← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 292

Sashe 58

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ne xaka ce min ba can kayi ba, jika na ne fa ya watsar da mu a titi yanxun nan yyi wucewarsa daga nayi ma katuwar uwarsa gyara, banda haka yaushe xaka gan ni bakin titi tsaye da gata na, motocin 'ya yana sun fi biyar wllh, ko da yake in mun je gidan ma xaka gane abinda nake nufi, ko kai so kake inyi ta tsayuwa kamar yar iska bakin titi?" Shiru yyi bai ce komai ba, Inna ta kalli su Imaan sannan ta kallesa tace "Yaro idan baxa su shiga ba ja ni ka kai ni gida, su kuma Allah ya kawo masu mafita, mu je ni dai" murmushi mai napep din yyi, Imaan ta turo baki ta shiga Maimoon ma ta shiga, inna tace "Atoh da kun tsaya jiran d'an sahun da xai je ku kwana a wajen" suna isa gida dama inna ta sauka napep din ta nufi gate tana gyara yafin mayafinta, Maimoon ta kalli Imaan dake dariya ta ja tsaki ta bude jakarta ta fiddo dubu daya ta basa ya bata canji ta wuce ciki, can suka ga inna har ta shige parlon su Maimoon, Imaan ta nufi part din su Maimoon ta bi bayan Inna, babu kowa parlon Abba hakan yasa inna ta dawo main parlor tana kallon mutanen da ta wuce da farko tace "Ahmadu baya nan ne" Daga kitchen Aunty ta leko tace "Bai shigo ba inna, kun dawo lafiya?" inna bata tanka ta ba ta fice parlon, bata tsaya ko ina ba sai part din su Imaan, ba kowa parlon sai kamshi dake ta tashi, cikin daga murya inna tace "Salama alaikum" Imaan ta bude kofar bedroom dinta tana lekowa, Inna tace "Ina Bukar din?" Daddy ya fito daga daki yace "Har kun dawo inna" karasawa cikin parlon tayi ko takalmanta bata cire ba ta xauna saman kujera tana share guntun hawayen idonta, Ammi dama na jin irin sallamar da inna tayi tasan ba lafiya don haka bata fito ba, duk xaton ta k'aran imaan ta kawo, Imaan da har ta cire kayanta ta sa Hijab kawai ta fito da sauri, Daddy na kallon inna a hankali yace "In ji dai lafiya inna" a fusace tace "Ina fa lafiya Bukar, shegen d'an ku ya watsar da ni tsakiyar titi gefen jaji yayi wucewarsa, daga nayi ma Rukayya gyara" Shiru Daddy yyi yana kallonta da mamaki, ta fashe da kuka tace "Gaskiya Bukar idan ba a bi min hakkina ba yau duk a station xa mu kwana gwara in kai karar can a bi min hakkina, da girmana da matsayina da martabata Mujaheed xai juye ni tsakar titi yyi wucewarsa?? Ae wannan babban magana ce wllh" Daddy ya sauke ajiyar xuciya yace "Subhanallah me ke damun Mujaheed haka" Inna ta tsaida kukan da take tace "Toh ai ba ni xaka ma tambayar ba, waya xaka dauka yanxu ka kirasa, kada ma ka nuna masa ina nan, kawai ce masa xaka yi ya xo xaka aikesa yanxun nan, daga nan sai kaji me ke damunsa ko wiwi ya fara sha bamu sani ba" Daddy ya kara sauke ajiyar xuciya, inna tace "Sae wani sauke sauken ajiyar xuciya kake Bukar, ko tsoron sa kake ne inyi ta kai na?" Yar dariya kawai daddy yayi ya dau wayarsa, inna ta tsuke fuska tace "Wllh yanda ya min tijara a kan uwarsa kai ma haka xaka masa tijara akan taka uwar, kuma idan baka ce masa aikensa xaka yi ba wllh baxai xo ba nan kuma xa mu kwasa mu tafi police station " Daddy dai bai ce komai ba yayi dialing number Mujaheed ba a dau lkci yana ringing ba ya daga, Daddy yace "Muhammad kana kusa ne?" Daga daya bangaren Mujaheed yace "Eh Abba" daddy yace "Toh ka xo parlor na yanxu" Mujaheed ya d'an yi shiru, kafin yace "Toh Abba" Daddy yace "Don't keep me waiting fa naji kayi shiru ko baka kusa ne?" Yace "Ina nan" Daddy yace "To ina xaune ina jiranka yanxu" Mujaheed yace "Toh" daga haka daddy ya katse wayar, inna tace "Kai xaka kwana a ciki wllh idan yaron nan bai xo ba Bukar" Daddy dai bai ce komai ba, Mujaheed ba don yanda yake jin kunyar daddy ba da fa ba xai je ba don yasan sarai inna na can, kuma da Abbansa ne ma ya kirasa ba lallai yaje ba, jallabiyarsa kawai ya xura ya fita dakinsa, banda girgixa kafa babu abinda inna take, da sallama ya shiga parlon, ba tare da ya kalli Daddy ko ita ba ya tafi ya xauna kasan lallausan carpet din parlon yace "Barka da dare Abba" Daddy yace "What happened between you and ur grandma yanxu?" Mujaheed ya daga kai yana kallonta yaga yanda ta wani tsuke fuska tana kallon sa, ya maida kansa kasa, inna na nuna Imaan dake kwance kan kujera tana kallonsu tace "Idan sharri na masa ga 'yar ka kwance kusa da kai ka tambayeta ka ji ko ba tsakiyar titi ya juye mu ba" Daddy ya juya ya kalli Imaan, a fusace Inna tace "Ke tashi xaune ki basa labarin abinda ya faru, ba tsakiyar titi Mujaheed ya sauke mu ba, naga kamar tantama Bukar yake" Imaan ta mike xaune tace "A'a ba fa tsakiyar titi bane inna, gefen hanya ne....." Rai bace Inna tace "Amma wannan anyi shegiyar 'ya... Dama akwai bambanci tsakanin gefen titi da tsakar titi, ke dai munafuka ce wllh" Imaan ta harareta ta gefen ido tana turo baki ta koma ta kwanta, Inna tace "Wllh Bukar gefen hanya yayi watsi damu, kuma kafin ya sauke ni don Allah mai yace min Imaan" da sauri Imaan ta daga hannu tace "A'a ba ruwana nima ban sani ba" Bude baki inna tayi tana kallonta, daddy yace "Yanxu dai ki tashi ki tafi ki bar ni da shi inna" inna tace "In tashi in tafi ka basa hakuri shima ya tafi xaka ce min" Tana fadin haka ta mike tace "Tun farko ma ban san me ya kawo ni gun Bukar ba, duk inda Ubansa ya tafi ai ya ci ace ya dawo yanxu" daga haka ta fice parlon fuska daure. Daddy ya hade rai yana kallon Mujaheed yace "Saboda baka da kirki xaka ajiye su bakin hanya Muhammad?" Mujaheed yyi kasa da kai bai ce komai ba, Daddy yace "Yanxu ka kyauta kenan, idan Hajiyar ka ce ko min abinda tayi maka xaka mata haka?" Yace "Kayi hakuri Abba" Daddy yace "Haba Muhammad, I am highly disappointed at you, this is very rude and stupid of you, she is our mother fa, no matter how she behaves baxa mu canxa ta ba" Mujaheed bai iya cewa komai ba, daddy yace "Ka tashi ka bi ta ka bata hakuri yanxu" yace "Toh, ayi hakuri Abba" Daddy ya kalli imaan yace "Ke kuma I've warned you times without number ki daina fada mata magana anyhow amma baki ji ko, xan fara sa6a maki soon wllh idan baxa ki canxa naughty attitude din nan ba, will you dare talk to ur mother that way?" mikewa xaune tayi kamar xata yi kuka, Mujaheed ya tashi yace "Xan je in sameta yanxu Abba" daga haka ya fita parlon. Washegari da safe da kyar imaan ta tashi tayi wanka tayi breakfast da Ammi ta ajiye mata a dinning, Ammi tace "Idan kin gama ki dau magungunanki ki sha kada in tuna maki, kuma da Ac kika kwana ko?" Ta xaro ido tace "Ammi wllh A'a" Ammi tace "Toh ga mura nan na shirin kama ki" Ta langwabar da kai tace "Jiya fa da daddare a napep muka dawo, kin ji sanyi kamar xanyi freeze a hanya" Ammi ta fiddo kindirmo a fridge yayi sanyi sosai ta ajiye mata a dinning din tace "Gashi ki kai ma inna inji daddyn ki, you make sure kin goge min dinning table idan yayi stain" Ta marairaice tace "Ammi my legs are aching me fa" Ammi ta harareta ta wuce dakin ta, Imaan na gama breakfast ta tashi ta dau kindirmon ta tafi kai ma inna, Tana shiga parlon bayan ta ajiye tana kallon inna dake ta kukkula dubulan da cin cin a leda sai ga Umma ta shigo parlon da sallama, Inna ta kalleta ta ci gaba da abinda take ta amsa sallaman ba yabo ba fallasa, Umma ta dafa kujera tace "Ina kwana inna" inna tace "Lafiya lau" Umma tace "Ya gajiyan taro" inna tace "Bana tare da gajiya duk ya bi lafiyar gado" Umma tace "Toh Alhmdllh Allah ya saka da alkhairi yaji k'an mahaifa" inna tace "Ameen" karasawa tayi kusa da inna ta ajiye ledan hannunta tace "Ga wannan dai ba yawa" inna na kallon ledan tace "Meye wannan din? Ke imaan xo ki bude" imaan dake xaune ta mike ta karasa kusa da Inna, Umma ta bi ta da kallon gefen ido, durkusawa tayi ta bude ledan ta ciro atamfa da pack din sabulu guda biyu da turare mai tsada" Inna ta bude atamfar tana kallo da kyau, tace "Holland ce wannan din?" Umma tace "Ehh" inna ta tabe baki tace "Toh, da dai basirar ki ce hakan da sai ince Allah yyi albarka, amma wannan ko kaffara baxan yi ba Ahmadu ya sa ki, Allah ya masa albarka ya kare min shi duk inda xai shiga, Allah ya ci gaba da hada kansu da d'an uwansa Bukar ya raya mai 'ya yansa yayi masu albarka, ita kuma wannan da ya aurar Allah xaunar da ita da mijinta lfya, ke kuma nagode da isar da sako" Umma ta dinga kallonta ko kiftawa babu, Imaan sai danne dariyarta take, Inna ta ci gaba da kulla dubulan dinta a leda, Umma tace "Sai anjima" inna tace "Mu jima da yawa" daga haka ta nufi kofa, inna na kallon Imaan tace "To ke sai kiyi ta kanki, don wllh jiya Mujaheed ce min yyi xai kakkarya ki ya xane ki, wai ya ganki da wani mai mota a tsaye a kofar gidan seeyama, imaan ina kuma kika samo mai mota kike ta boye min ban sani ba ni Asabe??" Umma ta d'an dakata bakin kofa jin abinda inna ke cewa, Imaan ta turo baki tace "Shi sa ma xan tashi in tafi yanxu kar ya xo nan, to har
Chapter 58 · 0% Book details