← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 262 OF 292

Sashe 262

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sati daya da komawar Umma Zaria Abba ya kira Mujaheed parlonsa da yamma, Mujaheed ya xauna kasa yana kallonsa yace "Ga ni Abba" Abba yace "Na ji shiru baka ce xa ku koma gida da matar ka ba, what's happening?" Murmushi Mujaheed yyi yace "Abba Inna ce" Abba yace "Me Innar tayi?" Mujaheed yace "She said I am not leaving with her" Abba yace "Ko saboda me?" Wani murmushin Mujaheed yyi bai dai ce komai ba, Abba ya gyada kai yace "Tashi ka tafi" mikewa yayi ya fita parlon. Inna ce tsaye parlonta inda take shiga ba nan take fita ba tana kallon Imaan, Imaan dai na kwance idonta a kan Tv bata yarda ta kalleta ba, Inna tace "Yau naga abinda ya isheni yarinya mara kirki kawai, to a kan me xaki debar ma mutumi dambuna kuma d'an walakanci ya bar min shi a walakance bai ci ba? waye kuma Mujaheed Allah na tuba mutumin da na yi wahala da shi, meye nasa ne ban sani ba, 'ya yana suna wahala dani ku kuma ku dinga cinye min" ita dai Imaan bata tanka ta ba, Inna tace "Yau naga jarababbiya wai ni xata nuna ma son miji, Yar figigiya dake kin san dadin miji, ba kunya ba tsoron Allah ki satar min nama ki kai masa shi kuma ya ki ci, anya Imaan kina son gamawa da duniya lafiya kuwa?" Shigowar Abba yasa Inna tayi shiru, Imaan ta mike xaune tana masa sannu da xuwa, Abba ya amsa yana kallon Inna ya xauna ya gaisheta, Inna ta shimfida tabarma fuska daure ta xauna tace "Lafiya lau Ahmadu ya aiki" yace "Alhmdllh" Imaan ta gaida Abba sannan ta mike ta wuce daki Inna ta bi ta da harara sannan tayi kwafa, shi dai Abba kallonta yake bai ce komai ba, Inna tace "Daxu ma Bukar ya kirani muka gaisa nace Allah yayi masa albarka, ya rabasa da sharrin mutum da aljan, ya shiga ko ina a sa'a ya fita a sa'a" Abba ya gyada kai yace "Hakan na da kyau ai" mikewa Inna tayi tace "Bari in d'an yi shara in dawo Ahmadu" Abba yace "Magrib ai ya kusa Inna, dama kuma magana na xo xa mu yi" Inna ta koma ta xauna tace "To lafiya dai ko?" Abba yace "A'a lafiya lau, kawai naga ya dace Mujaheed ya dau matarsa su tafi ko, tun da Alhmdllh ynxu bbu wata matsala...." Inna ta katse sa tana mitsi mitsi da ido tana girgixa kai tace "Ae ba Mujaheed ya halitto min ita ba balle in basa ita su tafi, waye kuma Mujaheed?? ku dai wllh ku dinga tsoron Allah komin rintsi, Ahmadu duk matan ka biyu da ka aura ka gaya min warce aka ta6a baka bbu lefe? Shi ma Bukar ya gaya min ko bbu lefe ya auri Aisha, sai Imaan ce xa a kai gidan Mujaheed ba lefe sbda ance maku gantalalla ce? Mutane dai bbu tsoron Allah ko digo a xuciyarsu, tirr wlh" Murmushi Abba yyi yace "Inna ai ba yace baxai yi bane, xai mata in sha Allah, wannan ai dole ne" inna tace "Toh yayi mu gani tukun, gwalagwalai hudu na kirga a lefen da Bulasawa yyi mata wllh tllh, duk atamfofin kuma babu na kasa da dubu hamsin, ga leshi duk 'yan dubu dari dari, to me yafi haka ma'ana?? kaiiii Ahmadu ku ji tsoron Allah, wllh Imaan ba banxa take ba, a kan lefen nan ma ni sai in soke auren nan gaba daya in ga ta tsiya don uwa ta bata ce min je ki kya gani ba, haka kawai ya cutar min jika ya kai ta ya barota bbu kayan aure jikata ta walakanta, to Allah ya tsine ma wanda yace auren xumunci ne ko ba ayi lefe ba bbu komai, don da alama an rada maku hakan ne shi yasa ku ke shashantarwa, to wllh bari ku ji, sai na ga akwati guda dai dai har sha biyu sannan Imaan xata bar gidan nan, idan ba haka ba gwara inyi ta kallon abata, ba ruwana ni yar gaskiya ce..." daga haka ta mike ta fita daga parlon tana cewa "A dai dinga tsoron Allah komin rintsi, ance maka don kai ka haifi Mujaheed sai in ki gaya maka gaskiya, haka kawai mutumi ka lallabo ka xo min nan don ka min dadin baki a cuci Jikata, Albarka uwata ta dinga sa min kafin ta rasu wllh..." Murmushi kawai Abba yake, can ya mike yana girgixa kai ya fita parlon. Karfe tara na dare Mujaheed ya shigo parlon Inna da sallama ya ganta xaune saman darduma tana xuba gyangyadi ga carbi a hannunta, tsayawa yyi yana kallonta, can yyi murmushi ya nufi kofar dakin walking without making any sound, yana bude kofar dakin Inna ta bude ido daya a hankali tana kallonsa har ya shiga dakin, yana shiga Imaan na fitowa daga bathroom daure da towel, xaro ido tayi ganinsa, lkci daya ta nufi gefen gado da sauri ta xauna tana kallonsa kamar xata yi kuka tace "Yaya shine xaka shigo bbu sallama, gashi ban sa kaya ba, kuma idan inna ta gan ka fa? Don Allah ka fita plsss" Juyawa yayi xai rufe kofar dakin ya ga Inna tsaye kyam bakin kofar tana kallonsa, duk da yanda ya so dakewa kada yyi dariya sai da yayi dariyan yana sunkuyar da kai, ta cakumosa fuska a murtuke tace "Dakina yyi maka kama da otal Mujaheed? Yaushe ka lalace haka bani da labari, bbu kunya balle tsoron Allah ka afka ma yar yarinya daki daga ita sai tawul ta fito wanka? Me hakan ke nufi fisabilillahi? Meye manufar shigo mata tana tsirara?" Ya wara ido yace "Toh xa ki hanani shigowa gun matata ne Inna?" Inna tace "Toh wllh ka gaggauta neman tubar ubangiji, ta ina ta xama matar ka baka fita hakkinta na aure ba Mujaheed? ga sadakin ka can a cikin dirowa sai in dauko maka in baka tsiyar ka yanxun nan kar ka kawo min nansans, Ina ce da shi kake takama?" Ya shafa kansa yana murmushi yace "Toh ai Aunty ta fara hada mata lefen sai ki bani matata mu tafi koh?" Inna tace "Wacece kuma Aunty? To wllh ka rufa ma kanka asiri ka amso kudadden ka ka samu yar gayu ka bata ta hada ma jikata lefe, kwata kwata ban yarda da siyayyan Aisha da Amina ba, duk yaushe suka waye? sai kaga kayan da suka hada ma Yusuf duk rubabbu ba kyau, Kamar daga kauye" dariya kawai Mujaheed ke yi yana kallonta tace "Atoh ni ba ruwana" tana rike da shi ta juya xata fita dakin yace "Toh sakeni mana Inna" Bata sauraresa ba har suka fita dakin ya juya yana kallon Imaan da tayi masa gwalo, wani murmushi yyi yana gyada kai Inna ta kulle kofarta sannan ta sakesa, ta xauna tace "Kudin akwatuna nawa ka bata?" Yace "Idan ta gama hadawa xa ki gani ai" tace "Ni da xa a ji ta nawa ma a siya mata sakk irin na Bulasawa har kayan ciki" Mujaheed bai tanka ta ba, bayan kusan minti goma Imaan ta fito sanye da hijab har kasa sai xuba kamshi take, kallonta kawai Mujaheed yake har ta xauna, Inna tace "In xuba maki abincin ne ko ko?" Gyada mata kai Imaan tayi, Inna ta mike tace "Ina xan bari ki lalace a shiyana Bukar yyi tunanin bana baki abinci ne ya kullace ni" daga haka ta shiga kitchen, Mujaheed ya bi ta da ido sannan ya mike, imaan na ganin haka xata tashi yyi saurin rikota, kamar xata yi kuka murya can kasa tace "Yaya ka bari kaga Inna xata fito ynxu fa.. " xaunar da ita yyi kusa da shi ya jawota jikinsa ya daura forehead dinsa kan nata yana kallon lips dinta murya can kasa yace "Ke kika ce mata sai na maki lefe koh??" Xaro ido tayi tana son komawa baya yaki saketa, rufe fuskarta tayi jikinsa hankali tace "A'a wllh, ita ce dai ta fadi haka...." Rungumeta Mujaheed yyi yana son dago kanta taki yarda, Inna na fitowa kitchen rike da plate din abinci tayi kasake baki bude tana kallonsu, sai kuma ta saki salati, da sauri Imaan ta fara turasa tanq xaro ido amma ya ki saketa, Inna ta ajiye abincin hannunta a kasa tace "Mujaheed iskancin naka a parlor na xae kare yau kuma? Haka kawai mutumi ka shiga ka matse min yarinya ba tsoron Allah??" Bata jira cewarsa ba ta tafi da sauri ta bude kofar parlon tace "Taho ka fita kada Ahmadu ya fitar min da kai yanxun nan, wannan wani irin iskanci ne da lalata, mutumi ka shigo xaka lalata yar mutane a parlona, meye ma'anar hakan ma dai tukun?" Imaan dai tuni ta janye daga jikinsa kamar xata yi kuka, a fusace inna tace "Ke kuma jarababbiyar yarinya kin wani sakar masa jiki kin makalkalesa shashasha kawai jarababbiya, to wllh kai ki xai yi ya baro ki don ma kiji in gaya maki, waye kuma bai san iskancin namiji, ohhh ni patuu yau naga iskanci gun yara, a parlon nawa kuma babu tsoron Allah xaka makalkaleta Mujaheed, Toh wllh bari Ahmadu ya shigo ba dani xa ayi wnn iskancin ba dama kada Mujaheed ya sake xuwa min nan wllh ni ba gantalalliya bace kuma ni ba yar iska bace" Imaan ta mike tana turo baki ta wuce daki, Inna na kallon mujaheed a fusace tace "Baxa ka xo ka fita ba ko sai na tafi na kira ubanka, banda baka da tsoron Allah imaan din ma nawa take gaba daya fisabilillahi da xaka matse ta haka kan kujera Mujaheed? Ni wllh ban taba ganin haka ba tunda uwata ta haifeni, to me xaka mata?" Mujaheed ya mike yace "Da kin yi ki shiru kiga abinda xan mata ai" daga haka ya bi ta gefenta xai fita dakin ta kai masa dundu a baya tace "Toh Allah ya isa wllh, ka je kai da Allah, wanda bai yi iskanci ba ma a rayuwar ya ya kare balle yyi iskanci" murmushi yyi bai kuma tsayawa sauraranta ba yyi wucewarsa. Washegari da safe Imaan ta tafi gaida Amminta daga part din Inna bayan inna ta jaddada mata ko minti biyar kada tayi
Chapter 262 · 0% Book details