Sashe 283
Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yace "A'a ina dubata a gida" Abba yace "Innar tana nan har yanxu?" Mujaheed yace "Ehh" Abba yace "Toh ka bari su taho tare gida tunda ta bukaci hakan, hakan ne kwanciyar hankalinmu gaba daya" yace "Toh Abba" daga haka Abba yayi masa sallama ya katse wayar. Inna ta gama hada kayan Imaan da kanta cikin jaka a bedroom dinta tana mita, Maimoon dai na tsaye tana kallonta, Inna ta xuge zip din ta mika ma Maimoon wayarta tace "Kira min Aisha" Maimoon ta amshi wayar ta kira Ammi, Ammi na dagawa Inna tace "Toh Aisha ga dai imaan nan na xo na sameta ba kanta, tunda nake ban ta6a ganin ta rame irin yanda na xo na sameta ba, Ni ba ruwana ki Kira mijin ki yanxu xan taho da jikata gida don baxan kirasa ya bata min rai ba yayi min rashin kunya, wllh babu mahalukin da ya isa hanani fitar da Imaan daga gidan Mujaheed yau, don idan ta mutu ni kadai nayi asara ba wani ba" daga haka ta mika ma Maimoon wayar tace "kashe min kayana" Maimoon na murmushi ta kashe wayar. Kafin Inna ta gama hade haden kayanta ta fito, har Mujaheed ya saka ma Imaan hijab yana rike da hannunta ya tafi parking space, front seat ya bude mata ta shiga ya rufe sannan ya koma cikin gidan. Bai ko bi ta kan Inna ba ya kira Maimoon yace ta xo su wuce sannan ya koma gun motar. Har suka isa gida Inna mita take cikin mota wai taya sauro xai shiga gida mai lafiya haka ya illata mata jika haka, bbu wanda ya tanka ta a motar, imaan dai baccin ta kawai take, daga karshe mujaheed ya kure karatun Qur'anin dake tashi a motar. Parking yyi Inna ta bude motar ta fice tana kallon Maimoon tace "Sakko ki bude mata ta fito" Maimoon ta fito ta bude side din Imaan, ganin tana bacci Inna tace "Kin ga jaraba koh? Wannan sauron lafiya ne kuwa ni patuu" Murmushi Maimoon tayi tana tashin Imaan, Imaan ta bude ido sannan ta fito motar tana rike da Maimoon sbda juya mata da kanta ke yi, Inna tace "Toh Allah dai ya isa" daga haka ta kama hannunta ta wuce sashinta da ita fuskarta babu walwala, Mujaheed ya bi su da kallo yana murmushi, Maimoon ma ta bi bayansu. Saman kujera Imaan ta kwanta ta juya baya, Inna dake ta kallonta tace "Bari in xubo maki abinci ki ci mu wuce asibiti, ba sai na jira kowa ya ban kudi ba, lafiyar ki ta fiye min komai dama tuwo nayi tun asuba kafin in baro gida" daga haka ta wuce kitchen ta xubo tuwa da miyar kubewar da tayi ta dawo parlor ta ajiye kusa da Imaan tace "Sakko ki ci, kin ji takwara" Imaan ta bude ido da sauri tace "Ni fa baxan ci komai ba ki tafi da shi" Inna tace "Baxa ki ci komai ba kuma, ni fa bana son wahala, yanxun nan xuciya ta debeni sai in tattaraki ki koma gidan Mujaheed din ki mutu" Imaan ta ki juyowa tace "Inna ni ki tambayesa na ci abinci fa" Inna ta xauna tayi tagumi tace "Ai ni na shiga uku" Aunty ce ta shigo parlon da sallama ta gaida Inna tana kallon Imaan tace "Wai imaan bata ji dadi ba" Inna tace "Wllh, wai xaxxabin cixon sauro Amina, yaushe rabon da ayi wannan ciwon fisabilillahi, tun tale tale fa, toh yanxu xamanin nan wa ke yarda sauro ya shigar masa gida ma balle ya cucesa?" Aunty ta dago Imaan tana kallonta da damuwa tace "Sannu Imaan" Imaan bata iya tace komai ba, Inna tace "Cewa nayi ga abinci ta ci in kai ta asibiti da kaina ta ki ci" Aunty ta dago abincin tace "Ki ci ko kadan ne imaan" tunda Imaan ta ji aroma din miyan, ta dauke kai tana matsawa daga kusa da Aunty, Aunty ta lura da hakan ta mayar da abincin ta ajiye, Inna ta kuma daukowa tace "Ji min mata, ki bata abinci kin mayar kin ajiye, abu dai baxa ayi sbda Allah ba" Imaan na hada ido da abincin for the second time ta mike da sauri tana rike da cikinta tayi hanyar dakin Inna, Aunty ta bi ta da kallo, inna ta saki baki tace "Meye haka kuma?" Jin kakarin amanta Inna ta kalli Aunty tace "Meye ma'anar hakan Amina?" Murmushi kawai Aunty tayi bata ce komai ba ta mike ta bi bayan imaan, Inna dai na xaune rike da abinci baki har lkcn a bude, can ta ajiye plate din ta wuce daki ganin yanda Imaan tayi mata amai a tsakar bandaki ta xauna gefen gado tayi tagumi, Aunty ta cire mata hijab ta ajiye a bucket, ta taimaka mata ta wanke bakinta sannan suka fito bandakin tana mata sannu, Inna tace "Toh aman meye wannan aka kirba min a bandaki duk karni haka? Bandakin da na wanke da hypo biyu daxu, ah gaskiya wannan rashin Imani ne, tana jin amai kuma baxata tafi can tsakar gida ba sai ta juye min shi a bandaki na, sannan ke kuma Amina kin dau hijabi dumu dumu da amai ki sa min a bokitin wanka na, haba jama'ah, wannan rashin kirkin har ina" Aunty dai bata tanka ba ta kwantar da Imaan dake maida numfashi tana mata sannu, Inna tace "Toh wllh Amina ki san yanda xaki yi da bandaki na ban dauko ta don ta cuce ni ba gaskiya, xuciya daya na daukota ganin halin da take ciki, meye kuma xata kaxance min bandaki da amai???" Daga haka inna ta fice daga dakin, Aunty ta koma bandakin don ta gyara mata, ta fito parlor daukan omo Inna dake xaune parlorn ta bi ta da kallo tace "Dama malaria na saka amai Amina?" Murmushi Aunty tayi tace "Gashi kin gani kuwa Inna" Inna tace "Toh Allah ubangiji ya mana tsari da shi, amma gaskiya mujaheed da kyar idan xan iya yafe masa wllh" Aunty ta fita tana dariya kasa kasa. Karfe goma saura Mujaheed ya shigo parlon Inna, har lkcn Imaan na daki tayi bacci, Inna kuma na bandaki tana wankewa bayan wanda Aunty tayi, ya shigo dakin ya nufi kan gadon ya xauna kusa da ita yana kallonta a hankali yace "Imaan" Imaan ta bude ido tana kallonsa yace "Sannu" ta gyada masa kai kawai, xaunar da ita yayi yace "Toh me kike son ci?" Ta girgixa masa kai, da damuwa yace "Noo dole xa ki ji da abinda kike son ci a ranki what is that?" Shiru tayi tana kallonsa, can tace "Ni dai danwake nake so yau" Yace "Ohk toh, bari in gaya ma Aunty ta maki" kwantar da ita yayi ya mike ya fita dakin, ya tafi can part din su gun Aunty, Aunty dake bedroom dinta tace "Ae kuwa babu flour wllh, sai dai kaje ka samu Ammi nasan baxata rasa ba sai tayi mata" yyi maza yace "A'a ni baxan iya xuwa ba Aunty ko xaki aika Maimoon" Aunty ta tabe baki tace "Toh xan kirata a waya" murmushi yyi ya mike yace "Toh ngd aunty" daga haka ya fita dakin, aunty ta kira Ammi, Ammi na dagawa bayan sun gaisa Aunty tace "Kina da flour don Allah" Ammi tace "Ehh baxa a rasa ba" Aunty tace "Toh Imaan xa ki yi ma danwake shi take son ci wai" Ammi tace "Toh bari in duba" daga haka ta katse wayar. Cikin kankanin lkci Ammi ta gama danwaken da farko Maimoon tayi niyyar kira ta kai danwaken amma sbda yanda take son ganin condition din 'yar tata, tayi deciding ta kai da kanta kawai, Inna na xaune Parlor ta sa tuwonta a gaba tana ci, Ta dinga bin Ammi da kallo har Ammi ta xauna ta gaisheta, Inna ta amsa tace "Yar ki kika xo dubawa kenan, ai har na kullaceki nayi xaton baxa ki xo ba don kece ta farko da na fara kira" Ammi tayi murmushi ta ajiye abincin hannunta tace "Ga danwake nan na kawo" Inna tace "Toh gata can, malaria ne ya kusa mata illa Ahmadu yace ba sai na kai ta asibiti ba an riga an kai ta" Ammi tace "Toh Allah ya sauwake" Inna tace "Ameen, mijin ya dai cuce ta jeki ki ganta" mikewa Ammi tayi ta wuce dakin, karasawa tayi kan gadon tana kallon imaan ta cire blanket din jikinta, Imaan ta bude ido, da sauri ta mike ganinta tace "Ammi" sai kuma ta rungumeta, Ammi tayi murmushi lkci daya jikinta yyi sanyi ganin yanda ta rame, Imaan tace "Ammi Ina yini" dago kanta Ammi tayi tace "Ya jikin?" Imaan tace "Da sauki" Ammi tace "Mu je parlor ki ci danwaken na kawo maki" Ta marairaice tace "Ammi ina son inje can bangarenmu mu" Ammi tace "A'a kiyi xaman ki a nan" Inna ce ta shigo dakin tace "Toh ta fito ta ci danwaken tun daxu babu abinda ta saka a baki" Ammi ta mike tana kallon Imaan tace "Sakko mu je ki ci" A plate Ammi ta xuba mata danwaken, Imaan dai sai kallon abincin take, ta dau fork da Ammi ta sa mata ta dau daya a hankali ta kai baki, Ammi ta koma saman kujera ta xauna, Inna dai sai kallon Imaan take tace "Toh ni dai ko wancan mayyar da ya saka ce ta kama jikata ba a sani ba...." Ko rufe baki Inna bata yi ba Imaan ta mike tayi hanyar daki da gudu tana yunkurin amai, Inna ta mike da mamaki tace "Yau naga tsiya, naga jaraba, meye kuma amai amai kamar me ciki? Aman meye kuma wannan take yi?" Mikewa Ammi tayi ta bi bayanta, Inna tayi shiru kamar me naxari, can ta bi bayansu ta shiga dakin da sauri tana xare ido tana kallon Ammi da ta dago Imaan tana mata sannu, tace "Mun shiga uku, Astagafirullah Aisha ko dai ciki ne da Imaan din?" Ammi dai bata kalleta ba kuma bata ce komai ba, Inna dai sai xaxxare ido take tana kallon Imaan dake sauke numfashi Ammi ta karasa shiga bandaki da ita. Inna ta saki salati tana tafe hannu dai dai shigowar Aunty dakin, Inna tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, ta cuce kanta wllh,