← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 244 OF 292

Sashe 244

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Yaya xai kawo ni yanxu ae kina gida koh?" Farida tace "Ehh Ina nan, bari in turo" imaan ta katse wayar tana kallon mujaheed dake driving idonsa a kan titi, yace "Xa mu yi baki daga kd fa" Imaan tace "Su waye?" text din farida na shigo wayar hannunta ta bude tana kallon address din sannan ta nuna masa, ya kalli wayar sannan yace "Baxa ki bari gobe in kai ki ba?" A takaice tace "Noo" yyi murmushi ya dau hanyar unguwar da Farida ta turo, tafiyar kusan minti sha biyar suka yi suka iso layin, yyi parking dai dai house number din, Imaan tayi dialing number din Farida tana dagawa tace "Aunty ina waje" Farida tace "To ki shigo ciki ina ce tare ku ke da Mujaheed din?" Imaan tace "Ehh tare mu ke" Farida tace "Toh ku shigo sai su gaisa da Mai gidan yana nan" Imaan tace "Toh" sannan ta kalli Mujaheed, yace "Ki shiga ki fito ina jiran ki" tace "Baxa ka shiga ba?" Yace "Yes" ta hade rai tace "Ayya, ita fa da kanta tace xa ku gaisa da mai gidanta, or are you feeling anything deep down?" Ya kalleta da mamaki yace "Like what?" Ta wara masa ido tana murmushi tace "Like kishi or so" Yar dariya yyi bai shirya yin hakan ba yace "Not when I am having you" turo baki tayi tace "Not when you have ur wife dai" ya ja hancinta yace "And you are the wife koh" ta make kafada tace "Ni ba matarka bace, matarka na gida" daga haka ta fita motar, ya sakko shi ma yana kallonta yace "Toh xa mu raba wannan gardaman anjima da daddare" da sauri ta kallesa amma bata ce komai ba ta nufi gate din gidan ya bi bayanta yana murmushi, Mai gadi ne ya bude masu gate din suka shiga, Mujaheed ya tsaya compound din gidan yace "I will wait here" Imaan ta tafi kofar shiga parlon ta danna bell, Farida ta bude kofar ganinta tayi murmushi sosai tace "Welcm imaan ina yayan naki?" Imaan ta mayar mata da murmushin tace "Wai baxai shigo ba yana waje" Farida tace "Na xata da aunt din ta ki xa ku xo ai" Imaan tayi yake tace "Ya ajiyeta a wani anguwa ne" Farida da ta hango Mujaheed tace "Dr ka shigo mana xa ku gaisa da Mai gidan ne" Mujaheed yace "Ohk" daga haka ya fara tahowa, Farida ta kama hannun Imaan suka shiga ciki, tarba sosai Farida da mijinta suka yi masu, Mijinta Dr Khaleel na kallon Mujaheed yace "Toh ya madam baku xo da ita ba su yi xumunci da Farida.. " Mujaheed ya d'an yi murmushi yana kallon Imaan, Imaan ta d'an marairaice masa tana girgixa masa kai a hankali alamar kada yace komai, Farida dai sai kallonsu take haka ma mijin nata, Mujaheed ya shafa kansa still smiling yace "Gata nan xaune ai" Farida ta dinga kallon Imaan da mamaki ko kiftawa babu, Mijin yace "Maa sha Allah, auren xumunci kenan ku ka yi, Farida ce min tayi sistern ka ce" Mujaheed ya gyada masa kai yace "Sure, auren gida ne" Farida dai sai kallon Imaan da taki dago kai take ta kasa cewa komai, Nan dai Mujaheed da ko a jikinsa suka dinga fira da mijin Farida, Farida ta mike daga karshe tana kallon Imaan a hankali tace "Mu tafi ciki Imaan" mikewa Imaan tayi Mujaheed ya bi ta da kallo yana murmushi ta balla masa harara kamar xata yi kuka ta bi bayan Farida, suna shiga daki Farida ta kulle kofa ta juyo tana kallon Imaan da sauri tace "Da gaske mijin ki ne Mujaheed yanxu Imaan?" Imaan ta kasa cewa komai lkci daya hawaye ya kawo idonta, Rungume ta Farida tayi cike da murna tace "Kai, amma i am very happy for Imaan, kinyi dacen miji Imaan...." Imaan dai bata ce mata komai ba hawayen dake idonta ya sakko Farida na kallonta da mamaki tace "Kuka kuma? Baki son auren ne Imaan?" Imaan ta xauna gefen gado tana goge hawayen idonta tace "Fasa aure na aka yi aka hadani da Yaya..." Farida ta dawo gefenta tana kallonta cike da mamaki da kuma tausayi tace "Allah sarki, ban ji labarin ma Imaan, but put this in mind Mujaheed shine mafi alkhairi gare ki shi yasa hakan ya faru Imaan, kin fi kowa sanin halin Mujaheed fa..." Imaan ta fashe da kuka tace "To amma yaya na kuma Anty Farida?" Farida bata san lkcn da tayi dariya ba sosai ta kamo hannunta tace "Toh ai ya fi dadi irin wannan auren Imaan, Kinga sai kiyi ta xuba masa shagwaba kamar yanda kike masabda hujja yanxu...." Imaan ta marairaice tace "Allah Aunty kunya fa nake ji" Farida tayi murmushi tace "Imaan kenan, kin san da dadewa na taba tunanin anya ba sonki Mujaheed yake ba, coz care din da yake baki is too much, kuma har muka rabu da Mujaheed ban taba kin yarda cewar baya son ki ba, ni nasan akwai abu a xuciyarsa game da ke, may be saboda mum dinsa yayi ta boyewa, amma ban taba jin kishin ki dai dai da na rana daya ba, cikin kaninsa ma duk mun fi sabawa da ke, sai ranan da ya xo gidanmu na karshe yake ce min kilan wataran ya hada ni da kanwata, nasan kuma ke yake nufi a lkcn" Imaan dai sai kallonta take, Farida tace "Amma sun rabu da matar da Ummarsa ke son ya aura koh??" Imaan ta tabe baki tace "Tana nan, tare ma muke yanxu, wllh Aunty Farida bana sonta" Farida ta xaro ido tana kallonta, can tace "Tana nan?? To yau kwananku nawa da auren?" Imaan tace "Gobe Friday sati daya, amma yau kwanan mu daya a Zaria" Farida tace "Kwananki nawa da tarewa?" Shiru Imaan tayi sannan a hankali tace "Just two..." Farida tayi murmushi tace "Toh ai babu xancen wani kunya tsakanin ki da Yaya yanxu koh?"
Chapter 244 · 0% Book details