← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 288 OF 292

Sashe 288

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

bai son yayi dariya yace "Ke dai baxa ki daina sa ma mutane ido ba a gidan nan" da sauri Inna ta kallesa tace "Maxa ku fitar min daga parlor ba ruwana, maxa maxa ku fita, kuma wllh kada in sake ganin kafafuwan ku a nan, bari kuma Ahmadu ya dawo, ni dai ba ruwana, tunda uwata ta haifeni ban taba ganin iskanci haka ba, haka ranan ka shige daki ka latse yar mutane saman gadona, wancan ranan kuma ka bi ta har bandaki ban san me ku ke yi ba, idan kuma kitchen ta shiga shi ma ka bita ka datse kofa, to wannan wani irin fitina ne, to kai baka da tsoron Allah ne? Ni dai ba ruwana wllh" Mujaheed na dariya yace "Idan kina sa min ido da ni da matata sai idonki ya tsiyaye nima ba ruwana" d'aga Imaan yayi suka fice daga parlon Inna ta bi su da kallo baki bude. Da daddare Abba ya shigo gaida Inna, ko amsa gaisuwarsa bata yi ba tace "Ahmadu kana ji na??" Abba yace "Ina ji Inna..." Inna tace "A gaskiya ka yi ma d'an ka Mujaheed magana ya dauke matarsa su bar gidan nan, ko kuma in har xa su xauna gidan nan su daina shigo min ni ba gantalalliya bace, don abubuwan da nake gani sun isheni haka, ni dai ba ruwana baxan ce komai ba amma gaskiya ya dauketa tunda mun gama bauta da ita ta samu lafiya sai ma wani tashen fitsara da take min, ko mi ta ci ta bar min shi kaca kaca a parlor duk wari sai dai ni in dauke in share, shi kuma Mujaheed na yi masa uxuri don tun ba yau yake min rashin kunya ba dama can ya rainani, wllh ce min yyi idona xai tsiyaye, to idan idona ya tsiyaye ina lafiya Ahmadu? Naka xai kalli tsabagen idonka ya maka wannan mugun alkaba'i? To ba ruwana kowa yyi ta kansa wllh ba don kai da Bukar ba ni dai babu abinda na hada da Imaan da mutumin nan Mujaheed" Abba dai bai ce komai ba kansa na kasa. Daren ranan Abba ya kira Mujaheed parlonsa yace masa washegari dama ya tabbatar ya dau matar sa su wuce gida tunda mahaifiyarsa suke renawa, sosai Mujaheed ya ji dadin jin haka har ransa amma bai dago kansa dake kasa ba, Abba yace "Sai ka ci gaba da kula da ita, coz abinda take bukata kenan yanxu, if possible a samar mata yar dattijuwa immediately sbda house chores, if there is anything you let me know" kasancewar Washegari lahadi ne da safe Mujaheed ya tafi part din Inna don yasan da kyar Imaan bata can, Xaune ya sameta parlor tana shan shayi da bread leda guda, Inna dake share bakin kofarta tace "Jiya na ajiye maka fura da nono shiru shiru baka dawo ba kuma" yace "Ni da kika kora da matata kuma me xan yi da furan ki" daga haka ya shiga parlon yana kallon Imaan dake kokarin boye bread din da take ci da sauri, yyi dariya yace "I caught you..." Kamar xata yi kuka tace "Ni fa ba duka xan cinye ba fa, nawa ne da na Inna" Inna tace "Karya take Mujaheed, daga wajen uwarta ta taho da shi, ba ruwana tass xata cinye shi, Ni wllh kada ma ta tsiyace min kai da wannan uban cin da take, ni gani nake ma ba na lafiya bane" Mujaheed yace "Toh Ina ruwanki?" Tsayawa Inna tayi tana kallonsa daga bakin kofa. Karfe sha biyu saura Imaan na saka Hijab dinta Ammi ta shigo dakin, tana kallonta tace "Ba abinda xaki tafi da shi" Imaan tace "A'a Ammi" Ammi ta xauna gefen gado tace "Toh na dai gaya maki ki rage ciye ciyen kayan xaki, sannan kuma ki daina wannan shegen son jikin kina kwanciya Kamar ruwa, try and be doing little works, ko da an kai maki mai aikin, sannan wanka kuma da kike yi da ruwan sanyi ki daina" Imaan tayi murmushi tace "Toh Ammi ai na daina" Ammi tace "Toh Allah ya kiyaye hanya" Imaan ta dau handbag dinta tace "Ameen, ai xan dinga xuwa fa bayan kwana biyu ki dinga min irin dambun da kike min" Ammi ta ta6e baki ta mike ta fita dakin, Imaan ta bi bayanta, gun mota ta tadda Mujaheed na jiranta, sai da ta shiga part din Aunty tayi mata sallama tukun tana bobboye cikinta da hijab kamar yanda take yi idan ta ga Aunty, duk gidan banda Aunty da Abba sai Yusuf babu wanda take boye ma ciki, da farkon fitowar cikin tana d'an jin kunyan Amminta tayi ta saka hijab tana takure kanta, amma daga karshe kuma kawai ta sake, amma Inna from day one take tsirara ma a gabanta da cikin, Aunty na murmushi tace "Toh Allah ya kara lafiya daughter, Allah ya kiyaye" Sabbin turaren humra da aka kawo ma Aunty ta debar mata da yawa sannan ta rakota har parlor imaan tayi mata godiya ta fita. Suna hawa saman titi Mujaheed ya kamo hannunta yace "Babu abinda xa a siya maki sweet?" Imaan ta langwabar da kai tace "Ni Ice-cream nake so plss Yaya, Ammi bata bari na sha wanda ka siya min shekaranjiya ba" Mujaheed yace "Toh amma karami xan siya maki sbda kinga garin da sanyi, bana son kina shan ice-cream din nan" Tace "Toh na ji, sai ka siya min har da pizza" ya shafa lap dinta ya kashe mata ido yace "Toh mum twins" ta turo baki tace "Bana so" murmushi yayi bai ce komai ba har suka isa babban eatry din Mujaheed yyi parking ya bude motar ya sauka, ita ma ta sauka a hankali, still tayi tana kallon motar da ya shigo yayi parking gefen motarsu a haraban eatry din...
Chapter 288 · 0% Book details