← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 164 OF 292

Sashe 164

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

taho gun su da sauri kafin imaan da ta wani 6ata fuska tana kallon umma tace komai yace "Noo Bata aka yi as gift na walima shine ta ke nuna min" Wani mugun kallo umma ta watsa masa tace "Take nuna maka kayi mata me, don tana karuwanci an bata laptop kuma sai ta taho nuna maka?" Da mamaki yake kallon Umma yace "Haba Umma, why all this" tsawa ta masa tace "Questioning dina kake yi? Sharri nayi mata ba iskancin take ba, ai wllh ko qur'ani xan iya dafawa in rantse iskanci take yi, ance maku a banxa yaron nan ke kashe mata kudi, ai kawai sai dai Allah ya shirya mana xuri'a, amma sai ta kawo wani shegen laptop ta nuna maka kayi uban me da shi??" Imaan dai kallon umma kawai take hawaye cike idonta, Hajiya Saude ta karbi laptop din tace "Lallai kam Allah ya shirya mana xuri'a amma dama waye bai san 'ya yan masu kudin nan ba" Mika ma imaan laptop din tayi tace "Karbi, Allah kuma ya shirye ki" Imaan taki amsar laptop din hawaye ya cika idonta, Umma tace "Sake mata tsiyarta mu wuce idan baxa ta amsa ba" daga haka umma ta wuce, Mujaheed ya sa hannu ya amshi laptop din hannun Hajiya Saude, ta bi bayan umma tana kyabe baki, Imaan ta fashe da kuka tana kallonsa, Bin uwar tasa yyi da kallo xuciyarsa na tafarfasa shi ma, har suka fita gate, kamo hannunta yayi ya wuce bayan apartment dinsu da ita suka tsaya cikin lallashi yace "Stop those tears imaan, she only said that to please her self, eraze her talk off ur mind now" shessheka ta fara yi, ya hade rai yace "Baxa ki daina kukan ba" goge idonta ta fara yi, ya sa hannunsa yana share mata idanuwan nata, murmushi yyi murya can kasa yace "You are taking ur pride to it rightful place in sha Allah Lil sis" turo baki tayi, sai ta basa dariya ya ja hancinta a hankali yace "My pretty stubborn Lil sis" ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, Mika mata laptop din yyi ta amsa yace "Yi wucewar ki ciki, on Sunday sai ku xo gidana tare da Inna in baki sauran gift din ki" make kafada tayi tana turo baki, yace "Why??" Ta wani hade rai tace "I dislike ur wife, I don't know.... I just don't like her" kasa cewa komai yyi yana kallonta, can a hankali yace "But it's also ur home, gidana ai naki ne" tace "Toh ai ita bata san haka ba, ko baka gaya mata bane" Dariya sosai ta basa don sae da yyi, ta tabe baki tace "Ni dai bana sonta kwata kwata" ya sauke ajiyar xuciya yace "Toh ni xan xo in dauke ku da kai na" imaan tace "Toh, kasan me Sadeeq ya bani" shiru yyi yana kallonta, lkci daya mood dinsa ya canxa, can dai yace "Waye shi?" ta wara ido tace "Lahh baka san sa ba Yaya? Toh ai shikenan, sai da safe" daga haka ta wuce da sauri tana murmushi ya bi ta da ido. Har titi umma ta raka Hajiya Saude suna tafe suna hira, Hajiya Saude tace "Toh ke kin dage tana karuwanci ta ya kika san haka" Umma tayi dariya tace "Ni kuwa xan fi kowa sani, ae ki bari kawai in Allah ya yarda sai uwarta Aisha ta ji kunya, sai ta gwammace a juyarta ta dauwama bata rufe bakin mutane da sauran ciwo ba" Hajiya Saude tace "Toh Allah ubangiji ya tabbatar da hakan, amma fa kamar Familyn Bulasawan ma naga sonta suke" Umma da taji ranta ya wani baci tace "Toh ae baxa su so d'an su ya auri warce ya lalata a waje ba, kuma muna nan sai Imaan tayi ciki a waje ba a dakinta ba" dariya sosai Hajiya Saude ke ta yi, Umma ta ja tsaki tace "Baki san ni bane, wannan yaron shine ajalin ita da uwarta, ba sai wani rawan kai suke uban ya mata kyautar rabin miliyan ba"
Chapter 164 · 0% Book details