Sashe 72
Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
maka jama'ah, uban me ka xo min??" Mujaheed yayi dariya yace "Haba dai mai gidan kuma kike kora yau inna?" A fusace tace "Yana kabari, tun raina bai baci ba Mujaheed ka fita" Mujaheed yace "Abba ne fa yace kada mu tafi dake Inna" ta buda baki tana kallonsa tace "Kai haba?" Yace "Xan maki karya ne" xauna wa tayi tace "Ikon Allah, shi Ahmadun yace ku tafi ku bar ni kenan, to ya ma kansa kuwa, shine har da shi a bani hakuri da masu gadi a tsakar gida daxu, har hawaye fa sai da na xubar" Mujaheed yyi murmushi ya kwanta kan kujera, Inna tace "Toh ae shikenan, ya jikin Imaan din?" Yace "Da sauki" inna tace "Kuma da gasken bata da lafiya Mujaheed? Naga kamar don kar aje kauyen da ita yasa ta langwabe fa" Mujaheed yace "Ni dai akwai abinci?" Tace "Gashi can wanda Aisha ta kawo min ne daxu, bai wuce shinkafa da miya ba, Idan kuma biskit xa ka ci ga su can iri iri a daki wanda aka kawo ma Imaan, Kazan ma daxu na dumama na karasa cinyewa..." Mikewa xaune Mujaheed yyi yana kallonta na kusan second goma, can yace "Wa ya kawo mata?" shiru Inna tayi kanta a kasa, can ta saci kallonsa suna hada ido tace "Yo wa gareta banda Bukar??" tana fadin haka ta mike ta shige daki.... Imaan ta fi minti biyu tsaye bakin kofar bedroom din Ammi ta kasa shiga don bata san me xata ce mata ba, bude kofar dakin aka yi ta ja baya da sauri, Ammi ta dinga kallonta tace "Meye haka kike yi a bakin kofa ta?" Ta fara kame kame ba tare da ta kalli Ammi ba, Ammi tace "Imaan" daga kai tayi ta kalleta kamar xata yi kuka, Ammi tayi kasa da murya tace "Tell me what you want" tana jan fingers dinta a hankali tace "Ammi dama... Dama Sadeeq ne yace min yana waje ya xo gaisheni" Ammi ta dinga kallonta tace "Waye Sadeeq" ta sunkuyar da kai tace "Abokin ya Muhsin" Ammi ta yi shiru, can tace "Toh kar ki dade" Ta d'an yi murmushi tace "Toh nagode Ammi" daga haka ta saka Hijab dinta ta fito don tun da aka yi la'asar Sadeeq ke waje amma ta rasa yanda xata sanar ma Ammi ta fita, sosai hankalinta ya kwanta ganin ba motar Mujaheed a parking space, kamar mai tausayin kasa ta fita kofar gida, Tsaye ta ga Sadeeq jikin motarsa ya rungume hannunsa, as usual sanye da spec dinsa, dogon hancinsa da cute millionaires belt dinsa shine first abinda xaka fara noticing a fuskarsa daga nisa, Ta sunkuyar da kanta har ta isa inda yake tsaye, kallonta yake daga cikin glass din idonsa ko kiftawa babu, murya can kasa tace "Ina yini?" Yyi murmushin da ya bayyan dimples dinsa ya cire glass dinsa yace "Lafiya lau Imaan ya jikin?" A hankali tace "Na ji sauki" yace "Sure??" Ta gyada masa kai, yace "Toh Allah ya kara lafiya, hope kin sha dosage na afternoon, I mean ur drugs?" Ta gyada masa kai tace "Na sha" yace "Good, ya mama fa?" Tace "She's inside" ya langwabar da kai yace "Yaushe xan xo gaisheta pls" ta xaro ido tace "A'a xan ce kana gaisheta" cikin sanyin murya yace "Ke dai baki son yan gidanku su san ni koh?" xata yi magana aka bude gate, Inna ce tsaye bakin gate din tana kallon mai gadi tace "Kai iliya kake ko ilu, Kasan kan waya kuwa? Hadiza xa a kira min duk ba kowa gidan sai mai laluran can kuma nasan tana can tana bacci yanxu haka, yaran duk sun tafi kauye sai gobe xa su dawo" Imaan tayi stiff inda take bayan gabanta yayi mugun faduwa jin muryar inna, Mai gadin ya mike da sauri ya amshi wayar yace "Toh Hajiya...." Buda baki inna tayi tana kallonsa tace "Eh lallai baka da da'a, banda barbada kace ma matan gidan Hajiya nima kace min Hajiya, to bari kaji ko wa enda suka dauke ka aiki ma inna suke ce min balle kai, bar gani na haka xuciya mai kyau da rikon gaskiya da amana yasa ka gan ni har yanxu da kyau na, amma wllh da kyar idan ban girmi wanda ya haifi kakanka ba ma" yayi kasa da kai yana murmushi sosai yace "Yi hakuri Baaba tuba nake" inna tace "Kaji min yaro dai" Imaan dai ta kasa tsaye waje daya tayi backing din inna xuciyarta sai bugawa yake, murya can kasa Sadeeq yace "Ur grandmum?" ta gyada masa kai a hankali, kamar ance inna ta daga kai ta gan su, sake baki tayi ta kalli mai gadin tace "Kai wancan ba Imaan bace nake gani a tsaye?" Yace "Ita ce Baaba" Sadeeq yace "Let me go and greet her tunda ta gan mu" imaan dai kasa cewa komai tayi, ta ji kamar ta fashe da kuka, ae kuma shikenan.... Sadeeq na isa gun Inna dake ta kallonsa ya risina ya gaidata da ladabi, tace "Kai ne sabon saurayin nata?" Murmushi Sadeeq yyi ya kasa cewa komai, Inna tace "Ikon Allah, Kai ni fa na haifi ubanta Bukar, jikata ce fa, ita kenan Allah ya ba Bukar fa, a hannuna fa aka haifeta wllh, yanxu d'an nan da ban fito na gan ku ba shikenan, kai a garin ku haka ake yi?? ko bata ce maka kakarta na da rai bane, ita tunda bata da hankalin cewa ka shigo ka gaisheni kai baxa ka yi tunani ka shigo ba, dubi fa yanda ta ji kunya ta kasa juyowa kamar warce ruwa ya cinye" Sadeeq dai sai murmushi yake yace "Dama ai xan shiga in gaida ki kaka, kiyi hakuri" inna tace "Ni dai ba ruwana a dinga abu saboda Allah, tunda dai na kama ka mu je ciki" Yana murmushi ya bi bayanta suka shiga compound din ta rufe gate, tana nuna masa bangaren su Mujaheed tace "Kaga wancan katon ginin?" Yace "Na gani kaka" tace "Toh na wan ubanta ne, barrister suke ce masa, a India yayi karatun lauyancin sa, matansa biyu sai 'ya ya bakwai, Mujaheed shine d'an sa na fari, ina tsaye bakin kofar asibiti aka haifesa, yana nan xaka gansa wani lafcece dogo, da yake ada yana daga wannan karafunan turawan, to da kyar dai Ahmadu ya raba sa da su, nima na dinga rokon Allah har ya daina, a gabana fa ya girma, tun yaye yake wajena iyayen suka bar min, yana gama sakandari dama babansa ya biya masa kudin karatun likita a turai, ai ko in gaya maka babu irin fitsarar da bai koyo a can ba gaskiya, ni dai lkcn da ya dawo ma tsoron sa nake ga wani uban gashi da ya tara, buduwar da xai aura ma yar hayi ce, to sai kaninsa Yusuf, xaka gansa shi kuma wani lagwai lagwai kamar ya karye malam, da ma muka samu ya d'an yi kauri yanxu, sai kaga yanda aka haifesa d'an fiyot, to sauran kuma duk mata ne" Murmushi kawai Sadeeq ke yi yana bin inna, inna ta nuna masa part din su Imaan tace "Toh kaga wannan bangaren na su Imaan ne, Ubanta a can Habuja wajen neman abincinsa yake, ita kadai Allah ya basa a duniya, to dai ya fi babu d'an agwai da bak'in da, uwarta na nan wata bafillatana sai kirki, toh ni kuma kaga akurkin da suka gina min nake rayuwa ciki" ta fadi haka tana nuna masa nata part din.