallama tace "Xan je mu gaisa da inna" Ammi tace "Toh idan xa ki wuce ki biyo ta nan mu yi sallama" tace "Toh Ammi" daga haka ta mike imaan na kallon Ammi tace "Ammi ni dai xan rakata gun inna, idan na dawo xan ci abincin" Ammi tace "Ai shi kenan" tare suka fita da farida tana rike da ledan ta, farida budurwar Mujaheed ce babu wanda bai sani ba a gidan, 2 years back kafin Ummarsa ta dawo gidan farida kan xo ta gaida Ammi da Anty, idan ko xata je gaida inna dama shi xai rakata kuma ko minti biyar baya yarda su yi a parlorn kafin inna ta fara xance yake janta su fita, sosai farida ke son Imaan tun lkcn da take xuwa gidan lkcn ma bata kai haka ba, suna isa bangaren inna imaan ta bude kofar ta shiga da sallama, Maimoon da Rahma na parlon xaune tare da inna, Farida ta shiga da sallama, inna dake xaune kan tabarma ta amsa tace "Wacece wannan kuma?" Maimoon tace "Lahh Anty farida sannu da xuwa" farida tana murmushi tace "Yauwa Maimoon, ykk" durkusawa tayi kasan rug tana kallon inna tace "Ina yini Inna" Inna tace "Lafiya lau ni dai ban gane ki ba" Maimoon tace "Inna faridar ya Mujaheed ce fa" Inna tace "Ayyoo farida ce, sannu da xuwa, kai ku kawo mata ruwa da sauran ayaban nan" Imaan ta mike ta dauko mata ruwa, Inna tace "Allah sarki, da yake sau uku ya ta6a kawo ki a gurguje shi sa ban gane ki ba, ya iyayen naki?" Tana murmushi tace "Sun ce a gaida ku inna" Tace "To madallah muna amsawa, Mujaheed din ne ya kawo ki kenan?" Farida tace "A'a ni kadai na xo" Inna tace "Atoh ba dole ki xo ke kadai ba, ni ma duk yau ban gansa ba ko gaisuwar Juma'ah ma bai xo ya min ba daga na kai kararsa kan ya doki yar kanwar nan ta sa, ko ke haka yayyinki ke cutar ki?" Murmushi kawai farida tayi, Inna tace "Toh Mujaheed kam cutan nasa kannin yake, kawai daga an sauke yarinya a babban mota ya daddage ya kwada mata mari ba laifin fari balle na baki wai ashe ma gantalallen direba ne ya sauketa, to kin san sa da xuciya sai dai kiyi ta hakuri kawai, dama tun da aka haifesa na ji irin kukan da yake a asibiti nasan akwai bala'i gaba, baki ji ba duk ya cika asibitin da muryarsa ga shi wani lafcece" Imaan ta fashe da dariya har da kyakyatawa Maimoon na taya ta, Rahma dai ta6e baki kawai tayi, Farida kam sai murmushi take kanta a kasa, Inna tace "Wllh ba xancen dariya ba nasan abinda nake fada, kuma a yunwace aka haifesa, kilan dai uwar bata ci abinci ba taje haihuwarsa, mu dai haka muka koma gida na wanke sa tass, baki gansa ba jazur da shi ba yanxu da ya kode ba, ke kinga wahalar da nayi da Mujaheed wllh k'are baxai ci ba, tun fa yana tsummarsa nake wahala don sai da nayi kwana hamsin ina kai komo a kansa, to ba abinda uwar ta iya har na koma gidan mijina, daga nan kuma sai dai in kai masu ziyara duk sati, lkcn baki ga uwarsa ba yar siririya doguwa kamar dai yanda kika ga wannan yarinyar Imaan" Inna na yamutse fuska tace "gashi uwar tayi ta cika masa nono yayi ta bulbula tumbudi duk k'arni malam, duk jikokina babu wanda yyi tumbudi kamar Mujaheed, ni ne ma nace uban ya sa masa Mujaheed" Imaan dai an samu abinda ake so don har wani kwanciya kasa take don dariya, Maimoon kawarta na taya ta, Farida dai ta kasa dago kai, Rahma ta wani hade rai tana hararan Inna ko Kadan bata ga abun dariya a wajen ba, Inna ta gyara xama tace "Lkcn yana da shekara daya da wata bakwai uwar ta yayesa, shi ma fa da kyar, ai duk cikin 'ya yan Ahmadu babu wanda ya sha nono irinsa, ya tsotsi uwar ba kadan ba, ko ke baki ga bakinsa d'an tsiyot kusan a tsuke ba? Ai duk tsotso ne yaja haka, sai yaje gantalinsa ya dawo ki ji yace Nono, uwar sai ta fiddo ta basa ya sha yyi nak sannan ya mayar, ke in takaice maki da kyar kanwar uwar ta yayesa don ni dai nace baxan iya wahala ba cikin kishiyoyi, ae ko sai kinga tashin hankali gunsa, bayan an yayesa kuwa idan Mujaheed ya daga maki roban yoghurt to bai direwa sai ya kwankwade tass, ga katon ciki yanda kika san an kifa masa kwarya, Sai uban kukan banxa da shagwaba, ni dai ba komai yasa na daukesa gaban uwar ba sai ganin xai hallaka, yo hallaka mana katon yaro haka yayi fitsari a tsaye kashi a tsaye uwar sai dai ta kwashe ta rabu da shi, duk ta dau son duniya ta daura masa, Shi kuma lkcn kaninsa isuhu na cikin tsumma an haifesa wani fiyot da shi kamar kyanwa ni na ma xata bakwaini ne" Shiru Inna tayi tana kallon Imaan, can ta xaro ido tace "Auzubillahi... Ke meye haka kike yi?" Maimoon ta tsayar da dariyar da take tana kallon Imaan, da sauri ta dagota tana xaro ido tace "Me ya faru Imaan?" Farida ma ta tashi da sauri ganin yanda numfashinta ke sama, inna ta mike a rude tace "Kun ga xata ja min jalala ina xaman xamana ko, to ita nake ba labari da xata dinga dariya haka taje ta mutu a banxa a buga ni a jarida? kai ku fitar min da ita kar ace a parlo na ne, meye kuma numfashi na neman daukewa daga ina ba yarinya da ta xo gaisheni labari? Ni dai ba ruwana a kai ta gun uwarta, ni wllh ba ita nake ba labari ba" Da gudu Maimoon ta mike xata je dauko mata inhaler suka kusa cin karo da Mujaheed xai shigo parlon, ya turata yace "Baki da hankali ne" kamar xata yi kuka tace "Ya M.A Asthma din Imaan ne...." daga haka ta fita, Da sauri ya karasa yana kallon Imaan yace "What happened" inna da har ta fara matsar kwalla tace "Ka fita da ita Mujaheed idan ma asibiti ne ku tafi, wllh ba ita nake ba labari ba xata sa ni a bakin duniya ni ban ma san lkcn da ta shigo parlon ba" Mujaheed ya kalli farida da mamaki, inna tace "Ka rufa min asiri ka fita da ita Mujaheed, meye kuma dariya haka kamar mahaukaciya, ban san meye abun dariya a xance na ba" dagata Mujaheed yyi suka fita parlon, can kusa da wani flower ya xaunar da ita yana kallonta yace "Relax now" da kyar take numfashin kamar xai dauke, Maimoon ta iso kusa da su ta durkusa ta mika ma Mujaheed inhaler din, budewa yyi ya kai bakinta da sauri, bayan wani lkcn ta dinga sauke ajiyar xuciya, maimoon dai sai kallonta take cike da tausayi, Ta jingina da flowern tana ajiye numfashi a hankali hawaye na sauka idonta cikin tsarkewar murya tace "Yaya xan sha ruwa" mikewa Maimoon tayi ta tafi dauko mata ruwan da sauri, shi dai kallonta kawai yake, bayan wani lkci ta daga kai suna hada ido ta kamo hannunsa ta kwashe da dariya, ya daure fuska yace "kina da lafiya kuwa?" Tana dariya a hankali tace "Wllh yaya babu abinda inna ta mance bata gaya ma Anty farida ba yau" ya wani xaro manyan idonsa yace "Kamar me?" Imaan ta kara fashewa da dariya hawaye na sauka idonta, ya hade rai yace "Baxa ki daina wannan dariyar mahaukatan ba" ta hadiye da kyar, har wani ciwo kirjinta ke mata cike da karfin hali tace "Labarin ranan da aka haifeka har sanda aka yaye ka take bata da yanda...." Ganin yanda Mujaheed ya bude baki da idanuwa yasa ta kara kwashewa da dariya tace "Wllh yaya har da tumbudi da fitsari da kashi duk ta fada mata" Mujaheed ya kasa rufe baki, Ganin irin dariyar da take ya sauke boyayyen ajiyar xuciya yace "Toh dariyar ya ishe ki haka" Mikewa yyi fuska daure xai koma part din Inna ya hangota tana tahowa da gudu, tsayawa yyi har ta iso
Chapter 27 · 0% Book details