Sashe 32
Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
na sauran yan matan gidan haka" Umma tace "Toh Ameen amma kuma lafiyayyun yan matan gidan dai koh?" Kawayenta suka kwashe da dariya Anty ta daga kai ta kalli Umma, Wata kawar Umma tace "Gaskiya kam irin wannan kaya ai sai mai lafiya, Mara lafiya kam yyi fatan samun mijin kafin ya sa ran kaya haka" Umma tayi wani dariya har da shewa, Hajiya Mariya da mood dinta ya canxa ta dinga kallon yayartata, ita dai Ammi kallon kayan da suke ta fiddowa kawai take, Umma ta kalli kawarta Hajiya Shafa tace "Ya haka hajjaju naga baki tashi duba kaya ba ko kema kina cikin sahun yan yi ma 'ya ta bakin ciki ne naga dai duk kin aurar da naki yaran" dariya sosai Hajiya Shafa tayi tace "Masu bakin ciki sun san kansu, ni ko in rasa Wanda xan ma bakin ciki rayuwar nan sai ke, jira nake duk a bar wajen In duba kayan a tsanake" Umma ta bata hannu suka tafa tana dariya, maganganu marasu dadi Umma da kawayenta suka dinga saki a parlorn, Anty da abun ya isheta ganin sai xancen mara lafiya suke tace "Ai kuma Hajiya abun fa ba daga nan yake ba, sai a ga kuma mara lafiya ya samu abun arxiki a rayuwa fiye da mai lafiya, so nawa kuma aka yi hakan" wani dariya Umma tayi tace "Toh ayi mu ga ko basilin xai toya kosai" Anty tace "Kwarai kuwa xai toya sai dai a dau lkci kawai" Hajiya Laraba tace "Toh ni duk wannan abun fa har yanxu ban ga amarya ba" Umma tace "Ohh tana can makaranta, gobe xata taho sun ma kusa gama jarabawa" Hajiya Laraba tace "Ayya tana Zarian kenan" Umma tace "In sha Allah" Mikewa Ammi tayi tace "Toh Hajiya Allah ya sanya alkhairi xan je in ci gaba da abinda nake yi" a dakile Hajiya tace "Oh toh madallah, ban ma san an gayyato ki ba da ina da niyyar tura Ummi ta kira ki sai ga ki" Ammi bata tanka ta ba tana kallon Anty tace "Anty Amina, bari inje in ci gaba da girki, kaya sun yi kyau maa sha Allah, Allah ya sanya alkhairi yasa ayi da mu" Anty tace "Toh ameen Ammi sai na shigo" Mikewa Imaan tayi xata bi Ammi Anty tace "Au har xa ki tafi don gulma" murmushi tayi ta shige gaba, daga Umma har kawayenta suka bi su da kallo ana tabe baki. Sai bayan da suka kusa part dinsu Imaan tace "Ammi yaushe ne bikin?" Ammi tace "Me ya hanaki tambayarsu a can" Imaan bata ce komai ba har suka shiga gidan. Da magrib Imaan taje kai ma Inna abinci taga akwatunan jere a parlonta, Inna tace "Kinga akwatunan yar uwar ki kuwa?" Imaan ta girgixa kai tace "A'a ban ga kayan ciki ba" Inna ta mike ta shiga sakko da su tace "Taho ki fiddo su ki gani, ni sai naga kamar ma mijin rufin asiri kawai garesa, ji fa na yarinyar nan Khadijah guda takwas aka kawo har da gwal biyu a ciki wannan kuwa ko axurfa ban gani ba sai dankunnayen kauye" imaan ta rufe baki xata yi dariya inna ta tabe baki ta xauna tace "Toh naga duk sai saurayin ya wani xo ya cika mana kofar gida da katuwar mota, ga kaya nan kuma duk abun kunya, anya ba gudunmawar da dangi suka dinga basa ya xuxxuba mata a akwatunan ba kuwa, ji fa har da man mai gurguwa na gani a ciki, man da aka yi yayi tun lkcn haihuwar Mujaheed" Imaan ta fashe da dariya har da kyakyatawa, Inna tace "Ni daga ganin dankunnayen da sarakuna dama jikina yyi sanyi, atamfofin kuwa har da na roba guda biyu idan dai ba idona ne yyi min karya ba, ga wani uban lace duk nauyin tsiya, sannan jallabiyoyin irin Wanda na taba siya a makka tun ina goyan Ahmadu da naje, bari in fiddo ki gani, ni da dai a kira min yaron inji muguwar da ta hada ma jikata wannan kayan" tana kokarin fiddo jallabiyar Yusuf ya shigo parlon tare da Mujaheed, Inna ta juya tace "Kun ga kayan yar uwar ku kuwa?" Yusuf yace "Na gani sai dai ko M.A" inna ta mike tace "Toh kai isuhu baka ga irin kayan ba, dama katuwar motar karya yake kawo mana kofar gida ya paka?" Yusuf ya bude baki yana kallonta, ta tabe baki ta xauna ta rungume hannu tace "Ni dai ba ruwana, sai kace xa a basa baxawara" Yusuf yace "Haba inna ina laifinsa duk fa kayan masu tsada ne wllh" a fusace Inna tace "Amma kai dai mugu ne wannan yaro, kai ka yarda ka hada ma figalalliyar budurwar nan ta ka wannan kayan, kai kana ganin idan mun kai masu xa su amsa, mutanen da suka jik'a cikin kudi gidansu gari guda motoci ta ko ina, Kai in takaice maka Idan basu koro mu da kayan ba kace ba ni ba" Imaan ta fashe da wani dariya har da kwanciya inna ta fiddo jalabiyyar ta watsa masu kamar xata yi kuka tace "Ku ji fa kayan da na taba siya lkcn ina goyan ubanku a makka" Ganin dariyar da Imaan take Mujaheed ya daure fuska yana kallonta yace "Ke waye kike ma dariya a nan wai" a fusace Inna tace "A'a bar ta tayi wannan ae abun dariya ne, har da fa mai gurguwa da basilin irin na tale tale, bar min ita tayi dariyarta" Tsaki Mujaheed yyi yace "Toh Allah ya sa ta samu hakan ita" A rikice inna ta mike tace "Auxubillahi... Bakin ka ya tsari danyen kashi Mujaheed, kai ka so a kawo ma Imaan irin wannan tarkacen, ai da na shiga uku wllh, bari kaji duk mai auren Imaan sai ya shirya a duniyar nan, idan na amshi akwatunan ta babu gwal na dan kunne, sarka da awarwaro da zobe kace ba ni bace, sannan atamfa idan na amshi na kasa da dubu ashirin kace ba nice Hajiya patu ba, kai in takaice maka idan ba akwatuna sha biyu ba dama kada shegen da ya xo yace xai aureta don xai ga barbadin bala'i" Mujaheed da ke gyada kai ya tabe baki yace "Ae sai ku yi ta xama, kinga sai ki jik'a ta ki shanye ko kiyi kwadonta ki cinye" daga haka ya fice a parlon, Yusuf ya girgixa kai ya fita shi ma, inna tace "Gantalallu kawai yan hassada wanda basa son ci gaba na, a haka xa ku yi ta gantali a titi."