← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 292

Sashe 11

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

bude motarsa suka yi ido hudu da daddy da ya fito Imaan ta rungumesa, Daddy ya sakar masa murmushi, hakan yasa ya nufe sa kamar mai kirgan steps dinsa, daddy na shafa kan Imaan yace "Ba kya girma koh Mamata" ta kara kankamesa tace "Don Allah daddy ka daina dadewa haka wllh ina Missing dinka" yyi murmushi yace "To xan daina mamana" Mujaheed ya risina yace "Sannu da hanya Abba" Wani hade rai Imaan tayi tana hararansa ta gefen ido, Daddy na murmushi yace "Thanks Son, ka bar mu a birnin tarayya ynxu koh" murmushi Mujaheed yyi yace "Ae kam daddy" daddy yace "Toh Allah yayi jagora, ya aikin fa?" Yace "Ae ban fara ba sai Monday Abba" Daddy yace "Allah ya kai mu" Daddy ya mika ma Imaan da ta turo baki ledan apples dinta da chocolates don a ko da yaushe tsaraban ta kenan, Mujaheed dai ko kallonta bai yi ba ya dau jakar laptop din daddy da wasu files ya nufi part dinsu, Murguda baki Imaan tayi ta jera da daddynta tana ci gaba da gaya masa yanda tayi kewarsa, Mujaheed ya sunkuyar da kai ya gaida Ammi bayan ya ajiye jakar hannunsa da files, ta amsa ta dau jakar ta wuce daki, Daddy ya xauna yace "Barrister bai dawo ba ko Mujaheed?" Mujaheed yace "Ehh bai dawo ba" Daddy yace "Ohk mun yi magana daxu ma" Mujaheed ya dukar da kai yace "Toh Allah ya huta gajiya Abba" daddy yace "Madalla nagode son" har ya fara tafiya Daddy ya kalli ledan apples da chocolates da Imaan ta sa gaba tana dubawa yace "Son baxa ka Debi apples ba" Da sauri Imaan ta jawo ledan jikinta tana kallon daddy, Mujaheed da har xai ce A'a don he isn't a fan of Apple ganin abinda tayi yayi kasa da kai yana shafa gashinsa yace "Toh Abba" daga haka ya nufeta, bude baki tayi tana kallon daddy lkci daya hawaye ya kawo fararen idonta, Mujaheed ya jawo ledan yana kallonta da kyau ya cire spare leda ya debi apples har hudu a cikin guda takwas da Daddy ya siya ya xuba a wani ledan yana kallonta har sannan, ya kara bude ledan chocolates din ma ya debi mai yawa ya xuba a ledan hannunsa, har ya mike ya sake dawowa ya dau Apple daya ya sa ka a ledan, daddy ya dauke kai yana murmushi, Mujaheed bai yarda ya kallesa ba yace "Nagode Abba" daga haka ya fice parlon. [6/11, 12:34 PM] +234 703 570 1601: 🌟⭐ *Imaan*⭐🌟
Chapter 11 · 0% Book details