Sashe 186
Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Umma tayi shiru tana kallon Mummy tana jiran jin abinda xata ce, sai dai fa gabanta faduwa yake, Safeenah da Hajiya Saude ma kallonta suke su ji abinda xata ce, Mummy da tayi shirun kusan minti biyu ta sauke ajiyar xuciya daga karshe tace "Alright, I will look into the matter, nagode da shawara" Umma tace "Atoh, banda mai sonka wa xai kawo maka haka har gida, yanxu xamani ya lalace mutane basu son fadin gaskiya ga ta nan dai kiri kiri ana ganinta, wllh bbu wanda bai san abubuwan nan da na gaya maki ba amma sai mutune su yi gumm su xuba ido, to mu ba mu gaji haka a xuri'ar mu ba gaskiya" Hajiya Saude tace "Wllh ko a gaban uwar yarinyar ce xa mu iya fadin abinda Hajiya Rukayya ta fada maki a nan tunda ba tsoronta mu ke ba, gaskiya ne dai sai mun fada, sam matar bata da hali, makirace ba ta wasa ba, yanxu haka ita gani take ta ci nasara tunda bbu wanda ya isa ya fito ya fadi aibunta duk ta rufe bakin kowa...." Mummy tace "Na ce maku xan yi shawara ai koh?" Umma tace "Toh Allah ya baki ikon yin wanda baxa ki dawo kina da kin sani ba wataran, Allah kuma nuna maki duk abubuwan da muke fada da idon ki, kai ko spy mace ne xa ki iya biya ta dinga shigowa gidan namu taga wainar da ake toyawa, wllh wllh duk ta mallake gidan......" Daga haka ta mike tana murmushi tace "Nagode da lkcn da kika bani Hajiya, Allah ubangiji ya mana xabi nagari..." Tana nuna Safeenah tace "Yar wajen Hon Usman Basiru ce wannan... Kuma surkata ce d'ana na fari ke aurenta, yanxu haka sun kusa wata uku da aure" Mummy na kallon Safeenah tace "Maa sha Allah, that's nyc, Allah ya bada xaman lafiya" Safeenah ta mike tana amsawa da Ameen, Hajiya Saude ma ta mike nan suka yi ma Mummy sallama, Mummy tace "Toh nagode, sai anjima" Umma tace "Mu jima da yawa Hajiya" kofa suka nufa kafin su isa kofar Sadeeq ya shigo parlon, kallon Umma ya dinga yi da mugun mamaki da su Safeenah, Umma ta sunkuyar da kai ta fita parlon su Hajiya Saude na biye da ita, Sadeeq na kallon Mummy ya karasa cikin parlon ya xauna har sannan fuskarsa na dauke da surprise yace "Mum what is she here for??" Mummy tace "It's not necessary you know Sadeeq" ya mike cike da damuwa yace "Why will u say so mum, don Allah ki gaya min me ta xo yi?" Mummy ta mike tace "Nace maka it's not necessary Sadeeq, I am busy upstairs pls" daga haka ta wuce ya bi ta da kallo, a hankali ya koma kan kujera ya xauna ya jinginar da kansa jikin kujeran ya rufe ido xuciyarsa na bugawa. Bayan kwana biyu Sadeeq ya shigo part din mum dinsa ya ganta da sisters dinta da few frnds a parlor suna xuba lafiyayyu kuma tsadaddun kayan lefen da aka yo daga Dubai cikin boxes set shidda sau biyu, sosai boxes din suka yi kyau sannan they look sooo unique kana gani kasan ba da kudin wasa aka siye su ba, Mummy na kallonsa tace "Perfumes da kace xaka Karo fa??" Yana dai tsaye yace "Ohk suna wajen Aunty" ta masa wani kallo tace "Wajen Aunty Kuma?? Me ya kai su can?" Shiru yyi bai ce komai ba, Kawar Mummy Hajiya Farida tace "Toh Aunty ce ta nemo maka mata da xaka bata kudin siyan turarurruka, kai sai samm baka san ciwon kanka ba Sadeeq, kila ma har ka hada yarinyar da ita Auntyn koh?? tunda ga kanwar uwarka" Shi dai bai ce komai ba, ya juya ya fita, Mummy ta bi sa da harara, Hajiya Farida tace "Ni fa ban ji dadin da tasan yarinyar tun a asibiti ba wllh, Bai kamata ta san komai ba a maganar auren nan" Imaan na xaune dinning misalin karfe sha daya na safiyar lahadi tana answering past questions din gabanta kasancewar gobe xa su fara waec, aka bude kofar parlor.... Inna ce ta shigo parlon da sallama Imaan na kallonta har ta karaso ciki tana tabe baki murya can kasa tace "Ko turaren wuta bana jin an sa ma parlon nan yau, dama fa tsafta sai wanda Allah ya so da Rahama yake ba ma, mu dai mun gode masa....." Imaan tace "Toh ba sai ki sa mana ba tunda ba mu sa ba" da sauri Inna ta juya ta kalleta, Bata dai ce komai ba ta xauna saman kujera, Imaan ta ajiye pen din hannunta ta shigo parlon tace "Ina xa ki je da sassafe haka?" Inna tace "Ina xan je kuwa da ya wuce gidan Mujaheed, wa gare ni banda Allah sai shi, jiya fa haka ya xo bashi da isasshen lafiya duk ya rame sai 'yan idanuwa, ya xama wani tsololo da shi sai tsayi kamar pal waya, ni dai ba ruwana wllh, Mujaheed da ko ciwon kai da kyar ka ji yana yi sai gashi duk ya xabge haka kamar ana cin namansa, ni ko nace anya matar nan ba mayya bace aka lika masa ya aura kuwa?? Tun fa da aka yi auren yake a haka yau lafiya gobe babu, toh ni dai yanxu gidan xan tafi idan ma Safara'u mayya ce muna hada ido xan gane, mayu kuma wasu iri ne ba mu kara da su ba a duniya, Ni wllh har dambe nayi da mayya, kuma da kyar idan Safara'u ba mayya bace" Imaan dake kallonta da mamaki tace "Mayya kuma Inna" Inna tace "Oh oh Allah, to idan ba mayya bace mecece, ce min yayi fa bai san me ke damunsa ba da na tsare sa jiya, wllh da barbajin gaskiya a xancena, ni dai duk abinda ya samu Mujaheed ni ya sama kuma baxan xuba ido haka ba, a kan Mujaheed sai duk in tada gidan nan Al-quran, ni bai fiye min kowa sau dubu dari biyar ba aka ce maki, idan xa ki tafi ki shirya ki tafi ki shirya mu tafi gidan yanxu in san abun yi, dama kuma ki taho da takadda da biro duk yanda muka yi da shegiyar matar xa ki rubuta min, don tambayoyi xan mata na dangin uwa da uba, a nan xa a gano tushen abun...." Xaunawa imaan tayi tana kyalkyala dariya sosai, Inna ta wani hade rai tana kallonta tace "Amma ke kam baki da da'a, Meye abun dariya a nan jikana na can rai a hannun Allah, Toh ni fa wllh a kan Mujaheed sai ince a fasa kawo kayanki da sadaki yau ba ruwana, haka kawai jikana ba lafiya xa a cika ma mutane gida da jama'ah... Bari ma in je in sami Ahmadu yanxu tunda ke matar banxa ce baki da mutunci" wani kallo Imaan tayi mata tace "Toh ni ce bani da lafiya da xa a fasa kawo kaya???" Inna ta saki baki tana kallonta, can ta mike tana kwalo ma Ammi kira, Ammi ta fito da sauri tana amsawa, rai bace Inna na nuna mata Imaan tace "Wllh jaraba kika haifa Aisha, mu dai kaf danginmu babu butulu wllh ban dai san ya naku yake ba, gaskiya imaan butulu ce, banda haka kiri kiri ta fito ta nuna ciwon d'an uwanta bai dameta ba saboda tana 6arin jiki tayi aure, baki ta6a xaunar da ita kin bata labarin irin bakar wuyar da Mujaheed ya sha da ita tun tana tsummarta bane wai? Ni dai wllh a dinga jin tsoron Allah, wllh baki xaunar da ita kin sanar mata ba da baxata fifita aure kan d'an uwanta na jini ba, idan ban sa an fasa kawo kaya ba gidan nan yau a kan Mujaheed ace ba ni bace, lefen banxa da hofi jikana ya fi lefe ne, wllh jiya baccin kirki ban yi ba sai da safe bacci ya kwashe ni, ban tashi ba sai daxu na shirya a gurguje na taho ta raka ni gidansa in ga abinda yake ciki, nace to ko ma matar ce mayya xan je in ga" Imaan ta tabe baki tace "Ba fa inda xan je gobe Ina da jarabawa, ko kuma ni likita ce da xan biki...." Inna ta fashe da kuka ta nufi kofa tace "Eh lallai Imaan ta xama jarabar duniya, Bukar ya haifi jaraba, Allah ka mana iyaka da Butulu duk inda yake.... Bari naje in samu Ahmadu ai na fi ki tsiya yau" daga haka ta fice daga parlon, Imaan na turo baki ta juya xata koma dinning Ammi tace "Wuce ki shirya ki bi ta ku tafi" ta juyo da sauri kamar xata yi kuka tace "Ammi karatu fa nake, ni wllh bana son xuwa gidan Yaya..." Ammi ta hade rai tace "Musu xa ki tsaya yi da ni kenan?" Lkci daya hawaye ya kawo idonta ta wuce dakinta, atamfa riga da skirt ta fiddo ta saka bayan ta feshe jikinta da turare, ta goga chappete a bakinta ta sa gogaggen Hijab dinta har kasa ta fito parlor rike da wayarta da karamin jaka, Ammi dake xaune parlor ta bi ta da ido, a hankali tace "Ammi sai mun dawo" Ammi tace "Allah ya kiyaye, you pray before leaving" Imaan ta gyada mata kai ta nufi bakin kofa tana karanto addu'ar fita gida a ranta. Part din su Maimoon ta nufa ta bude parlon ta shiga a hankali, ko karasawa cikin parlon bata yi ba ta dinga jin Muryar Inna a parlon Abba tana cewa "Gaba daya Imaan ta banu ta lalace, sam bata da kirki yanxu, amma abinda ya ban tsoro shine yanda aka boye mata wuyar da Mujaheed ya sha a kanta, bata fa yarda da kowa a lkcn sai shi sai uwar, duk ta fitsare masa jiki, har uban nata Bukar tsoron sa take... Toh meye kuma lkci daya sai yarinya ta xama jarababba mara Imani, ni ka ma kira min Bukar din in ji ko su ke koya mata, dariya fa ta dinga ba66akawa daga nace mata Mujaheed ba lafiya xan je gidansa, ni wllh na gaji da imaan a gidan nan" shi dai Abba bai ce komai ba kansa na kasa yana sauraranta, ta tabe baki tace "Ni dai