Sashe 18
Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
sauri, yace "Sakko" ba musu ta fito daga motar da kyar, ya dau magungunan da drinks din ya rufe motar, da sauri ya juya ganin kiris ya rage ta fadi ya kara kallon apartment dinsu, kamo hannunta yyi ta jingina jikinsa. Har suka isa bangarensu, ya bude kofar ya shiga parlon hade sallama, Imaan ta kwanta saman kujera ya ajiye drugs din hannunsa da lucozade boost ya kalleta kafin yace komai daddy ya fito parlon, yace "Har kun dawo kenan?" Mujaheed yayi kasa da kai yace "Eh mun dawo Abba" dukawa yyi ya dau ledan maganin ya fiddo gaba daya, ya bude wanda xata sha a lkcn yana kallonta yace "Tashi ki sha magani" Daddy ya tafi kitchen don dauko table water da cup, Mujaheed daure fuska kamar tana ganinsa yace "Baxa ki tashi ba?" A hankali ta bude ido ta mike xaune kamar xata yi kuka, daddy ya iso parlon ya ajiye ruwan da glass cup yace "So how much is the bill doctor" kallonsa Mujaheed yyi, sai kuma yyi murmushi yace "Bill kuma Abba" Daddy yace "Eh ba asibiti ku ka je ba, ga kuma drugs ka siyo" ya girgixa kai yace "A'a Abba, I have settled everything, Allah ya bata lafiya" daddy yace "Toh madalla, Allah ya yi albarka" Mujaheed ya debi ruwan ya mika mata tare da drugs din ta amsa, tana runtse ido ta kai baki sannan ta sha ruwan, mikewa Mujaheed yyi yace "Xan koma daddy Allah ya bata lafiya" Daddy yace "Ameen thanks Son" daga haka ya fita parlon, daddy na kallonta yace "Toh tashi ki shiga ciki ki kwanta" ba musu ta mike ta wuce bedroom dinta. Mujaheed na shiga parlonsu ya kalli mahaifiyarsa dake sakkowa downstairs, kai kana ganin shirin da tayi kasan fita xata yi, Anty dake parlor tana kokarin sa turaren wuta a burner ta kalli Mujaheed tace "Har kun dawo kenan, ya jikin nata?" Gabansa ya fadi sosai, ya hadiye abu da kyar yace "Eh na dawo" Anty tace "Daxu Abban ku ke gaya min ka kai Imaan asibiti, da naga breakfast dinka baka yi ba" kasa cewa komai Mujaheed yyi, ya d'an saci kallon Umma da ta tsaya stairs tana kallonsa baki bude, Anty tace "Ji walakanci ba da Mujaheed nake magana ba" Da kyar yace "Anty ba fa ni na kai ta ba, Abbanta ne ya kai ta" Shiru Anty tayi ganin yanayinsa, can ta saci kallon inda yake kallo, d'an tabe baki tayi ta duka ta ci gaba da abinda take, Umma ta juya ta koma sama, da kyar Mujaheed ya ja kafarsa xuwa dinning, har Anty ta gama abinda take Mujaheed na xaune bai taba komai a dinning table din ba, tace "Idan baka ci ka kai min su kitchen a ba almajirai" ya marairaice yace "Anty da baki yi magana a gaban Hajiya ba" Anty ta maka masa wani kallo tace "tunda uwata ce ita ba" Bai ce komai ba, bayan wani lkci ya mike ya fita parlon ko a mafarki bai ma son haduwarsa da Umma, to me ma xai ce mata ta yadda, part din Inna ya nufa, ya sameta xaune kan tabarma rike da cazbi tana ta xuba gyangyadi, kwanciya yyi kan kujera ya lumshe ido, inna ta yi gyangyadin ta mai isarta sannan ta bude ido, a tsorace ta koma baya ganin sa tace "Meye wannan?" Shi dai bai tanka ta ba bai kuma bude ido ba, tace "Wannan dai ba yi bane ina Lazimi kato ya fado min parlor ba sallama" Ba tare da ya bude ido ba yace "Kina gyangyadi dai" rai bace tace "Ya xaka ce ina gyangyadi ga carbi hannuna, ai asararre ne xai yi gyangyadi a wannan lokacin walha fa na gama ina lazimi ka shigo sadaf sadaf ban sani ba" Mikewa xaune yyi yace "Akwai ruwan shayi?" Tace "Eh akwai wanda uwarka ta kawo min" ya kalleta bai ce komai ba, tace "Can din hanaka ruwan shayin suka yi?" Komawa yyi ya kwanta, tace "Sai dai in sa Aisha ta dafa maka don baxan iya ba, baka ji bayana ba tun safe nake aiki, ko kai baka ga ko ina fess ba, leka dakina ma kaga yanda yake talli" shi dai bai ce mata komai ba, tace "Duk na tattara ma yarinyar nan me shigo min daki ta kwanta ta bar min tsummokaran dankwalayenta idan ta tashi tafiya, suna can baranda na ajiye mata, sai kaga hasken da dakin yyi wllh, ni dai da xata taimaka ta daina shigar min daki don Allah, ni tsoron da nake jiye mata idan tayi aure, ko ina fa ta samu barin kayanta take kamar mahaukaciya, Bukar dai ya haifo abinda ya fi karfinsa" mikewa Mujaheed ya sake yi ya shiga kitchen, ba a dau lkci ba ya fito rike da cup din ruwan xafi yace "Ina kayan shayin?" Makulli ta kunce a habar xaninta ta mika masa tace "Saboda ire iren su Imaan nake adana kayana, ba ruwana" Ya tabe baki ya amshi makullin ya shiga dakinta, closet dinta ya bude yaga gwangwanin madara manya har biyu da milo biyu sai kwalin sugar uku, da kwalin lipton girgixa kai yyi ya sauke madaran da Milo, muryarta yaji a bayansa tace "Da dai ka bari in xuba maka Mujaheed kada ka min barna" Wani kallo ya mata, ya debi cokalin Madara har uku ya xuba, ta bude baki cikin tsawa tace "Kai ubanka ne ya siyo min xaka diba haka, Bukar ne dai mai siyo min kayan shayi, shi Ahmadu sai dai ya jibge min kayan abinci kamar mayunwaciya, kudin nan fa da wahala ake samun su" shi dai bai tanka ta ba har ya gama hada shayin sa ya fita, tayi kwafa ta kwashe kayanta ta maida closet din ta kulle da makullin tana cewa "Ae dai gobe rana ce" Daga haka ta fito parlor. Har kusan azahar Mujaheed na bangaren Inna, har ya gaji da jin muryarta gashi bai taho da earpiece balle ya toshe kunnensa ba. Yana kokarin tashi ya je yyi alwala jin an kira sllh aka bude kofar parlon ya kalli kofar da sauri, Imaan ta shigo parlon rike da warmer, har ta rame ciwon kwana daya sai manyan idanuwa, Inna ta saki baki tace "Wacece wannan kuma?" Imaan bata ko kalleta ba ta ajiye warmer din hannunta, inna ta rike ha6a tace "Ni dai naga abinda ya isheni bai ishi ubangijina ba, yanxu fa sai ace jikinta ne ya tashi, fisabillah dubi yanda yarinya ta zabge ta koma fiyot kamar kyanwa Mujaheed, anya iyayenki na son ki kuwa yar nan, haka xasu xuba ido suyi ta kallonki kina wahala ga magani kasadan na wani malami a Maiduguri ance min babu ciwon da baya warkarwa, dubu hamsin aka ce xa a basa Bukar ya maida ni ban san abinda nake ba kamar shi ya haifeni, ta rasulu kawata xata cuce ni ne ake tunani? ce min fa tayi xata min hanyar samun maganin don can bayan tsauni mutumin yake, kuma babu kalan iskan da bai warkarwa da ciwace ciwacen da ba na Allah da annabi ba irin na yarinyar nan, amma iyayenta sun ba tsinannun turawa karfi sun amince masu dari bisa dari ba saurarana xa su yi ba, dubi don Allah yanda ta fige, lafiya muka rabu jiya amma ga iskan har ya tashi tunda gashi bata je makaranta ba" Mujaheed yace "ina kika ce mai maganin yake" Inna ta gyara xama tayi kasa da murya tace "Wllh a bayan tsauni ta rasulu tace yake, sannan aikinsa yanda kasan yankan wuka, sha ynxu maganin ynxu, duk xata fitsare ciwon da iskan inji ta rasulu" yyi murmushi yace "Ikon Allah, boka ne kenan?" Buda baki tayi tace "Kaji salu6a66e ko, ni dai ka rufa min asiri kar ka ja min kasa Ahmadu ya kafa min sabon babin wa'axi, kai ynxu fata kake inje wajen boka d'an nan" yace "Atoh, mutumin kirki dai baxai je bayan tsauni ya xauna ba" tace "Yo ai ni ce gantalalliya ma da nake xancen nan da kai na mance ashe d'an aiken turawan ne kai ma, Allah wadaran naka ya lalace, ba damuwa ni da ya xame ma dole xanje samo mata magani kuma kada wani shege ya min maganan banxa, Allah kuma ya tsine ma turawan nan dai" Imaan dake tsaye bakin kofa har sannan ta tabe baki tace "Kar ma ki amso ni baxan sha ba, daddy yace min in daina hada na asibiti da gargajiya" a fusace Inna tace "Kya tsufa a gida ina kallonki kina kallona don wllh babu namijin da xai auri ciwo da kudinsa ki karar masa da tattalin arxiki a asibiti, wllh baxan bari a cucesa ba duk sai na xayyane masa lalurorin ki don ni ba yar cin amana bace, ni yar gaskiya ce, ke ce ciwon kafa, kece ciwon baya, ke ce ciwon kai, ke ce ciwon mara, kece sanyin k'ashi, kece xaxxabi, kece ciwon jiki, ga shegen son jiki sannan in rufe masa da cewa duk iska ne da ba a san kansa ba, ba ruwana wllh" murmushi Mujaheed yyi ya mike ya fita don yin alwala, Imaan ta mata wani kallo bata son magana saboda daddy ta juya kawai ta fice mata daga parlonta tana murguda baki.