Sashe 166
Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Imaan na gyaran dakinta da safe misalin karfe tara bayan ta gama shiryawa Ammi ta shigo dakin tana kallonta tace "Jira kike in xo in fito da ke Imaan" Imaan tace "Yanxu xan fito" Fita Ammi tayi daga dakin Imaan ta bi bayanta ta shigo parlon tana kallon Inna dake xaune ta cakare cikin atamfa da hijab tayi tagumi, Imaan ta dau well ironed hijab dinta tana kallon Inna, Inna ta ki kallonta ta tabe tobaki tace "ku dai ba ku da tsari, baku da kirki, tun jiya ince maki xamu fita amma saboda walakanci ki bari in xo in xauna kamar gantalalla ina jiran ki..." Imaan tace "Ni shayi kawai xan sha, kullum sai ki sa mu dinga xuwa gidan mutane da asuba basu tashi ba ana mana walakanci" Inna ta xaro ido tace "Ni babu wanda ya taba walakanta ni, ki ji tsoron Allah, Ba kuma ruwan ki idan ma tsakar dare xan je gidan mutane, wllh ki daina haka ba halin xaman gidan miji bane..." Imaan bata tanka ta ba ta wuce kitchen ta hado shayi ta dau bread ta fito, sai da ta ji ta koshi sannan ta ajiye sauran bread din, Inna dai ta wani tsuke fuska, Imaan ta dawo parlon tace "Na gama" tsaki Inna ta ja ta mike ta nufi kofa tace "Mutane dae ba tsoron Allah a xuciyarsu, jiya mu yi magana rimi rimi ki dawo nan uwar ki tace kar ki shirya, to ta ma kanta ae, dama bafillatani kuma, kai dai kayi ta fatan ku rabu lafiya da shi, ni dae ba ruwana" Ammi dai na goge gogenta a parlor bata ce komai ba, Imaan na kallon Ammi a hankali tace "Ammi sae mun dawo" Ammi ta masu Allah ya kiyaye ta ci gaba da aikinta. Adaidaita Imaan ta tsayar masu a bakin titi, Inna ta shige adaidaitan ta xauna, Imaan na kallonsa tace "Kabala xaka kai mu" da mamaki Inna tace "Kaji jaraba ko yaro, ina ruwanta ita dai ba kawai ta shigo ka ja adaidaitan ka ba" Yayi dariya yace "Ae da gaskiyarta Kaka, gwara ta tambaya ta ji ko xan je" Imaan ta wani hade rai ta shiga, Inna tace "Bata da wayo ne, ai ku din ba wai tsoron Allah gare ku ba, da mutum ya tsaya gaya maku inda xa shi sai don mugunta ku fasa xuwa can din, shi sa nake shigewa kawai abu na in xauna, Atoh... ina xan iya da gantalallu" Murmushi kawai mai adaidaitan yake yi yace "Gaskiya ne Kaka" Dai dai kofar gidan Ta Rasulu mai adaidaitan ya tsaya, Inna tace "Kaga gidan aminiyata ta Rasulu kenan na xo, kuma babu irin motar da babu a gidan 'ya ya na, kawai dai nayi ra'ayin hawa adaidaita ne, ka ga kuma ni tsohuwa ce sai an bani ba wai miji gareni ba, kai koma da mijin yanxu shi ma ta kansa xai yi ya ji da tsufansa, don haka ni dai ba wata mai kudi bane, har naira 30 an sha kawo ni gidan ta Rasulu shekaru kusan goma da suka wuce wllh..." Tana magana tana duba jakarta ta fiddo naira 70 ta mika masa, yace "Kaka kudin ku dari biyu da hamsin ne" Inna ta wani xaro ido tace "Kai barawo ne d'an nan, a kan tsohuwa kuma satan naka xai kare yau sabida baka tsoron Allah??" Tuni Imaan ta shige cikin gate din gidansu Ta Rasulu, tana shiga parlon ta Rasulu ta fito dakinta da sauri tana cewa "Shegu dawowa ku ka yi marasa xuciya??" Ganin Imaan ce tace "A'a ke kuma daga ina?" Imaan ta xauna ta gaisheta Ta Rasulu ta amsa tace "Ca nake mayun yaran nan da na kora ne suka dawo, duk sun dameni watakil ma iyayensu basu tashi ba, ni kuma sai aka ce masu an hallito ni ne don wahalan jikoki ya kasheni, to ni ko su Muhammadu da..." Shigowar Inna yasa tayi shiru tana kallonta tace "A'a ashe tare ku ke Asabe" Inna na nuna Imaan tace "Ke din nan baki da kirki wllh, kina ganin mutumi xai fara ci min mutunci kan kudi kika gudu kika bar ni daga ni sai raina, ban ga amfanin biyo ni da kika yi ba ma don wllh sai a iya kama ni a nakada min shegen duka a titi kiyi tsit abun ki, wa xai maka haka banda bare dama, ae Bukar baxae min haka ba" Ta Rasulu na kallon Imaan ta rike ha6a tace "Gaskiya kam naka baxai maka haka ba dama, toh ya ku ka kare da mai mashin din Asabe" Inna tace "Yan arxiki suka taso suka basa dari biyu a nan waje ni ban ma san su ba, ni dai nace Allah ya isa don 70 nayi niyyar basa tunda ba a kasa ake hako kudin ba" Imaan ta wani daure fuska kamar xata yi kuka, Ta Rasulu tace "Ae yanxu yawanci duk barayi dake fashi da makamai a da ne suka koma aikin adaidaita, amma dai ai gwara haka koh? Da ace suna shiga gidajen mutane" Inna tace "Wllh nima nayi tunanin haka don har sai da na tambayesa ko barawo ne shi, kuma baki gansa ba bakikirin malam, ni dai da kyar idan yyi Imani lokacin da yake ganiyar fashi da makaman" Ta Rasulu ta shimfida mata tabarma tace "Tunda ku ka rabu lafiya ai Alhmdllh, ya su Ahmadu da Bukar" Inna ta xauna tace "Ahmadu yana nan lafiya, Bukar kuma yana can gun neman na kai, maganar da kika ce sai na xo xa mu yi jiya da rana, wllh gaba daya hankalina ya kasa kwanciya ni dai ina idar da sllhn asuba na fara aikace aikace na gama na sa ruwan xafi nayi wanka, na fito na shirya, na kada shayi da burodi na sha sannan na fito, wannan mata dake xaune ita ta 6ata min lkci banda haka da tun sassafe ma xa ki gan ni gidan nan" Ta Rasulu tace "A'a gwara da kika xo dama, to ni dai naje na samu mutumi kamar yanda muka shirya, kuma ga maganganu dai ba dadi wllh, wannan yarinya dai dake xaune gaskiya ido yayi katutu a kanta, da matsala ba kadan ba...." Inna tayi kwafa da karfi tana gyada kai tace "Ya tsole kuwa idon don ubansa, ko ma na wasu shegun ne, su rasa wanda xa su sa ma ido sai Imaan? Tabb lallai lalacewa ta tabbata wai jikar Patuu xa a sa ma ido " Ta Rasulu tace "Atohhh, ga dai shi nan ya bada icce da xa tayi ta wanka da kuma na sha, da na hayaki, duk na sati guda kuma ku rufa min asiri ko da kuskure kada tayi tsallaken kwana bata yi ba don ni ba wahalalliya bace, ba ku ji kafata da na dawo ba kamar xan daddatse su in huta, ni banda ma ta ki ce Imaan din ina ruwana da lamarinta, tunda muke da uwarta ina ga in dai ta tako gidan nan to Asiya ce ta haihu, to ina dalili, kawai albarkacin ki nake wannan wahalan, sannan abun tsoro da tashin hankali fa ce min yayi na kusa da ita sosai ne ke son ganin ya tarwatsa rayuwarta, ke kya yarda Asabe?? Wllh kar ki bari tayi wasa da Magungunan nan...." Inna tayi tagumi tace "Amma dai me yasa yanxu ba a tsoron Allah ne ta Rasulu, mu xamanin mu duk inda ka bi tsoron Allah ake kaca kaca ba wasa, kowa ya saka Allah a rai, yanxu ko tsoron Allah yayi karanci, to ko dai gun aikinsa ne aka sa ma 'yar sa ido ince ya hakura da aikin ya dawo mu xauna Allah xai rufa asiri??" Tsaki ta Rasulu tayi tace "Ka ji ki da rikicin tsufa, ce maki aka yi fa na jikin ku ne ke son cutar da ita" Inna tace "Ehh lallai xai cutar da kansa kuwa koma waye, xai san jikata yake nufin cutar wa, to yanxu dai abinda xai faru yanxu shine... Kowa dai yasan ni yar gaskiya ce sabili da haka baxan yi abinda bai kamata ba, shiryawa kawai xa mu yi ni da ke mu koma wajen, in sha Allahu ko nawa ne ni xan biya a mayar da nufin sharrin da ake ma jikata kan 'ya yan masu bin ta da sharrin, ba shkkn ba??" Ta Rasulu tace "Haka ma xa ayi, yanxu dai bayan kwana biyu ki taho ki kwana nan don da asuba xa mu fita amma gaskiya sai dai mu sami karyar da xan gilla ma Asiya da mijinta don sun ce in daina jajibe jajibe, ni ko jajibe jajiben da nake na neman lafiyata ne da na jikokina da na 'ya ya na, yanxu abinda duniyar baki daya ba gaskiya wa xai xauna, bana bi ta nasu ba basu san komai ba su yara ne" Inna tace "Ai ki kyale yaran yanxu mun dai haifesu ne bamu haifi halinsu ba, nima dai kafin in fito sai na gilla ma Ahmadu karyar don ba lallai ya yarda ma in taho ba" Ta Rasulu tace "Atoh, wa xai xauna" ita dai Imaan na xaune fuska daure sai kallon Tv take, inna bata bar gidan ta Rasulu ba sai kusan karfe sha biyu, Ta Rasulu ta dauko naira Hamsin ta bata wai su hau mota, Inna ta tabe baki tace "Da dai ba masu fashi da makamai suka koma yin d'an sahun ba, ba ruwana ajiye gantalalliyar hamsin din ki ina da dari xan lallabasa ya kai mu gida" Sabulun wanki kwaya daya ta Rasulu ta dauko ta mika ma Imaan tace "Ga shi kya wanke 'yan kampai, ni dai bani da komai dakin duk maroka sun xo na kwashe masu komai, gashi wata bai kare ba" Imaan ta amsa tace "Nagode" har bakin titi ta Rasulu ta rakasu Inna na rike ledan Magungunan hannu bibbiyu tsabar muhimmanci da ta basu, Ta Rasulu ta tsayar da adaidaita tace "Kai yaro nan nan malali xa ka kai su, kaga dai ba miji gareta ba ya rasu, nawa xa ka kai ta?" Mutumin yace "Dari uku Kaka" ta Rasulu ta buga adaidaitan tace "Toh je ka, mu ma neman dari ukun muke kuma ba mu ta6a fashi da makamai ba mu dai" Mai adaidaitan na dariya yace