← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 266 OF 292

Sashe 266

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

ke cike da nama ta wuce dinning ta xauna, tana ta xaune can bayan ta d'an ci abincin da xata ci, Hira kawai Mujaheed yake da Hajiya Mariya amma gaba daya hankalinsa na kan Ummar sa da tayi shiru bata cewa komai, can kuma ta mike ta wuce sama ya bi ta da kallo, jin ana kiran Magrib ya mike yace "Xan je masallaci in dawo mum" Hajiya Mariya tace "Toh sai ka dawo" ya kalli imaan sannan ya nufi kofa ya fita, Hajiya Mariya ta mike ta dau plates dake parlon ta kai kitchen ta fito tana kallon Imaan daga inda take xaune tace "Tashi kema kiyi sllh Imaan" Imaan tace "Toh" daga haka ta mike, sbda dadewan da tayi xaune a dinning din sai taji kafarta ya d'an rike mata, haka dai ta daure ta wuce sama, wani dakin daban ta bude ta shiga bandaki tayi alwala, ta fito ta xauna bakin gado, ta kusa minti biyar a xaune aka bude kofar dakin Ummi na tsaye bakin kofa tace "Ance ga darduma can kije kiyi sllh" Mikewa Imaan tayi ta fita dakin tana tafiya a hankali saboda kafarta, dakin Umma ta bude ta shiga da sallama murya can kasa, taga darduman a shimfide ba kowa dakin, ta hau saman darduman ta tada sllhn, tana ta azkar bayan ta idar da sllh Hajiya Mariya ta shigo dakin tace "Imaan ke Mujaheed ke jira xa ku wuce" A hankali Imaan tace "Toh" sannan ta mike ta dauke darduman ta linke ta ajiye, Hajiya Mariya tace "Sai ayi ta hakuri, Allah ya ba ku xaman lafiya" imaan bata iya tace mata komai ganin yanda take tafiya Hajiya Mariya tace "Me ya samu kafar kuma" kamar xata yi kuka tace "Ciwo yake son ya min" Hajiya Mariya tace "Ayya sannu, kun xo da drugs din ki ne?" Imaan ta girgixa mata kai, kama hannunta Hajiya Mariya tayi suka fita dakin, tun da suka sakko mujaheed ke kallonsu haka ma Umma, Hajiya Mariya tace "Wai ciwon kafa take Mujaheed, sai kun fita xaka siya mata magani ko akwai a gida?" Yana kallon Imaan yace "Xa mu siya idan mun fita" Daga haka ya mike ya nufeta yace "Yaushe ya fara maki ciwon?" imaan tace "Daxu" yace "Allah ya sauwake" Komawa gun Umma yayi ya durkusa yace "Xa mu koma kaduna umma, in sha Allah xan xo jibi" Umma tace "Toh Allah ubangiji ya kiyaye hanya ya tsare, Allah ya maka albarka" yace "Ameen Umma ngd" har bakin mota suka rakasu gaba daya, Hajiya Mariya na rike da hannun Imaan dake dingishi ta bude mata front seat ta shiga Imaan ta ce ma Umma sai da safe, Umma tace "Allah ya tashe mu lafiya" Hajiya Mariya ta rufe motar, Umma na kallon Mujaheed tace "Ko a kawo maku aboniki ne?" Yace "Toh Umma" juyawa tayi ta koma cikin gida sai ga ta ta dawo da kwalban man xafin gaba daya ta mika masa ya amsa yace "Mun gode sai da safe" daga haka ya shiga front seat Mai gadi ya bude masa gate ya ja motar sisters dinsa na masa Allah ya kiyaye hanya, sai da ya kusa barin layin yyi parking yana kallon Imaan yace "Sosai kafar ke maki ciwo?" Ta girgixa masa kai tace "Yana dai yi min ciwo" ya dau man xafin ya bude yace "Bari in shafa maki kafin mu kai kaduna in siya maki wanda kike shafawa" Bata ce komai ba ta daga hijab din jikinta da skirt tana yatsine fuska ta juya tana facing dinsa ta daga masa kafar, ya debi man xafin yana shafa mata a legs dinta tana masa kukan shagwaba tana rike hannunsa wai xafi, murmushi kawai yake yana kallonta shi dai bai ce mata komai ba har ya gama shafa mata ta sauke kafarta kasa yace "Sorry wife" ta make kafada tace "Ko dai lil sis" kallonta yyi yace "Koh?" Tace "Ehh" ya gyada mata kai yana murmushi yace "Gaskiya ne, come closer in shafa maki sauran na hannuna a jikin ki" Bai jira cewarta ba ya jawota ya saka hannunsa a hijab dinta ya daga rigar jikinta ya shiga shafa mata both hands dinsa a warm tummy dinta gently in a circular motion, ta xaro ido tana son komawa baya ya ki barin tayi hakan yana kallon fuskarta to see her reaction, da farko kasa cewa komai tayi, can kuma ta rike duk hannunsa kamar xata yi kuka tace "Wllh bana son irin haka yaya, don Allah stop it" Bai saurareta ba har sai da ya kyaleta don kansa yana murmushi, ta turo baki xuciyarta na bugawa har lkcn tana jin kamar hannunsa na jikinta, driving din ya ci gaba da yi yana satan kallonta yana murmushi. Har suka shiga garin kaduna Imaan bacci take tun bayan da suka baro Zaria, yayi parking a wani babban pharmacy yana kallonta ganin yanda take bacci hankali kwance don ya gyara mata kujeran motar, bai tasheta ba ya sauka motar ya rufe sannan ya shiga pharmacy din, duk drugs dinta ya siya mata da na shafawa sannan ya biya kudin ya fito, ya sameta tana bacci har lkcn, rufe motar da yyi bayan ya shiga ne ya tada ta, ta dinga bin inda suke da kallo, yana murmushi yace "Kin gama baccin ki na daren yau kuma yarinya, sae kuma gobe...." Ta gyara xamanta tace "Where are we now?" Yace "Kaduna" daga haka ya tada motar suka bar haraban pharmacy din... Gun masu gashin kaji yayi parking yana kallonta yace "Do you care for some?" Tace "Meye shi?" Yar dariya yyi yace "Kazan kika manta yau?" ta make kafada tace "Ni dai a koshe nake" yace "A'a kin taba ganin inda amarya ta kwana bata ci kaza ba?" imaan ta wani hade rai tace "Ni ba Amarya bace" yace "Xa ki san ke amarya ce yau" daga haka ya sauka motar ta bi sa da kallo, guda daya ya siya sannan ya hada da chill fresh milk da suke siyarwa a wajen, yana dawowa cikin mota ya mika mata, ta ki amsa ta wani daure fuska, ya ajiye yana murmushi bai ce mata komai ba ya tada motar, har suka isa gida fuskarta a daure yake, Mai gadi ya bude masa gate bayan yyi horn ya shiga gidan yyi parking, ya juya yana kallonta, hawaye ya gani makale idonta, sauka yyi motar ya xaga ta side dinta ya bude motar ya kama hannunta ta fito daga motar hawayen dake idonta ya sauko kasa, jawota yyi jikinsa a hankali yace "Yayah ne fa Imaan"
Chapter 266 · 0% Book details