← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 292

Sashe 101

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

kamar mai tausayin kasa take tafiya har ta isa gate, Yana ganinta ya bude motar ya fito ya rungume hannayensa yana kallonta daga glass din idonsa, ta sunkuyar da kai har ta isa kusa da motar, cikin sanyayyan murya tace "Ina yini?" Yace "Lafiya lau dear, ya gida?" Tace "Alhmdllh" yace "Baki jin dadi ne, you look pale" tayi murmushi tace "A'a lafiyata lau" yace "To kaka fa, ko xa ki rakani in je in gaisheta" ta xaro ido tace "A'a ai bacci ma take" dariya yyi yace "Sure?" Tayi murmushi bata ce komai ba, yace "Ya Ammi" tace "Lafiyarta lau" yace "I want to take you out for shopping ko tare da cousin sisters din ki ne xata yarda?" Imaan ta xaro ido tace "A'a baxa a bar ni ba" yace "Ohk then" Shiru tayi bata ce komai ba shi ma haka, ta d'an daga kai suka hada ido, da sauri ta dauke kanta, murmushi yyi yace "On Monday xa ku yi resuming third term ss2, I am still counting fa" yar dariya tayi bata ce komai ba, yace "Yea, ss3 kuma term daya kawai xa ku yi shkkn, just few months to go in sha Allah" Imaan dai ba ta ce komai ba ta dinga kallon motar Mujaheed da yyi parking a nan waje maimakon ciki don har mai gadi xai bude gate sai kuma yaga yyi parking a waje, fitowa Mujaheed yyi daga motar kana ganinsa kasan daga asibiti yake, Imaan ta sunkuyar da kanta da sauri, Suna hada ido da Sadeeq har xai shiga gate sai kuma ya fasa ya nufe sa, Sadeeq yyi murmushi ya mika masa hannu hade da masa sallama, Mujaheed ya amsa yace "Ya aiki?" Sadeeq yace "Alhmdllh, wlcm back" d'an murmushi Mujaheed yyi ya juya ya nufi gate, sai bayan da ya shiga ciki Sadeeq na kallon Imaan da mamaki yace "Why didn't you greet him?" Tace "Ba ma shiri yanxu" ya buda ido yace "Why??" Tace "Nothing" Sadeeq yace "Uhn OK, nima daga hospital nake nace let me branch and see you pretty face" Tayi murmushi ta boye fuskarta, wani leda ya ciro ya mika mata, ganin bata ma san yana yi ba sbda fuskarta da ta rufe a hankali yace "Take dear" xame hannunta tayi ganin leda yake mika mata ta xaro ido tace "What?" Yana kallonta affectionately yace "Take plss" bata fuska tayi tace "Aa thank you bana so" yace "Karba plss" tace "Aa Ammina xata min fada" Shiru yyi yana kallonta, ta girgixa kai tace "Wllh Ammina xata min fada" Yace "Toh shikenan" cikin sanyin murya tace "Kayi hakuri" yyi murmushi yace "Na yi, kar Ammi tace kin dade, ki shiga ciki" tace "Toh nagode" Yace "No thanks dear, bari in shiga in gaida kaka" imaan ta xaro ido tace "Ae bata tashi ba" yace "Ehh xan tasheta" daga haka ya nufi cikin gidan ta bi sa da kallo, Inna na bakin tap ya sameta, ta mike tana washe baki tace "Allah sarki Bukari ka xo min gaisuwar juma'ah ne" yana murmushi yace "Ehh kaka" tace "Toh shiga ciki ka xauna, bari in dauraye wajen nan in shigo" yace "Toh kaka" shiga parlon yyi ya xauna, Inna ta gama dauraye daurayenta ta shigo tace "Toh ya mutan gidan Bukar?" Yace "Alhmdllh kaka, dama sauri nake, nace bari in shigo mu gaisa, ga wannan a ajiye ma imaan" ajiye ledan hannunsa yyi, Inna tace "Atoh bari in shiga da shi ciki, Allah yayi albarka" daga haka ta wuce ciki da ledan, sai ga ta ta dawo da bowl dauke da dambun nama, ta shiga kitchen ta dauko leda ta fito ta juye a ciki tace "Gashi nan jiya nayi ni kadai rai na wllh, ko yaran gidan ban tsamma ba ma" Yana murmushi yace "Toh nagode kaka" Imaan ta ajiye abincin hannunta tana kallon inna tace "Ina yini" mikewa inna tayi tace "Jira ni in dauko maki sakon ki, ni dai idan Bukar ya dawo xan ji ko Aisha ce ta hanaki xuwa bangarena yanxu, banda haka taya kina ajiye min abinci sai ki gudu kamar ana koranki, Aisha dai bata isa ta raba ni da ke ba tunda ba ita ta haifa min ubanki ba, idan ma ita ke hure maki kunne duk xan ji idan Bukar ya dawo, ni ba ruwana" imaan ta bi ta da kallo tana tabe baki, bata dau lkci a daki ba ta fito rike da ledan da Sadeeq ya bata tace "Wannan yaron kirkin ne ya xo daxu yace in baki, ko meye a ciki oho, kila wani zinarin ne ma, ni dai ban bude ba don ban gaji cin amana ba" Imaan ta xaro ido tana kallon ledan, can tace "Me yasa kika karba inna?" Inna ta hade rai tace "Toh baxan karba ba? A garin fulanawa kika ga ake maida hannun kyauta baya? Idan baki so sai ki bar min babu abinda ya sha min kai, ni ina so" wani kallo imaan ta mata ta bude ledan, still tayi tana kallon kwalin tsadadden waya da ake yayi, Inna ta saki wani kabbara tace "Toh idan ba Sadeeq din ba dama waye? Wa gare ki banda Allah sai shi din? Ko Bukar baxai siya maki dankareren waya haka ba balle Ahmadu" Imaan dai ta kasa cewa komai gabanta sai faduwa yake, Bude kofar parlon aka yi, Mujaheed ya shigo da sallama hannunsa rike da ledan fruit inna na washe baki tace "Mujaheed kalli wayar da yaron nan Sadeeq ya siya ma Imaan, ni nasan yayi dubu dari biyar" Mujaheed ya ajiye ledan hannunsa yana kallon kwalin wayar, Imaan ta mayar da wayar leda taki yarda ta kallesa ta mika ma Inna tace "Ki ajiye min" inna ta karbi ledan da sauri tace "Toh, nima dai na fiye surutu wllh" daga haka ta mike ta shige daki, Imaan ta mike ta fice daga parlon da sauri. Washegari asabar inna na daki ta ji an bude kofar parlornta ta fito tana tambayar waye, akwatuna taga ana shigowa da, ta saki baki tana kallon akwatunan tace "Meye wannan kuma?"
Chapter 101 · 0% Book details