Sashe 85
Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
ya bude motar ya shiga yana kallonsa yace "Kai dai ka rage munafurci Sadeeq duk rashin jin ka don ka xo gaban surkai sai kayi ta wani sinne kai" Murmushi kawai Sadeeq yyi ya saka glasses dinsa ya tada motar yace "I will have ur time later" daga haka ya fara reverse suka bar layin. Kamar yanda Muhsin ya fada hakan ne ya faru don daddy na shigowa bayan Magrib ya yi ma Ammi bayanin duk abinda ke faruwa, Ammi tayi shiru duk jikinta yyi sanyi, A hankali tace "Toh yanxu ya ake ciki yallabai?" Ya sauke ajiyar xuciya yace "Ina imaan din, taje can barrister na kiran ta" Ammi tace "Ni dai Yallabai da dai a dakatar da yaron gaba daya, imaan har nawa take don Allah" Daddy yace "So kike ki ja mana matsala gun inna kenan, did you know maganar da ya dawo dani weekend kenan, ke kin ga abubuwan da inna ta dinga fadi a parlor kuwa jiya?" Ammi dai bata ce komai ba, Daddy ya girgixa kai yace "Fatanmu mu rabu da ita lafiya, gaba daya ta rikice ne yanxu" murmushi kawai Ammi tayi, Daddy yace "I don't even know me yasa xa ki ba Imaan fuskar kula saurayi at the first place, ko me xaki ce min baxan ta6a yarda baki san da xancen yaron ba, kuma ki wani ce min nawa Imaan take?" Ammi tace "A'a ko da baxa ka yrda ba I have to tell you I know nothing much about the boy, of recent naga tana waya shi ma sai da na mata fada, kai sai kace baka san yar taka bace da nuku nuku" Daddy yace "Wannan ba hujja bace, kina tare da ita 24/7 a gida...." Ammi ta dakatar da shi tace "Toh duk ba wannan ba ita innar da ta kirkiro abun sai a fada mata ta gaya ma yaron lalurorinta... If he wish to be with her like that shikenan, idan kuma baxai iya ba gwara tun wuri a san haka, I don't want my daughter's heart to be broken or anything of such..." Daddy ya dinga mata wani kallo ta mike ta wuce kitchen, yace "Wato you are even in support of the silly thing the girl did, dama nasan kinsan komai ai, tunda aure take so fine I will give her the best wedding ever" Imaan ta marairaice tana kallon Ammi tace "Toh me yasa yake kirana Ammi?" Ammi tayi banxa da ita, a hankali ta mike ta nufi kofa, Ammi tace "Kuma kiyi maxa ki dawo idan ya sallameki ki xo ki kai ma Inna abinci" to kawai tace ta fita parlon. A hankali Imaan ta bude kofar parlorn hade da sallama ta shiga ciki, Umma ce xaune parlor sai Ummi da Rahma, ta dauke xata wuce parlon Abba Umma ta dakatar da ita ta hanyar daka mata tsawa, Imaan ta tsaya amma bata juyo ba, Umma ta mike tana mata kallon tsana karara tace "Uwarki tayi ajiya parlon ne ta aiko ki kixo ki dauka?" Imaan taki cewa komai sai ma dauke kanta da tayi, Xagi Umma ta kunduma mata tace "Kin matsa bakin kofar nan ko sai na faffalleki da mari"