← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 167 OF 292

Sashe 167

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

"Nawa xa ku bada Kaka?" Inna tace "To ko dai ya kai ni gidan Mujaheed kawai, tun da ya tare sau daya naje gidan" Ta Rasulu tace "Toh shiga, ko nawa ne Mujaheed din xai bada" Inna ta shiga tana kallon Imaan da tace "Ni gida xan wuce" Inna ta kalli ta Rasulu tace "Kinga jarababba ko??" Ta Rasulu tace "Dalla shiga ku je, duk saboda ke tsohuwar nan babu kokarin da bata yi amma baki gani, indan ta uwarki ce ai sai dai a kashe ki mu taho muna kuka" Imaan ta shiga adaidaitan kamar xata yi kuka, ta Rasulu ta juya tayi wucewarta, wani gidan mai me adaidaitan ya shiga xai sha mai yana ba Inna hakurin xai siya fuel, Inna tace "Na Bulasawa ne?" Yace "Ehh nasa ne" Inna ta washe baki tana kallon wagegen filling station din tace "Ai d'a na ne wllh" da sauri mai adaidaitan ya juya yana kallonta, tana nuna masa Imaan tace "Kaga surkarsa kenan, kuma jikata ce ni na haifi ubanta, ita kadai garesa duniya" Mai adaidaitan yace "Allahu Akbar" Inna tace "Kai da kasan Allah kenan yaro" dariya ya fara yi sosai, imaan dai gaba daya abin duniya ya isheta, kamar ance ta kalli gefenta taga Sadeeq coming toward d tricycle, suna hada ido ya sakar mata lallausan murmushi, sosai ta ga ya rame, ta sunkuyar da kanta da sauri, ya iso kusa da napep din ya xaga gun Inna da fara'a yace "Kaka ina xuwa haka?" Salati Inna ta saki tana kallonsa ta kalli mai napep tace "Toh ka gansa nan, ubansa ne mai gidan man nan" Mai napep ya kalli Sadeeq da sauri, ya washe baki yace "Ai ko ga kama" Inna tace "Atohh, ya xo checking ne da yake yau lahadi, kasan cuta tayi yawa duniya yanxu" Sadeeq na murmushi ya gaisheta da ladabi ta amsa baki har kunne tace "Wai gidan Mujaheed xai kai mu, Ashe gantalallen mashin din nasa ba mai shine ya shigo xa mu siya" Sadeeq yace "Toh ku sakko in kai ku ga motata can" Inna fito kamar jira take ta nufi motar ba tare da ta bi kan d'an sahu ba, Imaan ta bi ta da kallo taji kamar ta nutse kasa, Sadeeq dai sai murmushi yake, yana kallon mai adaidaitan ya ciro dubu biyu ya mika masa, karba yayi yana masa godiya, a hankali Sadeeq na kallon Imaan yace "Come down plss, there is nothing to worry about" sakkowa tayi daga napep din, ya nufi motarsa ta bi bayansa, Inna har ta shige baya ta xauna, imaan na hararanta ta bude front seat ta shiga, har suka isa gidan Mujaheed Imaan bata ce komai ba a motar, Inna ce dai ke hira da Sadeeq tana nuna masa hanya, xai yi parking a waje tace "A'a danna hann, xa su bude maka" Sadeeq yace "A'a Kaka ai ba kowa ke son a shiga gidan sa ba...." Inna tace "Ka ji ka Bukar, gidan Mujaheed ne fa" murmushi kawai yayi ta bude motar tace "Kuma da gaskiyar ka, don ba ko yaushe Mujaheed ke da kirki ba" Imaan na kallon Sadeeq tace "We will talk later, thank you" Yana murmushi yace "I am happy I saw u after few weeks" murmushi tayi masa, yace "Yaushe xa ku koma sai in dawo in dauke ku?" Tace "Xa mu dai yi waya" yace "Toh shkkn, thanks love" fita tayi ta bi bayan Inna, ya bi ta da kallo har ta shiga cikin gidan, Imaan bata ko kalli Inna dake tsaye tana magana da mai gadi ba ta nufi entrance din gidan ta murda kofa ta bude ta shiga cikin parlon da sallama murya can ciki, Mujaheed ne xaune parlon yana operating laptop tare da Safeenah da ta makalkale jikinsa kamar xa su dawo daya yana shafa dogon gashinta... Lkci daya Imaan ta juya masu baya a hankali, sai kuma ta fice daga parlon, Inna dake tahowa tace "Basa nan ne?" Imaan dai bata ce komai ba.
Chapter 167 · 0% Book details